← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 237

Sashe 133

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kunsan abu dama in aka haɗa da mata. Ana cikin haka wata safiyar talata Shafa ta haifo ɗanta namiji santalelen gaske, ta haihu da kwana biyu matar Auwala ta haihu itama, sai akace za'a haɗe bikin sunan. Hadiza kuwa jiki yayi nauyi sosai sai turawa take yi tana lallaɓawa a hakan ita take ɗorama Shafa ruwan wanka, Baba Fhatsima kuma ita ke ma jaririyar wanka Anty Badi'a kuma ita ke ma Shafa wanka, da ɗora ruwan wankan yamma, ana jibi suna ƴan takai suka iso harda Sakina da Toye akazo. Aka haɗu harda Hadiza akaita sha'ani tare da tsare_tsaren yadda sunan zai kasance. Ranar talata Yaron Gwadabe yaci sunan mahaifinshi aka mishi alkunya da Abba. Yaron Auwala yaci sunan Malam ana mishi alkunya da Magaji kamar yadda shima malam ake mishi alkunya da wannan suna. An gudanar da bikin suna lafiya za'ace kasancewar ba'ai wani taro mai yawa ba Shafa bata da dangi a ƙasar. Gwadabe yayi ƙoƙari ƙaton rago ya yanka ma mai jego, ga naman ƙauri saida ya kwana biyar yana kawowa ba tare daya gajiya ba. Kayan fitar suna Shafa kawai yayi ma kala biyu, ita Hadiza yace inta haihu zaiyi mata. Ita kuma atampa da rigar yaro mai tsada ta ba Shafa. A ranar suna da daddare gaga_gaga sai Hadiza ta kama ciwon naƙuda. Wasane gaskene taita abu guda Anty Badi'a na kanta har saida akai sallar asuba kana ta haifo ɗiyarta mace mai kama da'ita tamkar an tsaga kara." Da uwar da ɗiyar suna cikin ƙoshin lafiya. Hadiza tana yin wanka tasha tea sai bacci. Su Anty Badi'a da Ene data bugo sammakone suka kintsa wajen akaima jaririya wanka ta fito tubarkalla a cikin farin seti sai bacci take yi. Matan Auwala da Mammadane suka shigo barka, me jego tana kwance tana baccin wahala, har su Auwala suka shigo da angon ƙarni Gwadabe bata tashi ba. "Gwadabe an sake zama angon ƙarni. Gata ku ganta" Anti Badi'a ta miƙama Gwadabe yarinya ya amsheta da bismillah ya shiga yi mata adda'a, sai ga Ayashe da Sakina harda Shafa mai jego tana riƙe da jaririnta. Taiwo da Kahinde, da Toye suna biye dasu. Yaran da suka zamema Gwadabe sanyin idaniya, yaran da yake jinsu a ranshi fiye da komai da kowa. Baya jin akwai wani ɗa ko ƴa da matanshi zasu haifa mishi da zai sosu sama da nasu Toye sai dai ƙasa. Soyayyar babarsu tana nan a ƙasan zuchiyarshi. Yanayin jini da ya ga Taiwo sai yaga Iyabo sak, kuma dama yarinya jikinta irinna Iyabonne dan ƙiba gareta. "Shafa har dake a fitowa? Ai da kin zauna kema ba jegon kike yi ba" "A'a Anty ai babu komai nazo inga ƙanwar Abbane, in ma Maman Abban barka" Ta faɗa da fara'arta. Anty Badi'a ta karɓi Abba a hannunta. Aka gaggaisa duka su Sakina duk sukai ma Gwadabe da su Anty Badi'a barka. Me jego bata san wainar da ake toyawa ba tana uwar ɗaku. "Me jegon bacci take yi. Amman inta tashi zan faɗa mata" Cewar Anty Badi'a. Gwadabe yace da Sakina. "Sakina zaman maraɗi ya ƙara kamaki dan sai anyi suna zaki tafi" Dariya tayi tace. "Ai nima haka nace. Duk da su Toye zasu koma makaranta, amman zamu zauna ayi suna damu" Aka ɗanyi wasa da Dariya dai, su Gwadabe suka tafi aiki. Mata kuma suka ci gaba da zuwa barka. Gaga_gaga haka akaita jego, kullum Gwadabe na siyo naman ƙauri itama yai mata na kwana biyar. Har ana jibi suna gwadabe bai sanarma Hadiza sunan da yaima yarinya huɗuba dashi ba. Da daddare bayan sun gama komai suna kwance suna hirar ma,aurata sai tace. "Nifa har yanzu baka sanar dani sunan yarinyarnan ba, ko nima sai ranar raɗin sunan zanji?" Ta ƙarashe tana dariya. Shi kuwa duk saiya koma kalar tausayi. "Dama tun ranar da nayi mata huɗubar nake ta tauna yadda zan tunkareki da zancan" Ai saita miƙe zaune ta ƙanƙance idanunta tace. "Kar kace da sunan tsohuwar beyerabiyar matarka kaima ɗiyata takwara?" Dama yasan za'a rina, baiyi mamaki ba. "E da sunanta nayi huɗubar ina fatan zaki amshi hakan. Nayi alƙawarin saka sunan nata ga ɗiya macce da zan samu ta fari....." "A'a Gwadabe mu bar zancannan dan narantse da Allah ba zaka ma ƴata huɗuba da sunan wata ba. Uwata na da rai ba'ai mata taƙwaraba sai tsohuwar matarka daka kasa mancewa da'ita" Take ranshi ya ɓaci nan suka haura shima ya farfaɗa mata maganganun da yasan dole ranta ya sosu. Ya suri fulo yayi ficewarshi zuwa falo. Ya barta a gado tana risgar kuka wiwi kamar wacce aka aikoma da saƙon mutuwa. Wani irin muƙu_muƙun kishin Iyabo yaita fisgar ranta. Washe gari ta tashi cikin fishi da ƙuncin zuchiya. Haka ta wuni sukuku, zuchiyarta cike da fargaba kasancewar Gwadabe a ɗakin Shafa ya kwana sai su Sakina ne suka tafi ɓarayin Yaya Tasi'u suka kwana. Bata san ya canja sunan yarinyar ba ko yana kan bakarshi nasa mata sunan matarshi? Haka gari ya waye, ga mai jego taci kwalliya ta fito shar cikin shadda bazin wacce ta siya da kudinta irin adashennan da malaman makaranta ke kafawa, ta fito tayi ɗan karen kyau yarinya ma tasha ƴar kanti me riga da siket. Tsakar gida ta fito tanaso tayi magana da Anti Badi'a, nan kallo ya dawo kanta. Su Sakina suna bakin magudana suna aikin kayan ciki, Gwadabe ya shigo da ƙaton rago, Mammada na biye dashi da ƙatuwar tinkiya duk aka rataye mata a barandarta. Saita shiga mamakin shin rago biyu ya yanka mata kenan sabida yasa sunan tsohuwar matarshi? Ita kuwa taci alwashi in sama da ƙasa zata haɗe ɗiyarta ko sunan Shafa ba zata ci ba balle sunan tsohuwar matar mijinta, alo tsiya alo danja. Shafa ta fito daga ɗakinta da kayan Ƴan biyu itama sai taga raguna biyu a ƙofar Hadiza a rataye ga kayan ciki cikin ƙaton bawo su Ayashe sunata gyarawa. Masu yanka kabeji,da masu yanka kaji nayi gidan ya kacame da aiki da halama sunan na dabanne. Dan matan gidama sai ɗan fitowa suke yi gulma. Matar Mammada da Matar Auwala dake ɗauke da ciki na wata shida suma suna tsakar gidan suna aiki, banda ƙannen Hadiza da kawayenta duk kowa aiki yake yi, ga Hadiza ta sha Bazin asalin babbar me geza. Ƴan biyu dake guje_guje a tsakar gida Shafa ta kira da hannu, a guje suka isa gareta, ta jasu ɗaki Gwadabe ya bita da kallo dan yaga kamar akwai ɓacin rai tattare da'ita bazai wuce akan raguna biyu data gani ba, da suturar jikin Hadiza ba. Yana gama ratayewa ya nufi ɗakin Shafa ko kallon Hadiza baiyi ba. "Gwadabe mufa har yanzu ba'a sanar damu sunan wannan jaririya tamu ba" Anti Badi'a ta katse mishi hanzarinshi. "Sunanta Fhatsima. Alkunyarta Ummi" Ajjiyar zuchiya Hadiza ta sauke ranta yayi fes. Anti Badi'a ta saki guɗa tana faɗin. "Baba Fhatsima dole tayi mana fantimoti na takwara. Bari in shiga cikin gidan in sanar." Dariya Mammada yayi yace. "Sun rigaku jin sunan tun asubar fari ai. Sai dai in akwatin zaki karɓo" Dukkansu suka saka dariya. Gwadabe a bayan gidan Shafa yayi wanka ya kintsa, ya fito ya sameta tana wasa da ƴan biyu. "Shafa" ya kira sunanta, ta ɗago ta zuba mishi idanu ba tare da tace komai ba. "Raguna da kika ga biyu. Yaya Tasi'u ne ya ba Hadiza ragon ni tunkiyar na siya. Kar kiga tafi taki girma wallahi yanayine kawai duk da nasan tafi taki tsada. Suturar jikin Hadiza da hidindimun da kikaga anayi, wasu ita da kuɗinta tayi, wasu matar wanta Anti Badi'a mace mai karamci ce tayi mata. Kiyi haƙuri kinji ko, umman Abba?" Murmushi tayi, shima murmushin yai mata. "Babu komai Allah yasa mu dace. Haka dai akaita girke_girken suna a gidan abinci saida akayi kusan kala uku, ga cincin da alkali, harda soɓo da kunun gyaɗa duk saida akayi. Me jego da yarinya kuwa sunga gata sosai. Dan hatta Gwadabe kayan da Yaima ummi baima Abba ba, sai haƙuri ya ba Shafa akan zai ƙaro musu in ya samu kuɗi. Washe garin suna tun sassafe aka kafa kaskon suya. Su Sakina suka shiga shirin komawa najeriya, Hadiza ta ɗeba musu nama mai yawa sosai da cincin da dubulan. Baba Fhatsima kuma ta musu tsarabar lalle ɗan nijar mai mugun kamu da yankan salateb harda gishirin lalle wanda ake kwaɓawa da toka a shafa sai lalle ya dawo baki wudik. Har sun fita Gwadabe zai rakasu tasha sai ga wayar Tamu yana roƙon a bashi Shafa tazo tayi wankan gida. Tamu ya wuce ya nemi abu ya kasa samu a wajen Gwadabe. Babu shiri suka ɗaga tafiyar zuwa washe gari. Shafa saita shiga murna tana haɗa kaya. Gwadabe ne ya kai zancan gaban uwar ɗakinshi Baba Fhatsima. "To ai babu lefi tunda ka amince, kaga sunyi kawaici ma dan da wasu ne kafin ta haihu zasu zo su tafi da'ita. Babu damuwa Allah ya tsare" Ita ta sanar ma Malam washe gari suka kama hanya sai Najeriya. Kan Gwadabe ya ɗauki zafi dan a ranar yana da zuwa wani ƙauye cin kauwa zai kai magani ba ƙaramin ciniki yake yi ba. Sai ya sha'afa bai sanar da Hadiza batun zuwa wankan shafa ba sai a bakin Shafar taji da taje mata sallama. Alhamdulillah sana'ar saida magani tana kai mishi sosai babu laifi, har magungunan ƙarfin maza da su yaji dakan maza yake siyarwa, abu kamar wasa saiya soma haɗawa da ƙwayar bature duk dai na mazan. Kuma yana zaga ƙauyuka dan cin kasuwa, yana ciniki sosai babu abinda zaice da Allah sai godiya. Koda ya dawo ga gajiya, ga hayaniyar kasuwa saida Hadiza ta tareshi da ƙorafinta. "Ashe kasan Shafa ba zama tayi ba za'a tafi da'ita wanka shine baka faɗa mun ba." ( Mata mu dinga lura da lokacin daya dace mu shigar da ƙorafinmu ga miji. Kuma mu sani mu tsaya a iyakar matsayinmu dan kare mutuncin kanmu, musamman in kina da abokiyar zama) A faɗace yace. "Ai ba huruminki bane dan Shafa zata wankan gida saina sanar dake ba. Tunda ta miki sallama ai Shikenan. Da dawowata kin tarbeni da ƙorafi'" Yana faɗar haka ya shige ɗaki yana ta tauna al'amura lamarin Hadiza ya soma isarshi gaskiya mace sai shegen ƙorafi shi kenan kullum
Chapter 133 · 0% Book details