Sashe 187
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya daɗe yana shafa bayan Shafa amman ta kasa bama zuchiyarta haƙuri ta dangana. Zuchiyarta ta daɗe tana ƙunsan wannan takaicin na yadda yake kasa ɓoye soyayyar Hadiza a ko'inane ko kara baya yi mata. Sai dai ita tayi mishi kara ta tayashi son abinda yake so. Haka Hadiza ƙiri da muzu taƙi amincewa asa ma ɗiyarta sunan Iyabo. Amman ita tambaya ɗaya yayi mata ta amince mishi. Ko kusa bawai dan tana son sunan bane, tayi hakanne domin son abinda mijinta yake so. Duk kawaici na danginta saida saka sunan Iyabo ya taɓa ransu, Tamu ne yayi kinini a cikin lamarin ya hanasu tayar da zancan. "Kiyi haƙuri Shafa koma menene ya saki kukan na roƙeki kukanki yana dafani? Da sauri ta ɗago ta zuba idanunta a nashi a ƙoƙarinta nason ganin da gaske yake yi kukan nata na gasa ranshin kuma. Ja taga idanunshi sunyi harda maiƙon hawaye. A hankali ta sauke kanta a sanyaye tana sauke ajjiyar zuchiya. "Inason sanin damuwarki da abinda ya sakaki wannan kukan. Ko dai ganin Hadiza da kikayi a maƙale danine ya zaburo miki da kishin ki uhm?" Shiru tayi tana share hawaye. Niyyar tashi daga jikinshi tayi yayi wuf ya sake dawo da'ita jikinshi. Kyakkyawan riƙo yayi mata ya tallafo haɓarta tare da yima bakinta riƙon alewar yara. Wata duniya suka shilla ta masoya Gwadabe da Shafa sunma mance a duniyar da suke jin daɗin rayuwarsu kawai suke yi. Labulen ɗakin suka ji halamar kamar a ɗage yake. Shafa ce ta yi saurin juyowa suka haɗa idanu da Hadiza dake tsaye tana hucin kishi. Gwadabe na zaune ko gezau baiyi ba balle yayi yinƙurin tashi. "Lafiya zaki buɗemun labulen uwar ɗakina babu sallama balle neman izini, in da kinga abinda yafi haka kuma fa? Kinga hakan ai bai dace ba. Baban Abba tashi kuje Allah ya bamu alkhairi." "Ni kike faɗama wannan maganar, ashe ba har zuchiyarki kika sallamamun mijin ba? In ba haka ba daga zuwa yayi miki sallama zaku ɓige da soyayya ba kunya babu tsoron Allah. To yayi zamanshi anan wajenki ki bashi abinda yake buƙata. Namiji da kishiya duk amincinku watarana sai sun munafurceka" Tana kaiwa nan ta saki labulen tayi ficewarta. Shafa ta dubi Gwadabe da taga yayi shiru baice komai ba, shi bai tashi ba, shi bai magantuba. Haƙiƙa taji ciwon maganganun Hadiza, ko dai dama ba yau ta soma yi mata ire-irensu ba, dannewa kawai take yi da ƙoƙarin a zauna lafiya" "Shafa kiyi haƙuri ki daɗa zan kuma yima tubkar hanci danna fuskanci Hadiza zuma ce sai da wuta. Ni na ɗauka lallami zai bi da'ita ashe ba haka bane. Jeki shinfiɗe yara sai ki dawo" "Kaifa ai ya kamata kaje ka rarrashi ƴar gwal ɗin taka da baka ƙaunar ganin ɓacin ranta." Shafa ta faɗa cikin sigar kishi da muryar tausayi ainun. Kunya ta shigi Gwadabe dan tabbas yasan Shafa akwaita da kawaici da yakana. "Ke dai jeki ki dawo, anan zan kwanta ke ba a gabanki tace in yi zamana ki bani abinda nake buƙata ba?" Murmushi Shafa tayi kawai ta miƙe taje ta yima yara shinfiɗa ta dawo ta tarar har Gwadabe ya tuɓe yana kwance." "Baban Abba kayi haƙuri karka biyema tuburarriyar matarka in kayi la'akari da mutuwar da akayi mata da tiyatar da akayi mata. Inma kana son ɗaukar mataki a wannan karon na roƙeka ka daure. In dai Yaya ce halinta ne zata sake ai." Da ƙyar Shafa ta sha kan Gwadabe ya tashi ya mayar da kayanshi yai musu sallama ya fice. Hawayen baƙin ciki Shafa ta sake sharewa ta sake komawa wajen yaranta. Da salllama Gwadabe ya shiga ɗakin fuska a turɓune, Hadiza tana zaune amman ko kallo bai isheta ba balle har ta amsa sallamarshi. Abinda ya sake ƙular dashi kenan, amman sai ya rabu da'ita ya haura gado ya kwanta yana shafar fuskar jaririyar da sai mutsu_mutsun somin kuka take yi. Ai kuwa kamar jira jaririyar take uban ya taɓata ta ɓalle da kuka. Nan ta shiga canyara kukan inya_inya Hadiza tayi funfurunfus taƙi juyowa ma balle ta san yarinyar na kuka. Shiko Gwadabe mamakine yasa ya kasa cewa da'ita uffan sai idanu da yake bin Hadizar dashi. "Ke Hadiza wai baki ji yarinyarnan tana kuka bane koko Yaya?" Yayi maganar da kakkausar murya. Hadiza ta sake bama banza ajiyarsu lamarin daya fusata Gwadabe ƙarshen fusata, fusatar da bai taɓa yin irinta ba." "Wai shin ba dake nake magana bane Hadiza kina da hankali kuwa?" Wallahi Hadiza ta sake yin watsin ruwan tsarki da Gwadabe harma ta yi kwanciyarta a gefen gadon ta juya mishi baya. Miƙewa yayi da jaririyar ya shiga jijjigata dan baƙin ciki da ɓacin rai jikinshi har rawa yake yi, take kanshi ya soma sara mishi. Shi kam ya gaji da matsalolin Hadiza. A yau yayi ɗan daka ce bai auri Hadiza ba ya rabu da'ita ta auri wani kamar yadda malam yace mishi. Lallai Hadiza mahaukaciya ce sosai. Kukan jaririyar ya karaɗe kab gidan harda ma can cikin gidan. Auwala ne ya tawo shi da matarshi suka shiga bubbuga kofar Gwadabe. Kafin yazo ya buɗe Sabitu ma ya fito. "Ko lafiyar wannan jinjira wannan kuka ai yayi yawa Yaya Auwala" Cewar Sabitu. Dubanshi Auwala yayi tare da jin sanyi a ruhinshi jin ɗan uwan nashi gudan jininshi ya kirashi da Yaya. Allah sarki rayuwa. ( Da ace mata zasu gane rarrabe kawunan ƴaƴa ba abu bane me kyau, ba kuma hanyace mai ɓullewa ba da sun huta. Ƴan uba ba abokan gaba bane. Ƴan uba abokan junane dangin junane.) Gwadabe ne ya fito da jaririya a hannunshi tana shiɗewa. "Wai lafiya Gwadabe Hadizan bata gidanne yarinya take irin wannan kuka na fitar hayyaci" Auwala ya tambaya. "Tana ciki taƙi karɓar yarinyarne kawai. Idanunta biyu tana ji. Iskanci da wulaƙanci take ji" "Kaji aikin rashin hankali na Hadiza ko. Ku bani waje in shiga in ci ƙaniyarta wawuya kawai" Cewar Mammada daya ƙaraso wajen. Ya amshe yarinyar yanata jijjigata. Allah sarki shi gashi haihuwar suke nema idanu rufe Allah bai basu ba. Ita Hadiza ta samu tana shirme. "A'a Mammada banda duka kasan anyi mata tiyata abi komai dai a hankali." Cewar Auwala kenan. Auwala ya dubi Sabitu yace. "Kaje shiyyar su Yaya Tasi'u ka taso su zata gane kurenta." Da sauri Sabitu ya tafi aiken da Auwala yayi mishi. Gwadabe ya nufi ƙofar ɗakin Shafa da jaririyar ya shiga aikin buga ƙofar Shafa. Buɗe sakata tayi Gwadabe ya shiga da jaririya a hannu ya miƙa ma Shafa. Ba musu tasa hannu ta karɓi yarinyar. "Ki bata Mama tasha, ki barta a wajenki tunda uwar bata sonta" "To amman kafa..." "A'a ni ban sanki da musu ba Ina girmamaki akan hakan. Ki sani nasan abinda nake yi." Haɗiye maganar dake bakinta tayi ta koma kan kujera ta zaro Mama ta zura ma jaririyar a baki. Nan ta soma tsotso tana sauke ajjiyar zuchiya" "Allah yayi miki albarka Shafa nagode ƙwarai da wannan soyayyar. Matsayinki na musamman ne" Yasa kai ya fice. Shafa ta girgiza kanta tana mamakin hali irinna Hadiza. Fitowar Gwadabe daga ɗakin Shafa yayi daidai da isowar Yaya Tasi'u harda Anti Badi'a dake biye dasu. A falon Hadiza duk suka taru. Gwadabe ya basu labarin iyakar dalilin Hadiza na azabtar mishi da yarinya da tayi. "Wallahi Yaya Tasi'u haƙurina ya kusan ƙarewa akan sha'anin fitinar Hadiza. In taso in kai ƙarane bazan iyaba. Ni wannan matsalar sabuwace a cikin rayuwata. Ni wallahi tsohuwar matata kafin ince tayi take yi. Haka ma Shafa take yi mun. Amman fa Hadiza ita kullum a ƙoƙarin ganin laifina take duk iyakar kyautatawar da nake yi mata." Hadiza tana tsakankanin yayyenta kanta a ƙasa sai jijjiga kanta take yi da dukkan alamu dai maganganun bakin Gwadabe suna dukan ranta in akai la'akari da Iyabo da Shafa da shi Gwadabe ya ambata. Gyaran murya Yaya Tasi'u yayi yace. "Allah ya kyauta. Ni na ɗauka wani gagarumin abune ya shiga tsakaninku ma da wallahi bazan ko sakko daga gadona akan wannan shirmen ba ko Auwala ya isa yaba Hadiza kashi. Kaga Gwadabe kar ka bari ƴan uwantaka ko zumunci ya hanaka gyara gidanka. Kai kasan komai akan abinda yaita gudana a baya a cikin gidan Malam. Duk da muna fatan komai ya zama tarihi tunda ga Sabitu abun sha'awa a zaune a gabana a ɗakin Hadiza kuma. Ke kuma Hadiza ni zan fi so ki kashe aurenki ki kima cikin gida ki dinga kallon rayuwar tsohon mijinki da tsohuwar kishiyarki. Ku kuma ku tashi kowa yaje ya kwanta." Ai nan Hadiza ta ɗago kanta ta dubi Gwadabe duba na wulaƙanci, ta maida dubanta kan Yaya Tasi'u tace. "Wallahi Yaya Tasi'u Gwadabe ba adali bane. Yafi fifita Shafa da yaranta dan kawai tana da maza a...." "Tas tas Yaya Tasi'u ya mari hadiza. Auwala ya zuba mata ranƙwashi a tsakiyar kanta, Sabitu ya zubo mata harara. Mammada da Gwadabe ne suka kwaceta dan Auwala zagewa yayi yana neman dukanta sai da Anty Badi'a tayi saurin shiga tsakani. "A_a Baban Sailuba karfa kuyi kisan kai fa. Yarinyarnan ɗanyan jego take yi, aiki kuma akayi mata. Ke Hadiza tashi ki shiga ɗaki kinji. Gwadabe ka kawo mata jaririyar tata." Da gudu Hadiza ta shige ciki Sabitu ya bita da mangari Allah ya sota bai sameta ba. "Wawuya shashasha in baki yi sa'a ba gobe zan sa Zara ta daka mun ke a gidannan" Cewar Yaya Tasi'u kenan a tare suka fice Gwadabe kuma ya kulle ƙofa yayi kwanciyarshi a doguwar kujera yana tubka yana warwara. Cin mutuncin da Babala da Yaya Hambali suka yi mishi sai dawo mishi yake yi. Yana mamaki ainun ace uwa ta tsugunna ta haifi ɗa ta dena sonshi. Duk da Yaya Hambali shine kanwa uwar gami a tsakaninsu. Mafi yawa_yawan lokaci Yaya Hambali ke zuga Babala ya harzuƙata ta hasaka har ta dinga furta mishi kalaman da basu dace ba. Wayarshi ce ta shiga kuka ya zaro a ajjihu yaga Bara'u ne. "Kayi haƙuri ban kiraka naji kun sauka lafiya ba sai kaine ka ɓige da kirana. Ina fatan kun sauka lafiya?" Bara'u yace. "Lafiya lau ka gammu a tsakar gida ma da yaran du. Zuwa jibi sassafe zan kwashi yaran muje Kano gidan Uwanin. Inma bamu je wajen Iyabo a jibin