← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 237

Sashe 90

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da nayi miki duk sanadiyyar kuɗin zinar ce. Kinga kema kuɗin yayi miki rana. Da yanzu daga ni har ke muna neman mafaka, tare da neman tudun dafawa. Jibeki fa jinyar wahala da azabar gidan Larabawa kike fama dashi. Kafin ke wasu sunyi, wasu fa tsabaragen wuya yankar jiki suke su faɗi su mutu, wasu su haɗiyi zuchiya." Da tsawa take yi mun magana yarinya ƙarama. Ko me ta tuna oho sai naji salama a muryar tata. "Iyabo tawa ƙaddararce haka. Kamar yadda ƙaddara ta zargo rayukanmu ta haɗamu a gidannan. Ki yi harkokin gabanki, ki barni inyi nawa Allah da kike ji da ganinshi me gafartama bayine." Hakane Faty Ubangiji Allah yasa mu dace. Ki taimaka ki ara mun wayarki zan kira gida. Tunda nazo ban samu damar ji daga garesu ba." Kamar dai ba zata bani ba dai. Sai ta miƙo mun. Number Burodami na lalubo a cikin kayana na kwafeta tsab a wayar na danna kore. Ruri biyu zuwa na ukun naji an ɗaga. Burodami Debisi Emi ni Iyabo ( Nice Iyabo) Ina faɗin haka sai kuka na baƙin ciki da nadama. "Ohh Ohh ohh Iyabo sai yau kika kira? Kin samu a damuwa musamman zuchiyar data shaƙu dake, ta horu da sonki. Ina fatan kina lafiya ko?" Sai kawai nace dashi. Lafiya lau, ya su Iyaa, da su Iyaa Beji da su Iya Kokodeen?" "Duk suna Lafiya. Jiya jiyannan Dada da Hamma suka koma. Sun zo kwanansu biyu. Dada ta damu da Iyaa ta faɗa mata baki kira ko sau ɗaya ba." Sababbin hawaye na matse a idanuna daɗin jin labarin Dada da Hammana ya sani cikin farin ciki. Allah sarki Dada. Suna lafiya ko? Kwanakin baya na ari waya na kiraka baka ɗaga bane. In Dada ta dawo a bata wannan lambar. Lambar yarinyar da muke ɗaki ɗaya ne. In akaci sa a na dawo hutu daga gidan aiki sai mu gaisa" Bai bani amsaba sai kuɗin ya ƙare. Kafin in ajjiye wayar sai ga kiranshi ya biyo ni. "To Iyabo zan bata. Ko bata zo ba zan shirya in an kwana biyu in kai mata. In naje gida zan kira in haɗaki da Iyaa. Kullum sai ta yi zancanki." Murmushi nayi nace. To Shikenan Burodami. Nagode, sannan a taya mu da adda'a. A faɗa ma Iyaa da Dada ina buƙatar adda'a" Buɗar bakinshi sai yace. "Masoyinki kuma mijinki na biyu ma zai hana idanunshi bacci wajen yi miki adda'a. Ina ɗan birri ɗan ƙauye me kiwo ba yamun ƙwacen masoyiya ba. In banda so da abinshi, me yasa zai kai kanshi dokar dajin da babu komai cikinta sai nono da fura" Ƙit sai na kashe wayarnan, raina ya ɓaci ainun. Miƙama Faty wayarta nayi, tare da yi mata godiya. Ban ɗaki ta shige, ni kuma naci gaba da cin tuwona. Sima na tsaye yana shafa mai yana rawa. Inata nazarin maganganun Burodami Debisi. Hammana ne ya faɗo mun a raina. Ya iyali ina son Hamma so marar abin misalin da hankali zai ɗauka. Dama zuchiyata wawuyar zuchiyace bata iya son abu ba sam. Haka kuma bata iya ƙin abu ba. Fitowar Faty daga banɗakine ya katsemun tunanina. "Da badan ƙafarki na ciwo ba, ai da kin rakani kasuwa inason sayen ɗan kunnen gold." Duk da nasan ina shan azaba sai nace mata. Da yaushe zaki je? Inason in ɗan fita ganin gari tsorone yake hanani dama." "Zuwa dare kinsan da daddare suke buɗe kantinansu. Khalifa zai zo ya kaimu. Daga nan ma sai ki rakani wajen wata ƙawata" Murmushi nayi mata nace da'ita. Tom Shikenan. Allah ya nuna mana sai in lallaɓa muje nima in gano gari kullum kana ƙunshe a gida" Yawu na haɗiye kana na ɗaura da faɗin . Ni ko Faty Uwani dai bata dawo daga gidan aiki ba tunda muka tafi ko?" Baki ta taɓe tace. "Ki yi tsammaninta dai zuwa shekara guda tim, ko wata shida haka. Kinsan fa su basu fiye son ana zuwa Ijaza ba. Ko mu sanda muke zuwa gidan aiki sai in mun gaji sai muyi ƙaryar ciwo shine zasu barmu mu tawo. Kinsan suna da tsoro gani zasu yi zaki mace musu ma" Dariya muka saka dukkanmu. "Allah kuwa. Haka suke da wannan tsoron. Mu kuma da munji aiki na shirin kashemu, sai mu langwaɓe" Haka mu kai ta taɓa hira. Daga baya kuma duk mu kai bacci, bayan mun yi sallar azahar kenan. Bamu muka tashi baccin ba sai kusan magriba. To ni daman a mugun gajiye nake, ga rashin samun wadataccen hutu. Wanka nayi a gurguje na ɗauro alwala. Faty ta faɗa banɗakin. Ina idar da la'asar ana kiran magriba. Tsakanin magriba zuwa isha a lokacin minti talatinne. Sai da mu ka yi isha Faty ta ajjiye mun wata baƙar abaya tace. "Ki saka wannan a saman kayanki. Ga turare sai ki shafa a jikinki" Karɓan turaren nayi a hannunta. Nayi kamar yadda tace. Ƙarfe taran dare Khalifa ya kirata yana ƙofar gida mu yake jira. Tare muka fito a jere mu uku. Nan naga dare tamkar rana. Kowa a cikin gida da ƙofar gidan sai hada hadarsu suke yi. Masu fita nayi, masu hira da takari nayi, gasu nan dai barkate. Wata baƙar mota me kyau muka shiga. Ina shiga na tarar da wani balarabe me gashi har kafaɗa, ya sa baƙar jallabiya yana ta kallona. Assalamu alaikum. Na furta murya na rawa. Dan naga kallon da yake yi mun yayi yawa. Faty ta juyo ta kalleni ta ɗan kashe mun idanu, ta maida kallonta wajen sima dake kusa dani tayi mishi murmushi. Na fahimci me take nufi sarai, tana nufin kar in ba da ita. Motarmu ta fice a layinmu a guje. " Masmuki ya bint?" Wanda muke gidan baya ya tambayeni da fara'arshi. Ismi Iyabo" Na furta a sanyaye. " Halta kafin? ( Tsoro kike ji)" Ya tambayeni, kafin in yi magana Faty tace. " Hiya daifun min najeriya" Sai ya girgiza kanshi yana mun dariya. " Anti jamilatun jiddan ( kina da kyau sosai) Halnastaɗi'u annakuna sahibain ( zamu iya zama abokai?). Ɗan dariyar yaƙe nayi dan a lokacin bansan me yake nufi da kalmar ba. Sima da murmushin ya bini. Sima kuma sai zungurata yake yi, nayi banza dashi. A bakin ƙaton kanti muka tsaya ko ina lantarki, sai hada_hada akeyi kamar rana. Ni dai ina biye da su Faty zungui_zungui. Wannan abokin saurayi nata ko yaya muka haɗa idanu sai yayi mun murmushi. Ni dai illahirin jikina a mace yake, zuchiyata sai harbawa take yi. Shagon gwala_gwalai muka shiga, abun mamaki saurayin Faty sai sawa yake yi ana cicciro sarƙoƙi manya_manya yana ta karawa a wuyan Faty. Da ƙyar suka ɗauki wata sarƙa da ɗankunne masu kyan gaske. Wannan aboki na saurayin Faty har za a mayar da sarƙoƙin a hallahesu, sai ya sa hannu ya ɗauki wata madaidaiciyar sarƙa mai mannen ɗan kunne, yace da me shagon. " Kam haza?" ( Nawa wannan) Ya tambayi me shagon, ya faɗa mishi kuɗin. Kuɗi ya zaro a aljihunshi ya biya kuɗin sarkar. Aka sa sarƙoƙi biyu a leda daban_daban muka fito. Daga nan sai muka wuce wani gidan cin abinci mai haɗe da ɗakunan kwana. Gurasa ce aka kawo mana da nono da ake dangwalar gurasar dashi, sai shinkafa kaza ( chicken biryani). Ni dai duk a takure nake ainun, ga kallo na masifa. Faty kuwa sai taɓe_taɓensu suke yi ita da saurayin nata, Sima kuwa a teburin wasu matasan larabawa yaje ya zauna abinshi, daga ƙarshe ma suka zame suka barmu daga ni sai Yariman kallo da murmushi ( sunan dana raɗa mishi kenan) "Ma sa'alti nis mi " ( Baki tambayeni sunana ba ƴan mata). Mafi arabiya ( ban iya larabci ba) Na faɗa mishi. "Halnastaɗi'ina antata kallami bil guggati ingiliziyya? ( Kin iya turanci to) Ya tambayeni yana ƙure ni da idanu. Ƙalil_ƙalil ( Kaɗan_kaɗan) "Halnastaɗi'u hannata kallam al'an ( Yanzu zamu iyayin magana)? Na'am ( E) Na faɗa a gajarce. "What bring's you to this country? ( Me ya kawoki wannan ƙasar)? Ya tambayeni tare da bani dukkan nutsuwarshi. I came to work ( Nazo aiki) Na sake amsashi cike da ƙosawar tambayarshi. " Wich tabe of work ( Wanne irin aiki?)" Na yi shiru domin bansan ma me zance mishi ba. Tambayoyin sun mun yawa, daga haɗuwa sai ya titsiyeni da tilin tambayoyi. Ina cikin zancan zuchi sai ga Faty ta ƙaraso tana gyara zaman rigarta. "Yi haƙuri na barki kina jira. Amman nasan Salim uban magana da bin diddigi bazai bar bakin ki ya huta ba. Dan ƙila har kakanki na huɗu ya tambayi sunanshi ko? Dariya ta bani sosai, haka dole na ɗan dara kaɗan. Saurayinta ne ya ƙaraso shima sai gyare_gyare yake yi. Bamu muka koma gida ba sai wajajen biyun dare. Har mun fito a motar Salem ya biyo mu. Ledar wannan sarƙar zinare ya muƙo mun. Tare da gyaɗa mun kai halamar in karɓa. Faty na kalla itama taimun nuni da in karɓa. Hannu nasa na amsa nace. Thank you very much ( Nagode sosai). Sai yai murmushi yace. Halnastaɗi'u annakuna sahibain? (Zamu iya zama abokai) Ya tambayeni. Cike da ƙosawa nace. Na'am" Sai naga yayi wani ɗan ihu tare da damƙe hannayenshi bibbiyu. Ni dai haka na ɗingisa na shige ciki. Faty kuma a wajen na barsu ko me suke taunawa ohon musu. Ɗaki na faɗa ina mayar da numfashi na. Ban wani jima da shigowa ba su Faty suka shigo tana dariya. "Kakarki ta yanke saƙa Iyabo. In dai neman kuɗi kika shigo ƙasarnan da zummar yi. Albishirinki ga mijin Aure sukutum kin samu. Salim yace dani in miƙa soyayyarshi gareki, kuma a yadda ya nuna wallahi sonki yake yi. Kinga kuɗi ya bani yace in baki kiyi siyayya" Kuɗin ta miƙo mun. Wanda a lokacin wannan kuɗi in aka canjasu izuwa kuɗi namu na gida najeriya zai iya kaiwa dubu ɗari. Dubu ɗari me darajar fin million ɗaya a wannan zamanin da kuɗi basu da albarka. To a lokacin kuɗi babbane dubu ɗari, baki na riƙe nace. Ke Faty bazan karɓi waɗannan kuɗin ba ko ba gaskiya ba? Domin bazai samu soyayyataba bazan iya aurenshi ba. Na baro masoyina a ƙasata, ina da yara, iyaye, ƴan uwa. Wannan sarƙar ma cike nake da taraddadin
Chapter 90 · 0% Book details