← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 195 OF 237

Sashe 195

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

an kai ruwan wankan kije kiyi" Fita Uwani tayi, ni dai nayi jigum sai ga kishiyar Uwani ta shigo da kulolin tuwo dana miya, harda gaushi. Itama da ciki a jikinta. Ajjiyar zuchiya na sauke na ajjiye yarinyar a gado na sakko da su Hassan duk bacci suke yi na shinfiɗesu na fito. Alwala na ɗaura na koma ciki, na tadda kishiyar Uwani na zaune tana cin tuwo. Ina kan rama sallolina Uwani ta fito wanka. Sallamar sallar magriba nayi wacce tayo daidai da shigowar Hafizu ya nemi waje ya zauna harda leda a hannunshi cike da balangu. "Gashi kici ki sha tea, gobe zan shigo da kayan tea ɗin. Ke kuma in kin gama sai mu tafi ko?" Yace da matarshi. A_a Hafizu ku dukka ukun inaso zanyi magana daku. Domin na fahimci kamar akan amaryarka ne aka samu wannan saɓanin" Ai sai ya gyara zama yace. "Alaja kinga maganarnan a batta kawai babu abinda zata haifar sai fitina. Kuskurena ɗaya na sakinta da nayi ne" "Sabida kana baƙin ciki da ɗaukakar da Allah yaimun akan kasuwanci ba. Hassadarka harta fito fili Hafizu na gama zama da kai Allah shine shaidata nayi iya yina. Iyabo na roƙeki da girman Allah karki tursasani komawa gidan Hafizu ki barni in auri wanda a ƙalla ko abincine zai iya bani. Wahalar Hafizu waccece ni Uwani ban shaba. Ke kuma ki ficemun daga gida kar in sake ganinki a gidana. Yaranku zuwa anjima in suka dawo daga gidan Hajiya zan rakosu da kayansu kije ki haɗa da ubansu kiyita rainonsu gaki ga rijalu tsohuwar makira" A zafafe kishiyar Uwani ta tashi ta fice harda doka tsaki dogo. Uwani ta bita da manyan ashariya ba sai faɗa ya tashi ba gaga_gaga da ƙyar ƙurar ta lafa wallahi Uwani dake jego itace har waje wai zata daki kishiyarta sai maƙota aka jayeta ta shiga. "Da ki tsaya mana kiga. Tsohon mitsiyaci saika bita ai." Ni dai da ƙyar na dinga jan Uwani har cikin gida. Hafizu na koma na samu a waje yama kasa tafiya. Hafizu kayi haƙuri ka ɗan ɗauke ƙafarka zuwa ɗan wani lokacin inta huce. Kafin in koma zanyi iya yina" Murmushi yayi yace. "Alaja karki ɓata yawun bakinki in dai ta balbalin ce ba zata dawo hannuna ba. Ki mata godiya a bisa halaccin da taimun Uwani ta zauna dani cikin baƙar wuya. Bana mance sanda take fita ta nemo mana abinda zamu ci. Sannan bana mance sanda talauci yasa ni da'ita duka muka bar ƙasar dan neman rufin asirin kanmu dana yaranmu. Iyabo kice mata Nagode ƙwarai Allah ya bata miji nagari wanda zai tausaya mata" A wajen ya tafi ya barni. Kai na girgiza na koma cikin gidan. Gaga_gaga haka muka wayi gari cikin hukuncin Ubangiji. Ina tsakar gida ina ma ƴan biyu wanka, Ummi kuma tana mana dumamen abincin kari. Uwani kuma sai gyaran ɗaki take yi ta kwanta ta hutama ranta taƙi fur. Kayan Hafizu ta jefo tsakar gidan a jaka. Ni da ummi me zamu yi in ba dariya ba. Haka Uwani ta kuma jefo kayan yaranta tsakar gidan. Wai Uwani da gaske yarannan mayar dasu zaki yi gidan Babansu, batun karatunsu a ina zai kwana. Bakya jiye musu wahalane?" "Bana jiye musu. Iyabo ke bakisan yaran da suka sha wahalar rayuwa Allah ya fi ɗaga darajarsu ba? Wallahi ko wayo da sanin ta kan duniya sunfi. Batun makaranta ba dole sai sunyi karatu zasu rayu ba. Wallahi bazan riƙe su ba gidan ubansu zasu koma" Muna cikin wannan jawabin sai ga Zaliha da yaran sun shigo. Suna ganina suka yo kaina da murnarsu. Jakar tsarabarsu na miƙa musu. "Zaliha da ke da ummi ku kwashi kayannan ku kai gidan Hafizu ku haɗa har da yaran." Mai sunan Hajiya dake itace babba tace. "Umma can zamu koma?" Uwani tace. "Canne yafi dacewa daku Ummu Kulsum. Maza bi su ummi su kaiku" Uwani ta kaɗa yarannan ko a jikinta. Harara ta doka mun ta zuba mana ɗumamen tuwonmu muka shige ciki. Saida na shirya ƴan biyu tsab na zauna muna cin abinci muna hirar yaushe gamo. Harna ba Uwani labarin naci gaba da yin makaranta kuma abun dai kamar zai ɗaure. Ki taya ni da adda'a dai Uwani. Inaso in zan tafi in yi sare_saren kayan kwalliya da magungunan mata ko da iyakar tsumi ne in jaraba. Amman meye shawararki tsoro nake ji, amman kuma zaman haka ba daɗi. Ga Hamma ni bansan ma yaushe zai dawo ba." Saida Uwani ta barbaɗa yajin daddawa ta saka lomar tuwo ta haɗiye kana tace. "Hakanma yayi Iyabo. Tunda ai dama hannu mitsiyaciyar kishiyarki ta saka miki. Yanzu kuma da izinin Allah munfi ƙarfinta. Zan kaiki gidan Sharubutu ya baki rubutu ki dinga sha. In sha Allah sai kin zama Hajiyar rugga Iyabo. In abubbuwa suka bunƙasa sai kici gaba da ɗakko kaya daga saudiyya. Ni nan da wata huɗu ma zanje saudiyyan da kaina zan saro kayan. Kinga lokacin in al'amura sun warware kasuwa ta buɗe miki sai mu tafi tare ai. In ma Hamman bai dawo ba sai ki tambayi uwar mijin naki. " Dariya nayi nace. Da wanne kudin duk za'ayi haka Uwani?" "Ke dai kiyi ta adda'a kawai. In dai Allah ya dafa miki aka ci gaba da siyan kaya a hannunki zan sai da ƙaramin gidana in ara miki jarin ki juya ki samu alkhairi. Iyabo ai hakan shine ƙawancen" Mun daɗe munata tattaunawa da ƙyar wajajen la'asar na yakice bayan na gama yima Uwani tuwon dare na leƙa gidansu Iyaa Debisi. Suna shago kamar kullum Iyaa Debisi ta hangoni, saita soma rawa tana ma ƴan biyu waƙar sunansu da yarbanci. Iyaa Kokodeen ce ta fito ita ta ɗauki Hassan Iyaa Debisi ta ɗauki Usaini. "Masha Allah yara sai girma suke yi. Ke ma ba laifi kinyi kyau ba kamar sadda muka je suna ba. Amman jibi shigarki dai irinta fulani kin ɗauko koriyar atampa kin saka" Cewar Iyaa Kokodeen kenan. Iyaa Debisi kuwa naci sa'a bata ce komai ba jikokinta sun janye mata hankali. Ina shiga gidan na tarar da Bose ta fito tana son zata tafi gida da yaranta. "Ahhh Antimi Iyabo. Kece da magriba haka muna shirin guduwa?" Rungume junanmu muka yi muna farin cikin ganin junanmu. "Ina yaran kuma?" Ta tambayeni. Suna wajen su Iyaa a waje. Na bata amsa ina Dariya. Matan gida duk suka shishshigo ganin yara bayan su Iyaa sun shigo dasu. Yaran suna da mugun farin jini sosai da sosai. Ni dai har nayi sallar isha, na fita na raka Bose da yaranta suka tafi gida. Yarannan suna hannun Iyaa Debisi. "Ina Daso, da mai gidanki, da kuma ƴan uwan naki?" Lafiya ƙalau Iyaa. Dada tace in gaisheki sosai. Ga tsarabarta nan, wannan kuma tawa ce a raba ma su Iyaa Beji." Kai Iyaa Debisi ta girgiza tace. "Angode. Iyabo kuma kina jin daɗin rayuwarki a wannan rugar? Naji labarin mijinki ya tafi cirani ya samu waiwayar gidane." Kai na sauke ƙasa a sanyaye nace. Iyaa inaji babu abinda yake damuna. Shi kuma bai dawo ba tukunna bai ko yi aike ba ma" "Hmm ba sai su shekara biyar ba ma basu waiwayi gida ba. Wasu ma sun fito sunji daɗin birni basa sake waiwayar rugarsu shinfiɗa sabuwar rayuwa suke yi. Uwani tasan kinzo kuwa?" E ta sani tama haihu jiya ta samu ɗiyarta mace. Gashi aurenta da Hafizu ma ya mutu" "Ahhh Ahhhh" Ta shiga jerawa tana dukan cinyarta. "Ai Shikenan ta huta ya huta. Ba'a matsa ma kai. Yayanki Debisi ma sun rabu da Yemisi fa. Yanzu haka yana neman wata yarinya a bayan layinnan. Kinsan gidansu Bola?" Ta tambayeni. E nasan gidansu Bola" "To yarinyar a gidan take Auwa. Yarinya mai hankali tazo ta gaisheni ma Debisin ya kawota" Allah sarki. To Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi " Tayi carab tace. "Shine ma alkhairin. Ke kinsan rikicin da akayine? Ai ni da Uwar Yemisi har abada. Yemisi fa kusan kashe Debisi tayi da duka. Duk ta farfashe mishi fuskarshi. Har ɗinki akayi mishi a gefen idanunshi. Watanshi guda a asibiti Yayanku Kokodeen na jinyarshi" Ta dinga bani labaran abubbuwan da suka faffaru, harda rashe_rashe da ƙaruwa da aka samu. Mun jima sosai kafin mu kai bacci, zuchiyata sai naji tayi sanyi sosai. Washe gari duk nabi maƙota da ƴan uwa duk aka gaggaisa. Sai wajajen azahar muka wuce gidan Uwani ni da Iyaa Debisi ta yi mata barka da jajen mutuwar aurenta ta tafi ta barni akan in anyi suna zan dawo" Mun sha suna lami lafiya. Kuma Hafizu yayi bajinta sosai, ya yanka tunkiya ƙatuwar gaske, ga kayan fitar suna kala ukku na mai jego, kala ukku na jaririyar yarinya taci sunan mahaifiyarshi. Taron suna ya watse lafiya, saina soma haramar tafiya, na shiga kasuwa na ɗan yi sare_sarena dai amman ban zura jikina ba dai Kuɗin hayane da Uwani ta ajjiyemun a wajenta da su naketa siye_siyena. Na sai su maggi, da kayan abincina harda taliyar murji Iyaa Debisi tayi mun, iyaa Kokodeen kuma ta haɗamun su elbo, da garin Amala, ga garin eba. Tsaraba dai rigijib. Uwani ma ta tsinta mun kayayyakin yara tace in siyar in jaraba ko zasu karɓu, in sun karɓu shikenan sai inci gaba da kasuwanci na. Sai da na yi sati biyu cur na tattare inawa inawa Burodami Debisi ya rakani tasha na tafi, ya bani kuɗi masu yawa, dan har nama ya kawomun mai yawa na soya nayi miyar tumaturi cikin ƙaramar robar fenti. Yanzu ya riga daya saduda yayi haƙuri har yarinyar da zai aura saida ya kawota da daddare ta gaisheni. Da yamma sakaliya sai gani na duro. Nayi lalle, da kitso, ga sabon lace da uwani ta ɗinkamun shi na sako. Matan gidan suna tsakar gidan anata hada_hadar girki sai ga ni na shigo da sallamata. Baɗɗo da Safiya ne suka tawo a guje suna yi mun oyoyo. Yaran maƙota na biye dani da kaya niƙi_niƙi. Baɗɗo ta tsaya saukesu, ni kuma na shige ɗakin Yafendo. A cikin ɗakin na tarar da Daso, da Yafendona Maman Dason kenan, da kuma Dada. "Ah Jabu kece da yamma lis haka. Lale da zuwa" Cewar Yafendo. Da fara,ata na shiga na nemi waje na zauna a gefen Daso. Sai kallona take yi, taga na
Chapter 195 · 0% Book details