← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 237

Sashe 129

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ga abinci Adda Jabu. Baɗɗo har yanzu bata gama girki ba shine nace bari in kawo miki" Murmushi nayi mata nace. To Nagode kwarai Safiya" Tana fita uwani ta shigo da gaushi. "Gashi kishiyarki ce ta bani. Kinga wata yaluwar atampar data saka wai ita tayi kwalliyar yamma? Wuyan rigar baya ko zama tsabar yadda yayi mata yawa, ta ko rambaɗa jar hoda fuskarnan tayi jawur." Dariya muka tuntsire dashi. Baɗɗo ce ta shigo da tiran abinci. Shinkafa jallof tayi da kifi, sai fura da dambu cikin jug ɗin silba. "Adda wannan nono da Dambun na Yaya Hamma ne. Kullum sai ya sha babu fashi nasan baki sani ba shine nayi miki. Ga abincinku. Adda Uwani muje muci namu Yaya Hamma ya dawo yana wajen shanu" Kwanukan abincin Safiya na mika ma Baɗɗo. Ungo ko yaranki sa ci, wannan ya isheshi ni a ƙoshe nake" Ta karɓa suka fita. Suna fita na ta da sallar Isha. Ina zaune ina lazimi Yaya Hamma ya shigo da sallama hannunshi riƙe da baƙar leda babba. Da sauri na miƙe na amshi ledar hannunshi na ajjiye a gefe. Zama yayi a kujera yana sauke ajjiyar zuchiya da gani a gajiye yake dan idanunshi sun lumshe da ƙyar yake buɗesu. A gefenshi na zauna. Sannu da dawowa Yaya Hamma " Hannuna ya riƙo ya matse a nashi, ya zuba mun idanunshi da yake lumshesu. "Amarya kinyi kyau. Ɗakinki yayi kyau sosai, tsarin ya burgeni" Murmushi nayi mishi kawai. Ina ka shigane tun jiya rabona dake. Murza hannuna yayi yace. "Ke dai bari, yadda naci burin daren jiya bai kasance yadda na tsarashi ba. Yarinya ba ita ta samu bacci ba sai asuba, ina dawowa masallaci kuma na wuce gidan Baffa Musa yana nemana. Acan na daɗe daga nan kawai saina wuce wajen aiki dan nasan gidan cike yake da mata. Aimun afuwa in ran gimbiyata ya ɓaci, ba da nufi komai ya faru ba. Su Inusa ma ƙorafi suke yi mun wai ban kawosu sunci tuwon Amarya ba" Ɗan murmusawa nayi nace. Ai babu komai. Ciwo ya doke komai ai, ciwonma na yarinya ƙarama. Su Iyaa sun tafi yau, uwani kuma sai jibi so take tabi Baɗɗo suje cin kasuwa akwai abubuwan da take son ta sassarane" "Uwani baiwar Allah. Wannan ƙawancan naku yana bani sha'awa gaskiya. Ina muku fatan ya dore har ku haɗa ƴaƴanku auratayya" Ameen. Yanzu dai me kake son ka soma, wanka, ko cin abinci? Naji sai warin rana kake yi" Duk wannan hirar a shingiɗe yake a kujera hannuna yana cikin nashi yana murzawa. "To wanne kika ga ya dace dani? Ni wanka ai sau ɗaya nake yi, wani sa'inma sai in kwana biyu gaskiya banyi ba, sabida yanayin aiki da kiwo" Dariya nayi, shima dariyar yayi yace. "Sai kinyi haƙuri mijin naki ƙazami_ƙazamine" A'a ba haka bane. Kar ka damu wannan duk ya kau daga yau. Wanka sau biyu safe da dare in sha Allah. Bari in kai maka ruwan wankan ka watsa sai kazo mu ci abinci, ga nono da dambu yana jiranka" Ina faɗin haka na miƙe na juye ruwan filas ɗaya a bokitin ƙarfe, na fita waje randata tana bakin ƙofata na surka mishi ruwan, na haɗa mishi da soso da sabuluna na kai mishi. Yaje yayo wankanshi tsab, na dangwalo mishi dakakken gawayi wanda aka cakuɗa da alim nace. Goge bakinka tas Yaya Hamma " Murmushi yayi ya amsa ya tsugunna a ƙofar ɗakina ya jima yana goge bakinshi. Ni kuma ina ciki na haɗa mana tea na zuba mana abincin Baɗɗo. Na zuba miyar stew da uwani tayi mana taji soyayyan kifi sukunbiya. Tare a plate ɗaya muka ci abincin, kaɗan yaci ya ɗauki nono da dambu ya sha, ni kuma na sha tea. "Akwai kazar amarci a ledar dana shigo da,ita ki ɗakko" Ai sai dai da safe mayi karin kumallo da'ita a yanzu gaskiya na ƙoshi. Gaga_gaga muka kammala duk abinda ya dace, muka ɗauro alwala muka yi sallar nafila bisa Shari'a. Daga nan al'amura suka soma sauya salo, daga ƙasa zuwa kan gado. A hankali abubbuwa masu daɗi da wuyar fassaruwa sukaita gudana. Har abinda aka daɗe ana mafarki ya tabbata a tsakaninmu. Abinda ya curemu muka zama guda kenan. Abinda ke ƙara soyayya da shaƙuwa a tsakankanin ma'aurata. Yaya Hamma yayi mun bazata, dan banyi tunanin tattali irin wacce na samu ba, asalima ban kawo irin wannan tattalin ga mutumin ƙauye ba, sai gashi ya kere tunanin Iyabo. Dan wallahi Gwadabe da wasa bai taɓa kaini irin wannan duniyar ba. Shima kuma na fahimci na kaishi duniyar da babu fulani a cikinta. Wannan yanayin ya ƙara mana so da shauƙin juna sosai. Bayan komai ya lafa muna kwance muna mayar da numfashi, Yaya Hamma ya juyo ya zuba mun idanunshi masu haske kamar madara. Abu ɗaya da ya bani tsoro shine na fahimci Yaya Hamma kamar baya aski ko ince baima taɓa yi ba irin yadda na fahimci yawan gashin. Amman nasa a raina zuwa washe gari zai aske shi tas. "Jabu soyayyarki ta kasance ta daban a zuchiyata. Kin kafa babban tarihi a wannan daren mai ɗumbun nasara da tarihi. Allah yayi miki albarka. Nagode da kika tallafi soyayyata baki hofantar dani ba. Wallahi Allah shine shaidata da ban sameki ba, komai zai iya faruwa dani, ina nufin komai. Ina roƙonki komai sauyin yanayi dana zamani kar ki gujemun, kar ki juya mun baya" Mun jima a wannan daren muna ma junanmu alƙawarurruka masu nauyi da girma. Daga ƙarshe tare dashi muka je banɗaki mu ka yi wankan Sallah. Duk da yana noƙewa tare da jin tsantsar kunyata, har rufe idanunshi da tafukan hannunshi ya dinga yi. hakan bai hanamu yin nishaɗi ba. Yanayi ne mai kyau, irin yanayin da na jima ina mafarki kenan Allah baisa na samu tare da Gwadabe ba, sai gashi na samu a wajen Yaya Hamma. Bacci mu ka yi mai daɗin gaske, baccin da saura ƙiris Yaya Hamma ya rasa sallar asuba. A gurguje ya zura rigarshi mai warin hammata da warin awaki ya fita. Idanu na lumshe tunanina yana mayar dani daren jiya da ni'imomin dake kewaye da daren. Marata na shafa ina fatan Allah yasa Yaya Hamma yayi ajjiyar jininshi a marata in haifa mishi kyakkyawan santalelen saurayi me kama dashi ya samu abokin shawara. Da ƙyar na fito nayi alwala wani irin muƙu_muƙun sanyi ake busawa sosai. Ina idarwa na kunna risho na dafa ruwan tea na zuva a filas na ɗakko wannan kaza na ɗorata akan plate. Na mayar ma da Yaya Hamma ruwan wanka. Yana shigowa na kai mishi ruwan wanka, ya tafi ya yo wankan. Ni kuma na shiga cikin gidan. Matan gidan duk suna kitchen ɗin tsakar gidan ko wacce girki takeyi a murhunta. Wani irin murhu garesu ginanne mai kyau, da laka ake ginashi, sai ɗan ramin dora tukunya. Duk ramuka bibiyu akaima ko wanne murhu, nawa yana kusa dana Hama sabo dal dashi har fenti akeyi mishi. Ɗakin Yafendo na shiga muka gaisa sannan na fito na nufi kitchen din. A dokin ƙofar kitchen ɗin na tsaya. Hama na dafa madarar shanu ta ɗago muka haɗa idanu. Ta wani turɓune fuska wuyan rigarnan nata a sauke nonuwanta rabi da kwatansu duk a waje. Wani tsohon kitsone a kanta duk ya furje. Ga gashi dai yala_yala amman babu gyara duk abun katifa ya rirriƙe gashin haka ma kan yaranta yake. Babbar ƴarta me sunan Yafendo tana gefenta riƙe da kofi hancinta sai yoyyo yake yi. Duk sanyin da akeyi kan yarinyarnan ba ɗankwali, ƙafarta babu takalmi ba suturar arziki. Maman Dada ina kwananku? Hama ta juya kai ta mayar da hankalinta akan madarar da take dafawa. Sai su Fatu da Safiya ne suka amsa muka gaggaisa. Baɗɗo ta gaisheni tare da cewa. "Yanzu nake son in kawo muku madara ku karya" To sai in tafi da'ita. Maman Dada kayan Yaya Hamma zaki bani yayi wanka yana son sauyawa" Sai ta saki muciyar da take juya madara ta juyo a fusace. "Shine ya aikoki ko zuwa kikayi ki sanar dani ya kwanta dake kome kike nufi Jabu? To bazan bayar da kayan ba shi bashi da ƙafar da zaizo ya ɗauki kayanne." Taja dogon tsaki ta fice fu a kitchen ɗin, saida taso bangazata na matsa da mugun sauri. Dariyar Uwani na jiyo daga bayana. Harda tafinta Uwani ƴar duniya kenan. Nima darawa nayi kawai. "Sai haƙuri Jabu. Yanzu Maman Dada a cikin fishi take" Cewar Safiya wacce na lura tana da hankali. Ba komai Safiya komai zai daidaita. Baɗɗo bani madarar" Madara ta miƙomin cikin kofin silba na nufi inda Uwani ke goge bakinta. "Wannan kishiya taki sai kinyi da gaske. Irin wannan daga miki murya da take yi haka, sai kace uwarki?" Ke dai bari Uwani. Bari in sallami Yaya Hamma zan zo in sameku, ƙila ma muje kasuwar tare in ya barni dan inason in yi siyayyar kayan miya da abinda ba za'a rasaba ƙila yau muna da baƙi masu cin tuwon dare. "To Shikenan sai kin shigo maza aje a kula da megida" Komawa nayi ɗaki na tarar da Yaya Hamma yana karyawa. Harka soma karyawa Yaya Hamma? Murmushi yayi mun. "Na gama ma. Inaso in fita kiwone yau nama ɓata lokaci sosai." Kallonshi nayi ya miƙe tsaye nace. To Allah ya tsareka ya dawo da kai lafiya. Yauwa Yaya Hamma nace abokan naka su nawa ne zasu zo zan musu girkinne?" Hularshi ya mayar kanshi kana yace. "Mu shida ne." To dan Allah inaso zan raka Uwani kasuwa siyayyarta da yawa kuma nima ina buƙatar zan ɗan yi siyayya". Jim yayi kamar bazaiyi magana ba dai. Sai yayi dariya kuma yace. "Da ƙafa suke zuwa cin kasuwar fa, mota wuya take yi sosai in zaki iya to kuje sabida dai Uwanine amman da bazaki ba" Nera ɗari biyu ya bani yace. "Ga kuɗin cefananki nan sai ki sai abinda zaki siyo acan yafi arha. Ki karɓi garin tuwo da ɗanyan man shanu a wajen Hama zan mata magana ta baki" A gurguje mu kai sallama ya fice. Kayan karin na tarkata na fito na nufi tsakar gidan. Yaya Hamma yana ƙofar ɗakin Hama da sandar kiwonshi, mijin Baɗɗo kuma yana kaɗa shanun waje. Bance musu um ba na wucesu kamar ma
Chapter 129 · 0% Book details