← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 237

Sashe 162

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mishi da murmushin ina share hawayena. "Nagode Jabu yanzu kin ƙaramun kuzari, nutsuwata ta dawo jikina ni zan tafi kiwo" To Allah ya tsare mun kai ya kareka. Inaso inna gama aikace_aikace zani gidan Cubu ance bata jin daɗin jikinta" "Assha to Shikenan sai kin dawo, kya gaisheta" Da haka mu kai sallama na koma cikin gidan. Ƴan tsurko sai kallona suke yi, ni ko bansan ma suna yi ba. Nazo na tarar Uwani ta gama wankin ɗauraya take yi. Tare mu kai shanya muka je ɗakin Yafendo muka karya. "Jabu kwanannan ina lure dake bakya komawa ɗaki har sai wannan yaron ya dawo ko ƙarfe nawa zai kai. Ga rama kinata yi, inna tambayeki Jabu sai kice babu komai. Amman ni ko a fuskarki inna kalla sai inga damuwa ƙarara. Ki sanar dani abinda ke damunki Jabu, ni Mamanku ce baki da wacce zaki sanar ma matsalarki daya wuce ni, ko dai rasa idanunki guda da kika yi ne kika saka abun a zuchiyarki yake ta nuƙurƙusarki? Ki sani bawa baya wuce ƙaddarar da Allah ya ƙadarto mishi. Kuma har gobe bamu cire rai ba anata neman magani in da rabo sai kiga idon ya dawo kinci gaba da gani dashi. Murmushi nayi kamar yadda na saba, kaina na ƙasa gudun karta gane ƙarya nayi mata nace. Babu komai Yafendo. Wannan ramar ta canjin yanayi ne kawai, sai ɗan zazzaɓi dake damuna a tsaitsaye kuma ina shan magani. Rashin shiga ɗaki zafine kawai yayi yawa dake a cikin zafin muke. Sai naga tana murna ƙila tana tunanin ko ciki ne dani. Au ai kuwa makon jiya ya kamata inyi jinin al'ada kuwa amman banyi ba. Na faɗa a raina" "To masha Allah. Muga hannunki " Saina miƙa mata, ta duba tafin hannuna sai tayi dariya tace. "Sai ki dinga yin komai a hankali. Girkinma ki dena yi Baɗɗo in tayi ta zuba miki, ke dai kiji da kanki, wannan yaron abinci ba damunshi yayi ba dama" Duk sai kunya ta lulluɓe na fahimci dai Yafendo taga ciki ne dani. Sai naji wani farin ciki marar musaltuwa nake jina kamar wannan cikin shine cikin fari. Allah ya bani mai albarka, wanda zasu ji tausayina. A nan Yafendo ta fita ta barmu anyi haihuwa a maƙota zata shigar musu barka. Na sanar mata zamu shiga muma gidan barkan, daga nan kuma zamu je gidan matar Baɗejo. "Ke baki san ma kina da ciki ba? Ni ko kinga ina ganinki ki kai mun kama da masu sabon ciki sabida naga kinyi haske. Amman da banji kince kina da cikin ba sai nake ganin ƙila sabida ramar da kika yine yasa kika yi fari. Nifa na mance ban faɗa miki ba Gwadabe yaje gidan Hajiyarmu nema na fa" Take gabana ya tattake ya faɗi, zuchiyata ta tsinke jin an ambaci Gwadabe. Na yi jim ina tuno Gwadabe na, da irin rayuwar da muka gudanar duniya kenan. A duniya banyi tunanin ko a mafarki aurena da Gwadabe zai ƙare ba. Bayan ya ƙaren banyi zato ko tsammanin zan so wani ɗa namiji rabin yadda nake son Gwadabe ba. Ashe ba haka bane so da ƙaunar Yaya Hamma a zuchiyata ya dakushe tauraruwar Gwadabe a zuchiyata ta yanda ba'a iya hango ƙyallinta ko misƙala zarratan. Sai dai ina gani girma Gwadabe fiye da kowa, ina girmama ƙoƙarinshi a kaina. Yarana suka faɗo mun ai sai hawaye." "Au harda kuka Iyabo dan kawai na ambaci sunan tsohon mijinki?" Gwadabe yafi ƙarfin kawai Uwani kema kin sani. Kar kiyi tunanin da ɓirɓishin son Gwadabe a zuchiyata alhalin da aure a kaina. Wallahi ko ɗaya, kuma nasan yin hakan laifine. Sunanshi da kika ambatane ya tuno mun da irin zaman da muka yi. Kukan da nayi kuma yarana na tuno kawai. Neman me Gwadabe yake miki, neman jin labarin inda nake ko? Gwadabe manya. Ina mishi adda'ar Allah yasa yana cikin aminci tare da yarana, ina mishi fatan samun macen da zata soshi fiye dani " "Kamar kuwa kin sani. Har lambata yaso karɓa Hajiya ta hana tana gudun kar Hafizu ya zargi wani abun. Kinsan tunda na soma kasuwanci Hafizu ya soma mun baƙin ciki, da yaga maza sai ya koresu a shagona. Na kulle gidan na koma gida satina daya yaita sintiri kinsan ba zuchiya gareshi ba, ga talauci na damunshi a gidan nawane yake samun abinci me kyau ya kwanta a lallausan zanin gado. Nifa Allah auren Hafizu ya fita raina. Kuma a yanzu haka ciki gareni, amman inaga ko wata ɗaya baiyi ba ma To Hajiya dai ta faɗa mishi kina aure a garin da mahaifiyarki take. To sai dai tace ta mance bata tambayeshi yayi aure ko baiyi ba. Ta dai tambayi yaran yace suna cikin aminci sunata karatu" Allah sarki Gwadabe nagode sosai. Inason ganin ƴaƴana in sha Allah inna shigo Kano zan ɗaukeki mu shiga takai ko tsirenine Babala sai dai tayi" "A'a ki rufa ma kanki asiri. Mijinki kishinshi da yawa kiyi zamanki ni zanje in dubo miki su da izinin Allah. In kuma sun girma babu mamaki Gwadabe ya dinga kawo miki su su kwana biyu. Amman ki samu matsalolin da kike ciki su warware. Wato Iyabo idon naki ya mutu da guda ɗaya kike gani? Allah mai iko mata muna ganin jarabawa iri da kala a gidajen aure, sai dai muce Allah ya bamu mafita. Tashi mu je mu dubo Cubu, daga nan muje gidan Dada ko?" Sai da mu kai wanka, Uwani ta shiga ɗaki ta ɗakko mun kaya nasa. Mu ka je ɗakin Baɗɗo ta tayani muka buɗe dila sabida ta cika ma Baɗɗo ɗaki, inaso in raga mu kai gidan Dada. Kayane gangariya na yara, mis dana jarirai masu kyau. Na jariran muka ware waje guda basu da yawa sai kawai nace ni da uwani mu raba tunda cikine damu. "Aa ni na tara kayan jira jirai da yawa kin mance na saida dilar kayan yara? Ki ajjiye dai zasu miki amfani, tunda basu da yawa sai kawai ki ɓoyesu kinga in aka baki kuɗin kya yi wani abun dasu." Muka ware kayan kashi kashi. Muka ɗaubi ƙunshi biyu wanda zamu tafi dashi gidan Dada na ware ma yaran Hamma, da yaran Baɗɗo, da yaran Amaduyal, Safiya ma na ɗaukarma yaronta guda ɗaya, matar Baɗejo ma haka. Me jego da zamu shiga mata barka ma zanzo in duba mata kala ɗaya ranar suna in bata dan muna mutunci sosai ta kanyo zuwa na musamman wajena mu yi hira duk ranar da bata je tallar Nono ba. Da muka fita gidan Dada muka soma zuwa sabida kaya da muka doro a ka ni da Uwani niƙi_niƙi muma muka saje da matan ruga. Daga gidan Dada ne bayan mun yi azahar sai muka tafi, na ba Dada ɗari biyar nace ta yi musu girki ga yaran Jatau ma suna gidan suna wasa. Da Sallama muka shiga gidan Cubu. Kishiyoyinta suna tsakar gida ko wacce na aikin gabanta. Gidan a share yake ƙal suna da tsafta sosai ko bokatan gidansu babu kazanta a jikinsu labulayen bukkokinsu kuwa tas'tas haka jikkunansu ma tas. "Sannunku Jabu anzo duba marar lafiya kenan?" Cewar kishiyar Cubu wacce acewarsu ita akaima kishiya tunda kafin zuwan Cubu itace Amarya, mata ta uku kenan. Na fahimci kamar tafi sauran guzumayen sauƙi dansu sunci sun ƙoshi suna da manyan yara gaisuwar arziki basa amsawa ni shi yasa ko kallonsu banyi ba. Na amsa ma kishiyar Cubu da cewar. Wallahi kuwa nace dai bari inzo in dubata. Ina wuninku?" In kun tanka sun tanka mu dai muka shige bukkar Cubu tana kwance ba yadda take duk ta bushe ta komaɗe, ga zafi amman tana ƙunshe a ɗaki tana fifita. Ganinmu ne ma yasa taji daɗi. Cubu kina zaune ke kaɗai a wannan zafin ga matan gida a waje kowa na shan iska ba zaki fita rumfarki ki sha iska ba?" Cikin rawar murya tace. "Adda inna fita sai suita zubar da habaici suna zagina wai Dadana ma taƙi zaman aure da girmanta amman aurenta ya mutu, mu bamu da tarbiyya muna ma kishiyoyin Dada rashin kunya. Dake kishiyata ta biyun ƙawar Baba Dije ce, ko ɗazu Baba Dije tazo wajenta. To Adda sai suita azabtar dani, kuma ranar girkina babu wanda yake taimakamun, ko da bani da lafiyannan basu ɗauke mun komai ba, kuma ina jin ƙaurin kara zanta hararwa" Ƙuri muka zuba mata ido ni da Uwani. Kafin muyi magana sai ga kishiyarta da nono cikin ƙwarya yaji sikari da dambu ta ajjiye mana. Cubu har wannan kishiyar taki da naga kamar tafi manyan kirki bata taimaka miki?" Sai Cubu ta ɗanyi murmushin da yafi kuka ciwo. "Adda wannan matar muguwar makirace tunda nazo gidannan take ƙullamun makirci a wajen mai gidan. Bata so taga ya ambaci ko sunana" Uwani tace. "Amman yaya tsakaninki dashi kuna zaune lafiya baya cutar dake?" Cikin kunya tace. "Baya cutata, yana bani haƙuri kullum akan halayen matanshi shima sunfi ƙarfinshi ne. Kuma yana kawo mun nama da lemun kwalba a ɓoye, shi kaɗai nake iya ci" Ajjiyar zuchiya muka sauke dukkanmu. Uwani tace. "Komai zai zo miki da sauƙi tunda mai gidan baki da matsala dashi. Shawarata anan shine ki zage ki ƙwaci ƴancinki babu wanda zaizo ya ƙwatar miki ƴanci. Karki bari habaicinsu ya hanaki fita ki wataya, yadda kowa yake a zube a tsakar gida yana shan iska kema ki dinga fita. Yanzu lallaɓa ki fita mu gyaggyara miki ɗakin naga duk tarkace, in kin samu lafiya ki roƙi mijinki ya saki a makarantar dare da Iyabo take koyarwa kema ki samu ilimi." A darare Cubu ta fita, kai kawai na girgiza ina mamakin wannan rayuwa. Tas muka gyare mata ɗakin nata kayan wankinta Uwani ta haɗa tace zata tafi dashi ta wanko Yusufu ya kawo mata. A tsakar gidan muka sameta tanata sheƙa amai uwargidan tana kanta tana faɗa akan tana musu ƙazanta kamar a kanta aka soma ciki bayan ta shigo gidan ta gansu da ƴaƴansu. Ta inda matarnan take shiga ba tanan take fita ba. Mu dai bamu ce komai ba Uwani ta gyara wajen ta zuba ma Cubu ruwa ta wanke mata fuska ta kamota suka dawo tabarma ta saka mata fulo ta kwantar da'ita." Sannu Cubu. Zan yima Dada magana a turo miki
Chapter 162 · 0% Book details