Sashe 16
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiryawa nayi cikin doguwar rigar Atampa, ɗaya daga cikin kayan da Alaja ta bani, atampar mai kyauce kuma tana da tsada da gani. Hijabi mai roba_roba na saka kalar atamfar sak. Na ɗauki Taiwo na goya, Kahinde kuma Sakina ta goya shi. Uwani zamu je asibitin Murtala Babala tana can bata da lafiya gara in je kar in yi wani babban laifin. "To sai kun dawo, nima ƙoƙari nake in gama gyare miki uwar ɗakin yadda ya kamata. Gobe za'a zazzo da yawa. A nan ma ni zan kwana gobe na koma gida Hafizu baya nan ya tafi Lahadin makoli mahaifinshi bashi da lafiya. Yaran kuma suna gidanmu " nace da'ita. To Shikenan ma, sai mun dawo to. Sakina muje." Shigarmu ward ɗin mata ke da wuya na hangi su Yaya Haula dukkansu a zazzaune a tabarma da mazajen nasu. Kallona suka shiga yi da suka hangoni. Sannunku Yaya Haula ya mai jikin?" Sai da ta taɓe bakinta tace. "Jiki da sauƙi" Gaishe da su Sukairaju nayi tare da yi musu ya mai jikin. Yaya Harisu cikin murtukewa yace. "Da'u ka kai su wajen Babala su gaisheta" Da'u yayi gaba muka bi bayanshi har bakin gadon Babala, tana zaune ta jingina bayanta da matashin filo. Yaya Halima kuma tana tsaye tana haɗa mata tea. Muna isowa Babala ta kawar da kanta gefe. Sannu da jiki Babala, ya ƙarfin jikin? Na furta muryata har tana rawa. "Da sauƙi" Ta bani amsa ciki_ciki. Yaya Halima kuwa nunawa tayi bata ma san Allah yayi ruwan tsaron mu ba. Gaisheta nayi tare da yi mata ya mai jiki. Babu yabo babu fallasa dai ta amsa mun. Da Sakina ne dai su kai fara'a. Sunto Taiwo nayi na miƙa ma Babala ita, tasa hannu ta amsheta, Sakina ta ƙara matsa da Kahinde. "Ba shakka gashi nan yara sun ɗebo ƙoƙon asali. Kamanninsu sak da dangin uwarsu dai kamar yadda Toye yabi sunanshi." Iyakar abinda tace kenan ta miƙo yaran. Raina ya sosu ainun ko Allah ya rayasu bata ce ba, balle ta yi musu adda'a a matsayinta na kakarsu. Yaya Halima kuwa ko kallo yaran basu isheta ba. Bayan na gama goyo ne ta kalleni sak tace. "Na ji saƙonki na gode da har kike tunanin mahaifinki ya fi mahaifin Gwadabe daraja a wajenshi. Burinki ya cika yaranki uku babu wanda Gwadabe yayi ma takwara a danginshi. Har ni da na ɗau jimirin renon cikinshi na wata goma ya kasa saka sunana ma ƴarshi. Taiwo da Kahinde ɗin dai da kika sanar, shima shi ya jaddada a matsayin sunan yaranshi. Ko da yake dama tuni kun gama tsarin komai tun ma yaran suna ciki." Baki na buɗe inason in ba Babala haƙuri amman sai ɗaga mun hannu tayi. "Kije kawai, bana son ganinki, bana kuma ƙaunar zamanki da Gwadabe, zuchiyata ba zata taɓa samun salama ba madamar kina amsa sunan matar Gwadabe abadan" Cikin razani da tashin hankali mai girma na shiga. Lokaci guda Gwadabe da aurenshi ya fice mun a raina kwata_kwata. Na yi alkawarin inayon arba'in zan tursasama Gwadabe sakina ko dan ya ga haske a rayuwarshi, domin na fahimci har abada Babala ba zata taɓa ƙaunata ni da abinda na haifa ba, wannan shi ake kira NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE. Ko Gwadabe bai sake ni ba, ni kuma zan fice a rayuwarshi.Wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke a hankali na soma tafiya dan barin ɗakin. In sha Allah ƙarshen aurena da Gwadabe yazo, ko da kuwa soyayyarshi ita zata zam silar numfashina. Fitowa daga ɗakin ke da wuya, na jiyo Harisu yana zagina tare da ƙorafi kan sunayen yara da aka saka. Sai ji nayi na muzanta ko fita ma bazan iyaba. A tsaye Sakina ta iskeni. "Ki ƙara haƙuri dai Iyabo damo sarkin haƙuri. Mu je kinji" Da taimakon Sakina na iya fitowa, amman har muka isa guda ban iya furta ko kalmar A ba, sai ajjiyar zuchiya kawai nake saukewa. In sa abinci a cikina wallahi na kasa sabida tsabar damuwa. Sakina da Uwani sai aukin rarrashina suke yi, amman na kasa ce musu komai. Ni tunanina ya na ga samarwa Gwadabe sauƙi dan fishin iyaye masifa ne, nayi imani fishin da Babala take kwana ta tashi dashi akan Gwadabe shi ya hana shi yin arziki. Kullum cikin faɗi tashi yake, ta hana kowa ya taimaka mishi. Yaya Hambali shago gareshi babba a kasuwa da yake siyar da dabino da gyaɗa, buhu_buhu yake siyarwa yana da yaran shago sosai. Amman Babala ta hana shi ya ɗauki Gwadabe ko da a matsayin yaron shago. Yaya Harisu shi kuma mota yake ja zuwa ƙauyuka a haka ya sai wasu motocin guda biyu ya bayar anayi mishi hayarsu. Sukairaju kifi bushasshe yake saidawa a kasuwa, shine zuwa argungi, shine zuwa maiduguri, da Yawuri saro katan katan na kifi, kuɗi yake samu sosai da sosai Ɗan fodiyo kuma Kafinta ne kuma ogan kanshi ne. Da'u shi kuma Yaya Hambali ne ya buɗe mishi shagon sai da kayan masarufi dangin shinkafar hausa, gyadar miya, masara, wake. Duk wannan matakan sun haushine da taimakon Allah da taimako da jajircewar Yaya Hambali, domin Yaya Hambali guda ne harda ɓari ga ƴan uwanshi, yana musu tsananin so. Ina lokaci yayi da zan fita fit a cikin wannan ahalin, nima in je in yi rayuwa mai kyau. In ba haka ba bala'o'e iri_iri zasu iya saukar mana a sakamakon fishin da Babala take yi da Gwadabe. Abubbuwa nawa Gwadabe ya kama suka lalace, yayi sana'o'e a ƙalla iri huɗu karen mota shine na biyar. Amma tafiyar bata wani nisa sai abun ya lalace, ko mai gidanshi ya koreshi, ko a yi mai wani ƙazafi, ko na sata ko na ƙashin tsiya." "Iyabo ga tea ki daure ki sha, wala Allah ruwan nono yazo miki. Kinga Taiwo da Kahinde kuka suke yi baki ma sani ba. Kar ki kuskura waccan munafukar ta falo ta fahimci kina cikin matsala, yanzu ta shigo. Surukar taki ma an sallamota tana ɗakin umman Nazifi." Hannu nasa na amshi tean hannun Uwani na sha, dan jikina har rawa yake yi tsabaragen yinwar da nake ji. Sakina ta miƙo mun Taiwo da take ta canyara ihu kamar wacce ake zare ma rai. Ga man zaitun da audiga Sakina bani in goge kan mamana in gwada musu ko zasu jawo ruwan yazo" Miƙomun Sakina tayi, na bi kan mamana na goge da man zaitun tas na ba yaran suka soma ja. Cikin ƙudurar Allah sai ruwan nono ya soma zuwa. Nan kuka yaƙare aka shiga tsotseni. A wannan daren bana ce na yi bacci mai kyau ba. Misalin ukun dare sai ga Gwadabe, a lokacin duk su Uwani suna kan gado sun yi bacci ya shigo. Ganinsu ne yasa ya koma falo, ni kuma na ɗebo jariran na biyo bayanshi, yana zaune a kan kujera. Laila kuma tana kwance tana bacci ta yi baje_baje cinyoyinta duk a waje. Miƙa mishi yaranshi nayi yasa hannu ya amshesu yana fara'a. "Maman biyu barka da sauka, ina fatan babu inda yake miki ciwo ko?" Babu, sannu da dawowa" Iyakar abunda na faɗa kenan shima ciki_ciki. Idanunshi yana kan yaranshi yace. "Ya dai akwai wani abu dake damunki ne, ko an yi wani abunne? Iyabo a yanzu ya kamata ace kin saba da komai. Ki toshe kunnuwanki dan abubbuwa da yawa zasu faru kafin ayi suna kema kuma kin sani. Yanzu haka nafi awa ɗaya da shigowa Babala naketa ba haƙuri tayi fishi wai ban mata takwaraba ita da mahaifinmu. Nace mata zan sake yin sabuwar huɗuba in hakan zai bata farin ciki. Amman taƙi fur tace mun in na sake ma yaran suna bata yafe ba, wallahi kar kiji......." Ɗan yatsana nasa a kan laɓɓana nayi mishi halama da yayi shiru, nuni nayi mishi da Laila dake kwance. Ai ba shiri ya haɗeye maganarshi. Mu ka ɗan taɓa hirarmu kaɗan, ya miƙo mun ledoji manya biyu, mu kai sallama dashi zai kwana a ɗakin zaure, ɗakin su Nazifi, Bara'u ma yana ɗakin. Da tunane_tunane na ƙarashe daren nawa, sai jefin asuba bacci mai nauyi sosai ya ɗebeni bani na farka ba sai taran safe lokacin ƴan uwana sun ƙaraso, har an yima ƴan biyu wanka sun fito ras dasu, dan Gwadabe ya kawo kayan jariri kala biyar biyar, sai nawa na fitar suna kala biyu, da takalmi da mayafi, sai sarƙa, dasu nabkin, da paints na yara, da man shafawa, da sabulu. Ɗayar ledar kuma kayan abinci ne a ciki. Ina farkawa Yemisi tace. " Lo we. ( Je kiyi wanka)" O dara ( To) Kawai na iya ce mata na ɗauki zani na lulluɓe jikina dashi na fita. Ina fitowa maƙotanmu suka soma shigowa barka. Matan gida kuwa babu wacce ta leƙo, sai aikace_aikacensu suke yi kawai. Bayan jama'a sun ragu sai na fita zuwa ɗakin Yaya Haula dan gaishe da Babala. A falon na tarar da Gwadabe da Bara'u gurfane a gabanta. Ɗan fodiyo yana gefenta yana ɓallo mata magungunanta. Gaisheta nayi da jiki, da ƙyar ta kada baki ta amsa mun. Ɗan fodiyo na gaishar kafin na gaishe da Bara'u da Gwadabe. Ni dai anan na tafi na barsu. Da tuwon masara miyar kuka da bushasshen kifi Uwani ta tare ni, harda tea mai madara, ina bacci Gwadabe ya shigo da kayan tea. Anty Mulka ce ta shigo ciki tace. "Wai Iyabo su dangiin mijinki basa zuwa taya aikine? Tun sassafe muke ta aiki a tsakar gidanku, amman babu wacce ta taya mu komai. Mun fitar miki da randunanki tsakar gida, wata bushasshiyar mace tazo tana faɗar maganganun banza, har tana dangantamu da ƙazanta. Mu fa ba zamu ɗauki irin wulaƙancin da sukai mana lokacin sunan Toye ba. Bga won ( ki ja musu kunne) sai in zaune mace ni yadda nake da ƙibarnan" Nan Bose da Kauliya suka ɗauka suma sai yare suke ta yi mun. Uwani ce tai ta basu haƙuri ni kam kuka na saka musu kawai. Ganin kukan nawa ne yasa su kai haƙuri. Tun ganin da naima Gwadabe a falon Yaya Haula ban kuma saka shi a idanuna ba. Da rana Iyaa Debisi ta aiko mun da farfesun kan akuya cikin kwano shi naci da rana, su kuma suka dafa taliya. Uwani na kira nai mata raɗar ta zuba ma Babala