← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 237

Sashe 110

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ƙananan yara bane munsan menene so, haka munsan ƙiyayyar itama. Amman me yasa baka sanar dani kana sona ba a lokacin da zan tafi Saudiyya ba?" Dariya yayi, ya damƙe hannunshi halamar yana cikin farin ciki. "Wauta, da tsoron kar in faɗa miki zumuncin da muke yi ya lalace, ni baki soni ba, kuma zumunci dani ma ki ƙiyi. Amman ko a filin jirgi naso sanar dake kwarjini ki Kai mun. Amman na sanarma da Dada ƙudurina kuma tasama abun albarka tayi farin ciki, babu mamaki ƙila sunyi maganar da Dadarmu amman bata ce mun komaiba kasancewar akwai kunya mai tsanani a tsakaninmu" To naji. Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi. Amman wani hanzari ba gudu ba. Bazan ɓoye maka ba, zanyi maka dukkannin irin biyayyar da ba kai zato ba. Amman bazan iya ɗaukar tallar nono ba gaskiyar magana. Amman inaso zan dinga kasuwancin kaya tsakankanin ƙauyannan, zuwa cikin gari, dan nayi sarin kayayyaki iri_iri. Amman batun tallar Nono babu shi, ka amince ko kana da ja?" Duk wannan maganar kaina a ƙasa nake yi mai. Ya jima bai bani amsaba yana nazari can sai naji ya nisa yace. "To Shikenan. Indai tallar nonone bakya so, to ba zaki ɗauki tallar nono ba Jabu. Zanyi iyakacin ƙoƙarina na ganin na fahimtar da duk wanda zai kawo tsokaci. Babu damuwa in Allah ya yarda, fatanmu Allah yaba Dada lafiya yasa albarka a cikin lamarin. Yau abinda ya tsaya mun cak zai barni in huta." Dariya nayi cikin zolaya nace. Menene ya tsaya maka?" Ya bani amsa da cewa. "Baki ga na rame ba? Ai tunaninki ne kawai yaketa ɗawainiya dani. Ko wajen aiki naje tunaninki baya barina inyi sukuni. Musamman in ina cikin daji da shanu, nafi ware lokaci na musamman ina hango irin rayuwar farin ciki da soyayyar da zamu gudanar a cikin ɗakinmu. Jabu zansa ki mance duk rayuwarki ta baya nayi miki alƙawari.' Mun daɗe sosai muna musayar kalaman ƙaunaa dan nima ba'a barni a baya ba. Zagewa nayi na dinga zaro mishi zaren maganganun ƙauna mai sanya nutsuwa da annashuwa. Daga ƙarshe ya rakoni har ƙofar ɗakin majinyata muka rabu kamar ba zamu rabu ba tsabaragen shauƙin juna. Na tarar da Baɗɗo tayi baccinta ta duƙunƙune da bargo. Dada ma sai baccinta take yi. Majinyatan ɗakin kusan rabinsu duk sunyi bacci. Dada na zuba ma idanu ina mata sdda'ar Allah ya tashi kafaɗarta taga aurena da Hamma. Ina roƙon Allah ya bata tsawon ran da zata goya ɗana da zan haifama Yaya Hamma a bayanta. A wannan daren in banda shauƙi babu abinda ke ɗibana. Tunanina yayi zurfi ya kaini har zuwa tsufana a gidan Yaya Hamma yaranmu suma sun girma, wai gamunan har a tsufan Yaya Hamma bai dena alfahari dani ba. "Baiwar Allah " Naji wata mata ta ambaci sunana ashe ma'aikaciyar jinyace har ƙarfe biyu tayi tazo sake ma Dada ruwan dake ɗaure a hannunta. Matsa mata nayi tayi aikinta, Dada dai bata farka ba, nima a haka bacci ya kwasheni zuwa asuba duk akayi waje damu, za'ayi shara a yi mopping kana a sake ma marasa lafiya zanin gado. A wannan rumfar muka haɗu da Sumayya bayan munyi Sallah muka gaggaisa ssi take cemun. "Bari inje in ɗaura girki kafin masu shara su gama gyaran ɗakin jinya. Girki kuma Sumayya, anan kuke girki?" Sai tayi dariya tace. "Anan nake yi. Gudun ɗaurama mutane wahala kinsan nace miki mun jima sosai a asibitin shiyasa. Bazai yiwu ace kullum sai an kawo muku abinci ba" Ksi na gyaɗa maganarta gaskiya ne. Bakin ƙofar ɗakin jinyar muks koma, muns zama Yaya Hamma yana ƙarasowa. Ina kwana Yaya Hamma?" Na faɗa a ladabce fiye ma da na da. Shima ya amsani a mutunce fiye da jiya. Suka gaisa da Baɗɗo. "Yaya jikin Dadan, ta farka kuwa?" Baɗɗo ce ta bashi amsa" "A's bata farka ba tukunna dai. Amman sunce zata farka yau" Shirune ya biyo baya kowanne da abinda yake lissafawa a zuchiyarshi. Ƙarfe takwas daidai aka bads izinin masu kula da masu jinya zasu iya komawa. Tare muka shiga ciki mu uku. Dakta muka gani a tsaye a kan Dada yana dubata, wani irin amai take yi kamar zata amayar da duka hanjinta, harda jini_jini a cikin aman. Ba shiri wannan Dakta ya kira wasu ma'aikatan kiwon lafiya mata suka kawo gadon tura marasa lafiya aka ɗaura Dads. "Zamu shiga da'ita ɗakin tiyata da gaggawa, ku biyoni maza" A gaggauce Dakta yayi maganarshi gabaki ɗaya hankalinmu ya tashi ganin halin da Dada take ciki. A bakin ɗakin tiyata muka tsaya, Dakta yaima wata mace magana, shi ya shige da Dada ita kuma tace ni in biyota. Binta nayi ta bani takaddar sanya hannu da kuɗin aikin a rubuce. Ta nuna mun windon da zan kai takaddar in biya, inna biya in dawo mata dashi. Nafi awa biyu anata cuku_cuku na biya duk abinda ake buƙata na dawo na tarar da su Yaya Hamma a bakin ɗakin tiyatar sunyi jigum. Ga wasu iyalanma munzo mun tarar dasu jigum_jigum da halama wani nasu suma suke jira a fito dashi. Kamar awa guda da zamanmu aka buɗe kofar ɗakin tiyatar aka tuƙo wata dattijuwar mace. Wannan iyalan suka bi bayan gadon suna hamdala. Da idanu na bisu ina fatan muma a fito da Dada lafiya cikin nasara. "Jabu bari in fita daga harabar asibitin kar su Baffa suzo su tarar Dada bata ɗakin jinya. Zan dinga leƙowa." Kai kawai na iya gyaɗawas, ya wuce nabi bayanshi da idanu har saida ya ɓace. Hawayen daya gangaro a kumatuna nayi saurin sharewa. Awa ɗaya awa biyu muna dai zaune. Yaya Hamma na leƙowa yana dubamu. Su Baffa Musa ma sun iso, da su Daso harda Hama. Amman su suna can wajen ɗakin jinya suna jira. Baffa Musa ne kawai yazo ya dubamu. Ni a lokacin babu abinda nake yi sai kuka kawai. Awan Dada uku a ɗakin tiyata Allah cikin ikonshi aka fito da'ita a gadon marasa lafiya. Muna biye da gadon ni da Baɗɗo mum riƙe hannun junanmu gam. Su Daso suna zaune a tabarma muka wuce ciki. Anyi sallama a ɗakin sosai muma mun samu an mayar da Dada gado. "Mun mata aiki cikin nasara yanzu jini zamu ƙara mata. Sai zuwa gobe zata samu farkawa. Tana farkawa kuyi maza ku kira Dakta, kar a bata komai taci. Allah ya ƙara sauƙi" Ameen mungode Dakta" Na amsashi. Ina zaune a kujera na tusa Dada a gaba sai hawaye nake zubarwa, zuchiyata tana ɗaci. A cikin wannan yanayin su Baffa Musa suka shigo suka riskeni Baɗɗo sai baki take bani. Daso ta matso kusa daf dani ta riƙe mun kafaɗa, mutum baida kama. "Kiyi haƙuri Jabu. Ayi ma Dada adda'a Allah yasa anyi tiyatar a sa'a, Allah ya tashi kafaɗunta." Ameen Daso mungode, sannunku da ƙoƙari" Baffa ma yace. "Ayi haƙuri, ciwon uwa akwai ɗaga hankali. Kuma duk mai rai mamacine, in Daso shan ruwanta bai ƙare ba ko ciwon da take ciki yafi wannan zata tashi. In kwananta kuma ya ƙare tana gaɗa tsabar lafiya saita faɗi ta mutu, ayi haƙuri" Kai na gyaɗa ma Baffa kawai. Hama cikin dakewa kamar ba itace wannan mai fara,arba tace. "Sannu Jabu. Baɗɗo Allah ya ba Dada lafiya" Ameen hama mungode sosai. Haihuwa kikayine?" Dan na ganta da sabon goyo ɗanye sharab. Baɗɗo ce tace. "Haihuwa tayi gobe za'ayi suna. An samu mace" Allah sarki Allah ya raya mana su." Na faɗa a sanyaye. Yaya Hamma yace. "Ki bata jaririyar ta ganta mana Hama" Da fullanci yayi Maganar, saida ta mayar mishi da amsa kafin ta sakko yarinyar ta miƙa ma Daso, ita kuma Daso ta miƙo mun. Bismillah nayi na amshi yarinyar a tsumman goyo, yarinyar na ƙarnin nono. Zanin goyon na warin hammata . Dan hammatar Hama cike maƙil take da gashi har wani ja yayi da wani dattin fari.Yarinyar fara sol, ga gashi duk ya lulluɓe goshinta da gefen kunnenta. Yarinyar takai minti biyar a hannuna na miƙa ma Daso ita. Allah ya raya mana" Daso ce ta amsa, Hama kuwa bakinta ko motsawa baiyi ba. "Jabu ga abinci mun kawo muku. Da yamma matar Amaduyal zata kawo na dare. Dadanmu tace zata zo da rana inta gama tallan Nono " Da hanzari Baɗɗo ta buɗe ledar abincin. Tuwon masarane da miyar kuka da nama a ciki. Ta zuba nata ta zauna ta soma ci. Ni kuma na haɗe musu kan kwanukan jiya nasa musu a leda. "To mu kam zamu tafi. Ni na bari ana dafa mun Nono" Cewar Daso. Godiya muka yi musu. Baffa Musa yace shima kiwo zai tafi dan haka zai koma. Ya zaro dubu biyar ya bani yace in riƙe a hannuna. "Nima zanje in dawo Jabu. Ba jimawa zanyi ba" Cewar Yaya Hamma. Ledar kwanukan abincin jiya na miƙa mishi. Mu kai musu sallama suka fita. Ajjiyar zuchiya na sauke na zuba tuwonnan da nama yanka biyu. Babu maggi acikin miyar sai gishiri haka na tuttura na kora da ruwa yinwa nake ji sosai. Tea na haɗa kofi ɗaya na kwantar da wannan tuwo. Yaya Hamma baifi Awa uku ba ya dawo, ya dawo ya tarar an ɗaurama Dada ƙarin jini. Mu kuma har munje munyi sallar azahar mun dawo muna zaune muna ɗan hira ya shigo. Sannu da zuwa mu ka yi mishi. Wanka yayo dan har kaya ya sake da suwaita da hular sanyi duk ya canja. "Jabu anfa samu gidan siyarwa. Abokinane zaiyi aure shine yayi gini. To auren yasha ruwa sakamakon wuta da uwargidanshi ta buɗe. To shi yace da zai samu mai siyan gidan shi ko nawane daya siyar. Gidan babbane ɗakuna biyarne, sai madafi da banɗaki. To me kika gani?" To Yaya Hamma in kana ganin babu wata matsala ai ni dama nafison in siya gida ba fili ba. Nawa kuɗin gidan?" "To da na nuna mishi ke zaki siya, yace mu kawo dubu sittin da bakwai. Amman yayi sauƙi sosai ni dai nace sittin zamu biya. In yayi miki ki ƙirgo kuɗo yanzu sai in koma in bashi, gobe zaki ganshi ya ƙaro shanu." Jakata na zuge na ƙirgi kuɗinnan cas na ba Yaya Hamma. "To saina dawo bazan jima ba" Yasa kai ya fice murmushi nayi na cikar burina, hatta wahalar da nasha domin
Chapter 110 · 0% Book details