Sashe 18
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
miƙa mishi ya shafa kansu yai musu adda'a ya miƙo mana su. Sannan ni yai mun adda'ar samun lafiyar shayar dasu cikin lafiya, Gwadabe kuma yayi mishi adda'ar samun tagomashi ta yanda zai ciyar dani lafiyayyen abincin da zan raini yarana cikin ƙoshin lafiya. Iyaa Debisi ta fito itama tayi nata addu'o'in, aka miƙa ma Babala abun magana, "Allah ya raya su da imani" Kawai tace shima sabida idon mutanene da taga sun yi yawa a kanta. Iyaa Kokodeen itama ta yi nata, su Burodami kokodeen da Burodami Debisi duk dai kowa yayi nashi.Daga nan kuma akayi adda'a kowa ya shafa. Sai Bose ta ɗauki kwano ta dinga bin mutane ɗaya bayan ɗaya sunata zuba kuɗi, mu kuma muka koma cikin jama'ar suna. Dangina rankatakab ɗinsu ankon atampa mai ruwan kunun kanwa ce a jikinsu maza da matansu. Abinci aka soma rabawa masu kalangu kuma suka amshe fagen. Haka dai akaci gaba da gudanar da shagalin suna bamu muka tashi ba sai ƙarfe biyun rana. Daga nan kowa ya watse, duk wani gudunmawa a wajen aka bani, sai da muka cika bahun biyu da kaya da atampopi, kuɗi kuwa na same shi sosai ƴan biyu sun yi goshi sosai. Bayan mun koma gida sai na sake wanka na kwalliye da shaddar da Ayashe ta bani na fito shar dani. Sai lokacin na samu nutsuwa naci abinci na ba ƴan biyu nasu abincin. Kafin la'asar har an gama soye naman suna tas Anty Mulka ta ƙuƙƙullama duk waɗanda suka dace, ni dai da Gwadabe cikin ƙaramar samira kawai muka tsira dashi a matsayin rabonmu. Ragon ɗaya sukutum aka ba su Babala, ɗayan kuma ni da ƴan uwana duk muka rataya akai, wanda na samun ma Babala ta aiko laraba wai in ƙara mata nama ƙawayenta na Takai basu samu ba. Dan haushi samirar duka na miƙa mata na yi kwanciyata dan in ɗan huta. Washe gari Ayashe ta ɗau hanyar garinsu, da rana su Sakina suma suka wuce. Uwani dasu Bose ne suka gyara mun ko'ina su kai mun girkin dare kafin magriba duk suka watse ɗakin daga ni sai ƴaƴana misalin taran dare sai ga Gwadabe ya shigo furkarshi ɗauke da fara'a, nima murmushi na sakar mishi. MRS BUKHARI