← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 237

Sashe 95

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

inda zan dosa ba, ina tsoro da gudun faɗawa matsala" Nan na soma labarta musu baƙar wuya da azabar da na sha, da ƙazantar dana tsinci kaina a ciki na ƙarfi da yaji. Uwani ta fashe da kuka tace. "Nima haka na samu wata uwar aiki ta dinga tursasani irin ƙazantar da aka saki a ciki. Iyabo naci baƙar wuya. Kinga dama ni tunda labarin mutuwarki yazo garemu na yanke yin waya da su Hajiya, da Hafizu da yaran duka. Dan na yanke har abada bazan koma Najeriya ba. Dan bansan me zance ma danginki ba" Ina hawaye nace Sake komawa gidan aiki kika yi bayan rabuwarmu dake da nace ki bani wata ɗaya zan dawo?" "Gidajen aiki har uku ma masu mugun hatsarin gaske. Amman babu abinda zamu ce da Allah sai godiya. In sha Allah daga nan sai gida Najeriya. Kuma na gode Allah nayi Umara har sau biyu. Kefa kin samu wannan damar?" Ta tambayeni da karshashiin son jin amsa. Idanu na lumshe na buɗe. Na samu damar yi sau ɗaya. Alhamdulillah. Bani da burin daya wuce in sa iyayena da yarana a idanuna. Nifa tunda nazo ƙasarnan sau ɗaya tak nayi wayaa da Burodami Debisi " Faty tace. "Ai kuwa wani mai suna hakan ya kikkira wayata. Sai wani mayen Hamma da duk bayan kwana biyu sai ya kira wayata yanaso yayi magana dake" Idanuna na lumshe soyayya da kewar Yaya Hamma suka dirarmun a zuchiyata farin ciki ya kamani. To ku aramun waya in kirasu. Allah sarki Yaya Hamma ɗan amana ashe ina ranshi kamar yadda shima yake raina" Faty ta miƙo mun wayarta tana daga kwance. "Banyi serving number shi debisin ba. Amman na seving ɗin ta Hamma guda ɗaya. Dan lambobi daban_ daban yake kira dasu. Daga baya ne yace in save ɗin wannan, in kin zo in baki shine layinshi. To shine dawowar da baki yi ba sai yau" MRS BUKHARI
Chapter 95 · 0% Book details