← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 237

Sashe 5

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwadabe:.

Tunda ya shiga ɗakin Babala, Babala ta tare shi da ruwan faɗa itace harda kukan ta ji labarin Iyabo ta shanye shi, ta mai sheshi Ɗan aikinta. Duk ta hanyar da yaso ya ɓullo mata dan ta fahimci dalilin da yasa yake mata aiki, amman Babala ta fututtuke. Su Goggo Iyatu suma suka ara suka yafa, mai makon su rarrashi ƴar uwarsu sai ma sake zugata da su kai ta yi.
"Wallahi Kyauta wannan lefinki ne. Dan wallahi da nine Tanimu ya kwaso mun ƙabila da sunan matar dazai aura. In sama da ƙasannan zata haɗe bazai aureta ba. Ki duba yanda ya shure soyayyar ƙanwarsa Laila fa Kyauta. Da ba dan na kai zuchiyata nesa ba da zumuncinmu ai ya taɓu" ( Kyauta sunan da dangi ke kiran Babala dashi kenan. Babala kuma sunan da ƴaƴa da jikoki ke kiranta kenan) Cewar Goggo Iyatu kenan. Goggo Jummalo tace.
"Ai yanzu ma bata ɓaci ba Iyatu. Har yanzu Gwadabe zai iya auren Laila. Tunda har Laila ta iya kaso aurenta domin tana son Gwadabe .Ya kamata a wannan karon ya aureta ko dan dole dan ubanshi a nuna mishi mu muka haifeshi ba shi ya haifemu ba. Wallahi a wannan karon aurenshi da Laila babu wata makawa." Da sauri Gwadabe ya ɗago jin labarin mutuwar auren Laila ba ƙaramin kiɗimashi lamarin yayi ba. Ga wata magana da Goggo Jammalo take faɗe, shi yanzu ina ya ga ta yin aure alhalin abinci ma da ƙyar yake iya kaiwa gidanshi, har yanzu bai soma sana'a a matsyin ogan kanshi ba. Ta yaya ma zai auri Laila? Wannan ma maganace da bata dace ace an ma tare shi da'itaba, duba da irin halin talaucin da yake ciki, da kuma babban dalilinshi na ƙin Lailan a bayan. Da ƙyar Gwadabe ya yakice ya bar ɗakin Babala yana yarfe zufarshi. Yana hanzarin barin shiyyar ya jiyo muryar Laila a bayanshi tana kiranshi.
"Gwadabe ji mana dan Allah " Cak ya tsaya bai juyo ba, bai da niyyar juyowar. Sai itace ta tako har inda yake, ta fuskanceshi.
"Gwadabe guduna kake yi ne?" Kallonta Gwadabe yayi, tare da girgiza kan shi.
"Tayaya zan guje ki kina gudan jinina Laila? Na ga ai mun gaisa ko, ko akwai wani abunne bayan wannan?" ÆŠan murmushi Laila ta yi tare da cewa.
"Babu komai. Ka ji labarin mutuwar aurena, da musabbabin mutuwar tashi ko?"
"Ai kina jiyo duk bayanin da su Babala suke yi mun. Allah ya daidaita tsakaninku da mijinki. Laila in da gaske dan ni kika fito daga ɗakin ki, kin tabka babban kuskuren da zaki jima kina cizon yatsan ki. Sam ni Gwadabe bani da ra'ayin ƙarin aure, lafiya lau muke zaune da Iyabo, bata rage ni da komai ba, ta bani dukkan lokacinta da zuchiyarta. Haka zalika ni ma zuchiyata tana gareta. Ina mai baki haƙuri a karo na biyu." Yana dasa aya ya wuce ya barta da jin kunya.
Yana tafe yana mamakin irin ƙiyayyar da su Babala suke yi ma Iyabo, duk da dai shima irin wannan tsanar akayi mishi a gidansu Iyabo. Da dama a cikin gidansu Iyabo basa ko amsa sallamarshi. Bayan sallar la'asar kuma Babala tasa akayo mata kiran kab yaran nata, dan Haula ta tsokata mata abinda ya faru a can gida Kano da safe kafin su tawo. Shine wannan wucewa da Iyabo taga sunyi. Bayan sun gurfana a gaban Babala da Goggo Iyatu, da Goggo Jammalo, da Goggo Takura. Duk waɗannan ƙannen Babala ne, babban wansu Baba Magaji shi yana Maraɗi tare da iyalinshi. Nan Yaya Hambali ya soma yi ma Babala bayanin abinda ya faru, harda ma waɗanda suka wuce.
"Babala Iyabo ta gama mallake Gwadabe, shi yake yi mata komai da kika sani. Wallahi Babala har ruwan wanka sai Gwadabe ya kai mata, haka zaki ga ta fito tana kallon su Haula ɗaɗɗaya. Duk abunda Gwadabe ya samu akanta yake ƙarewa tas. Ai kin ganta sai ƙiba take narkawa, shi kuma yana ƙarewa kamar wanda ake lasa. Ni shi yasa nace su bar mun gidana kawai, dan ba ƙaunar buɗe idanu nake in ganta a cikin gidan ba Babala. Tunda har Gwadabe ya soma takamun burki, wataran sai duka. Kafin akai ga hakan gara su tashi kawai, ina da buƙatar wajen nasu dama zan zuba dabino a ciki. Babala irin taɓarar da Gwadabe da matarshi suke yi a cikin gida kare fa bazaici ba. Wallahi sai ki ganshi da gajeren wando yana barbaɗa mata garin Amala ita tana tuƙawa sunayi suna waƙar yarbawa. Wannan baƙin ciki da mi yayi kama" Yaya Harisu yace.
"Gaskiya ne gara ya kama mata haya a can nesa damu Babala. Ƙazantar da baka gani ba tsabta ce. Dan wannan yaron baya ko jin kunyar idanunmu, wallahi zaki ganshi a tsakar gida yana wanki tana mishi shanya, wataran har waƙar yarbawa zaki ji suna rerawa abun takaicin ya iya waƙar. Gwadabe ya rasa wacce yake so duk dangi, duk cikin ƙabilunmu na Hausa fulani kyawawa, sai wannan buskutar beyerabiyar ce ta ja hankalinshi." Haka ɗaya bayan ɗaya kowa ya goyi bayan Gwadabe ya bar ma Yaya Hambali gidanshi. Shi kuwa gogan yayi ƙuri yana jiran irin hukuncin da Babala zata yanke. Gyaran murya tayi tare da cewa.
"Na ji bayananku kab, kafin ku koma za ku ji hukuncin dana yanke. Zanyi shawara da ƴan uwana, akan batun matarshi kuwa wannan ƙabilar? Alkadarinta ya riga ya kusan karyewa. Ku tashi kuje in Allah ya kaimu gobe zaku ji hukuncin dana yanke" A sanyaye Gwadabe ya bi bayan ƴan uwanshi. Zuchiyarshi cike da ƙuna gami da taraddadin me ka je ka zo.

Iyabo:
. Sai zuwa bayan isha na samu hutu. Duk mun baje a tsakar gida muna shan iska. Ina kwance akan tabarma nayi matashin kai da hannuna. Toye yana zaune a gabana. Ƴan uwa sai hira da shewa suke ta ta yi abun gwanin ban ƙawa, ni kuwa mujiya na kasance a cikinsu, komai a tsorace nake yinshi, bana son in ɓata ma dai_dai da yaron gidan na goye rai. Ina gani ɗazu yarinyar Asiya matar Lawal tana dukan Toye, babu wanda ya kula. Gashi ba sa'arshi bace dan zata yi shekaru tara da doriya ma. Sai da ta gaji dan kanta ta barshi.
Ina kwance barci ya soma dibata Yaya Halima ta zo inda nake tai mun ƙerere a ka.
"Mandiya hamshaƙiya sai ki taso ga can kayan miya da su alayyawo zaku gyara, gobe da asuba za'a aza tukunya" Da sauri na miƙe ina faɗin wash dan wani irin ƙara ƙuguna yayi mun mai zafin gaske. Toye na kwantar ya riga ya soma bacci a zaune. Tunda muka zauna zaman aikinnan ba mu bar aikin ba sai wajajen sha biyun dare, sannan kowa ya kwanta. Da asussuba kuwa washe gari muka tashi da aikin tuwo, dan kafin takwas na safiya mun kammala tuwonnan tas mun malmalashi mun jera a fantekoki. Zuwa ƙarfe sha ɗayan rana gidan biki ya cika danƙam da jama'ar biki, sai haya_haya kawai kake ji. Daga waje ma haka ƙofar gidan take danƙam da maza ƴan ɗaurin aure. Yaron Sakina ne yazo ya kirani.
"Umman Toye wai inji ummata kizo ki yi wanka" Allah sarki ni Iyabo. Kowa a gidan sai wanka akeyi ana kwalliya, yara da manya. Amman ni babu wanda yai mun ta yin wanka. Bin bayan yaron nayi har zuwa gidansu. A falon Sakina na samu Gwadabe da Bara'u suna zaune suna cin tuwon biki. Ƙur ya ƙura mun idanu, take na ji hawaye na shirin zubo mun, har numfashina na karkatsewa. Fitowar Sakina daga uwar ɗakine ya katse kallon ƙudan da muke ma juna.
"Maman biyu tun ɗazu nake ta jiranki ki zo ki karya ku yi wanka ke da Toye, sai mu ka ji shiru kuma" Kujera na samu na zauna duk illahirin jikina babu inda baya yi mini ciwo, kuma babu inda bai yi mun tsami ba, zazzaɓi ne kau a jikin nawa ma, ga jiri da ke damuna.
Ke dai bari, aikin abincin bikine bai bani damar zuwan ba. Kinga ko karyawa ma ban yi ba. Bara'u ina kwana ya akaji da taro?" Na faɗa kaina a ƙasa.
"Lafiya lau Iyaa Toye Tsuntsun soyayya, ya jiki_ jikin?"
Alhamdulillah. Na dubi Gwadabe nace. Ekaro oromi ( ina kwana mai gida?) Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
"Kin tashi lafiya, ya jiki_jikin naki? Wato kina ta aiki bayan kinsan likita ya hanaki aiki mai wuya ko? Gobe ma kowa zai watse daga yau biki ya ƙare, tunda yau za'a kai Amarya ɗakinta ai" Boyayyar ajjiyar zuchiya na sauke, dan jina nake tamkar a ƙaya wallahi. Zame jiki Bara'u da Sakina su ka yi su ka bar mana ɗakin. Suna fita Gwadabe ya dawo kusa dani ya zauna.
"Iyabona" Ya faÉ—a muryarshi na rawa. Kuka na fashe mishi dashi.
Gwadabe na roƙeka da girman Allah ka sauwaƙe mun zuwa taron biki ko suna na danginka. Ba ƙaramin muzanta nake yi ba. Ka ware mana wasu lokutan domin ziyarar danginka, amman ba lokacin wani sha'ani ba." Shiru yayi yana kallona idanunshi suka kaɗa su kai jawur.
"Ki ƙara haƙuri bisa wanda kike yi da dangina Iyabo. Nasan kina takura sosai, kuma kina shan baƙaƙen maganganu marasa daɗin saurare. Amman ni ko na so barinki a Kano, kinsan ba yarda Babala zata yi ba. Kuma hakan zai ƙara haddasa wata fitinarne. Iyabo bana son kukan ki, ki share hawayenki gobe da wuri zamu bar Takai ki yi haquri kinji?" Sai na ji tausayinshi ya kuma kamani, ga ɓoyayyar damuwa ina gani shinfiɗe a fuskantar shi, duk da yana ta ƙoƙarin ganin ya ɓoye mun halin da yake ciki. Amman na san Tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. A hankali na furta.
Gwadabe na ganka a cikin damuwa meke damunka, kar kayi yinƙurin ɓoye mun, dan bama ɓoye ma juna damuwarmu. A kai nane ko Gwadabe?" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da kamo hannayena dukka biyun ya ɗan matsesu kaɗan. Idanu na lumshe ina cike da tsantsar tausayin aurenmu.
MRS BUKHARI

*DAN ALLAH KUIMUN AFUWA NA SAURARI ƘORAFE_ƘORAFENKU AKAN KU WATA BIYU YAYI MUKU YAWA. AYIMUN AFUWA MU BARSHI A WATA BIYU, NA SAKE TURO WANNAN PEJINNE DOMIN IN MUKA DANNAR ƘIRKI DASHI. NAN DA WATA BIYU ZAKU JINI DA CI GABAN LABARIN NAGODE*🙏🏻🙏🏻
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
Chapter 5 · 0% Book details