Sashe 198
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muka haÉ—a kai da matan gida, da Æ™awayen Hama na maÆ™ota, da danginmu kusan mu rai ashirin, ko wacce da goyonta, wasu da yara a hannu raÉ“e_raÉ“e muka nufi gidan suna. Sai an hau keken shanu ake isa ruggar su Hama. Rugarma babu yawan bukkoki É—an Æ™aramin wajene. Tun daga nesa muke hango mata sunata shiga gidan sunannan. Da sallama muka shiga yuu. Yara na guje_gujensu manya anata hidimar gyaran kayan miya, masu tsintar shinkafa nayi. Gidan nake kallo ko da dai taro akeyi amman da gani gidan Æ™azamai ne babu ko shakka. Kuma irin gidajen talakawan fulaninnan da ko akuya basu mallaka bane. Abun mamaki duk dangin Hama sun san Daso sai ambaton sunanta akeyi. Ni dai ina biye dasu har cikin wata bukka. A ciki muka tarar da Hama É—are_É—are a gado da jaririyarta a gefenta. Kanta an yarfa mata kitso jelarnan har gadon bayanta, ga Æ™unshi tayi jawur dashi, har jaririyar akaima Æ™unshin hannu da Æ™afa. Akwai wasu dattijai biyu a É—akin, da wata yarinyar mace a zaune a kan gadon da hama take. Ƙaremun kallo Hama ta shiga yi, tana kallon suturata, wani irin mugun kallo take yi mini. Hmm Waje muka samu mu mu uku muka zauna ragowar suna daga waje. Sannu mai jego, ashe kin sauka. Ina wuninku?" Na Æ™arashe zancan da gaishe da matan É—akin. Ko sun fahimci nice kishiyar Hama sai naga anyi mun amsawar wulaÆ™anci. Ni dai daman nasan za'a rina sai naja bakina na tsuke. Duk motsi Hama idanta na kaina. Ita bata gaisheni ba, ni dana daure na gaisheta sai tayi funfurunfus taÆ™i amsawa tana daga Æ™wance suna magana da Daso. BaÉ—É—o ce ta miÆ™e zata É—auko mana jaririyar É—ayar yarinyar macen dana ce muku tana zaune a bakin gado sai tayi carab ta damÆ™e hannun BaÉ—É—o" "Yarinyar bata da lafiya kar ki ma soma É—aukarta mai son ganinta ya ganta a haka" Maganar da tsawa_tsawa da iskanci take yi. Hassanne ya soma kuka sai na suntoshi zafi na shirin kashemu. Ya haÉ—a zufa yayi sharkab. Duk matan É—akin wallahi sai suka zuba ma yaronnan ido. Da naga haka saina miÆ™e tsaye. Zan É—an fita daga waje in basu Mama, nan É—in akwai zafi. Ga wannan Æ´ar gudunmawatace babu yawa" Na ajjiye ledar na ja hannun BaÉ—É—o muka fice." "Lallai saifa kin tashi tsaye. WaÉ—annan yaran maza kyawawa sune yaran kishiyar taki shine kike kwance kike bacci? Ai in dai da yarannan to yaranki sun zama bola a wajen Hamma" Karab a kunnena duk da dai da fullanci tayi maganar na ji tsab abinda tace É—in. Bansan kuma wacece ba dai. Ni dai na ja turmi a tsakar gida ina shayar da biyu ina tofesu da adda'a. Yaran duk wanda ya kallesu Allah sai ya Æ™ara. Sabida haskensu gasu da jiki kunsan yaro mai Æ™iba anfi sonshi, gasu Æ´an biyu abun yayi musu yawa. Muna dai zaune su BaÉ—É—o sun shiga anata aiki dasu. Ni dai bansa hannuna ba kuma bazan kuwa saka ba in ji da kallon banzan ma da akeyi mini. Muna zaune da Safiya da Adda A'i yarinyar Baffa Musa muna ta hirarmu har azahar ba'a gama girki ba, har mu kai Sallah. Ni kuma yarannan gasu da tsotso yunwa ta kamani sosai. Kuma ni ko karen hauka ya cijeni ai bana sa abincin gidansu hama a bakina ba. Wallahi aka sauke abincinnan akaita rabo ni dai har abincinnan naga babu har an zuba ma tukunyar abincin ruwa. Ba'ace ku ga naku ba, amman fa iyakar mu mu ukunnan da muke zaune dan BaÉ—É—o dasu akai komai an zuba musu to batayi tunanin ba za'a bamu ba saita cinye abunta. Hmm sai wajajen uku na yamma aka kawo mana abincin. Shinkafa da miyace a mugun jaÆ™ale shibkafar kamar fate, miyar kuwa yadda kukasan markaÉ—aÉ—É—iyar kabewa wai miyar stew ce. Ni dai gaskiya loma ban sa a bakina ba. Awarar nono na fita na siya naci na danne daa ruwa. A hakan ma Sai naji zuchiyata na tashi da Æ™yar na mayar da aman da nake ji. Muna yin sallar la'asar muka nemi hanyar garinmu. Nasha habaici sosai. Ko wacce figaggiya sai kaji tana me za'ayi da Æ™iba, ai anfi yayin mata sirara. Wata ma bata da maraba da cry fish amman sai fi'ili. Saida muka fito na sauke ajjiyar zuchiya na shaÆ™i iska da kyau. Washegari na tashi da kunce tsaraba da rarrabawa. Wajajen azahar na wuce gidan Dada acan muka wuni cur miyar dana tawo da'ita rabi na zabtare na kawo mata. Acan na iske Cubu da yarinyarta. Cubu wai har yanzu ashe baki koma ba?" "Bata koma ba kin ganta nan. Ni nasa an kira mun mijin nake tambayarshi ko lafiya. Yarinyarnan in laifi tayi ni ya sanar mun ya daga zuwa wankan gida zai hana yarinya komawa É—akinta. HaÆ™uri dai kawai ya bamu. Ni fa jikina ya mutu gaskiya ruwa baya tsami banza" Jikina ya mutu nima. Tabbas ruwa baya tsami banza akwai wani abun a Æ™asa. Kishiyoyima ai ba zasu barta ba. Amman babu komai akwai Allah. Shinkafa fara na dafa mana har dare mu ka ci Dada nama huÉ—u manya nasa mata da kifi, da ganda tana ci tana shi mun albarka. Ni dai tun bayan la'asar daf magriba saina soma jin wani sabon yanayi a tattare dani dai haka. A daddafe nayi Sallah ina zaune nayi tagumi sai nake jina kamar wata marar lafiya haka. Ganin É—alibaina sun soma shigowane yasa na É—an sake kaÉ—an na Æ™warara kaina. Nan muka soma karatuttukanmu bayan mun gama na baje musu kayayyaki. Allah cikin ikonshi janbaki da gazal É—aÉ—É—ayane kawai yayi ragowa du sun kwashe komai nerata dubu ashirin cas a cikin jakata. Bayan nayi Sallah saina goya biyu nayi ma Dada sallama muka kama hanyar gida ni dasu BaÉ—É—o. Æarayin Yafendo naje na kai mata nata shinkafa da miyar nai musu sallama na shige É—aki na kwantar da Æ´an biyu ina zaune ina harhaÉ—a kan kuÉ—aÉ—en ciniki, da kuÉ—aÉ—en da nazo dasu, da wanda Burodami Debisi ya bani. Sai naji gabana yayi mummunar faÉ—uwa. Ba shiri na dafe Æ™irjina na runtse idanuna. Daga haka sai nayi maza na miÆ™e tsaye na cusa kuÉ—aÉ—ennan a jaka. Na saÉ“a biyu a bayana, na mayar da mayafina na suri Æ™aramar jakar da kuÉ—ina ke ciki. Wallahi tiryan_tiryan ba saina fice a gidanba na naushi hanya, inayi ina haÉ—awa da gudu_gudu. A lokacin wata guguwace nake jin tana tashi a kaina, ji nake kamar zan rasa rayuwata inna ci gaba da shaÆ™ar iskar Jaɓɓi lamba. Hakanne yasa na shiga gudu_gudu burina in bar rugar kawai. Babu wani tunani a kaina, bana iya tunanin komai burina na barin garinne. Ina fitowa kan iyaka na samu mota ta cika zata Girai saina faÉ—a motarnan. Ina zaune shiru kaina na wani irin zafi da ciwo. Gaga_gaga muka iso Girei. Na kuma samun motar cikin gari nanma na shige. Banfa san ina zanje ba, ni dai burina inyi nisa kawai. Muna shigowa tasha aka saukemu. Nayi tsayuwata a gefe nayi shiru. Nafi minti sama da talatin a wajen. Wani É—an wuniyonne yace. Hajiya ga rumfa can da Æ´an uwanki mata kije ki zauna mana. Hala kema fasinjar Lagos É—ince? Gashi motar ce ta samu matsala tashi sai gobe da sassafe. Ko kin fita ba zaki samu abun hawa ba" Haka nabi bayan bawan Allahnnan izuwa rumfar da matannan suke. Harda masu goyo. Waje na samu na zauna shiru. Hankalina baya jikina bansan meke mun daÉ—i ba sam. Amman nasan nice Iyabo, Hassan da Usaini ƳaÆ´anane iyakar abinda kaÉ—ai nake tunawa kenan fa, duk rayuwata da asalina ya goge a kaina bansan kowa ba sai kaina da Æ´aÆ´ana fa. Allah gwanin iko da hikima. Allah ya tsare duk mata da sharrin kishiya mai asiri. Gata ayi fito na fito, ko makirci ko kuita cin uwar sabada a tsakar gida. Duk macen da aka taÉ“a yima asirin gusar da hankali da tunanine kaÉ—ai zasu fahimci Iyabo. Gaga_gaga cikin dare kowa yayi bacci, ammanni ina zaune na zuba ma yarana dake bacci saman cinyoyina idanu ina kukan da bansan dalilin yinshi ba. Sai in dinga jin kamar ana kiran sunana. Wannan dare shine dare mafi muni a rayuwata. SauÆ™in dana samu asussuba muna idar da Sallah akace mu shiga mota. Ni dai matan da muka kwana rumfa É—aya nabi muka shiga wata Æ™atuwar mota muka zazzauna mazanmu da matanmu dukka. KuÉ—in mota akace mun biya nera dubu biyar. Na Æ™irga na bayar. Matar dake kusa da kujerata na tambaya. Dan Allah baiwar Allah motar inace wannan wanne garin zata je?" "Lagos zata je ke É—in bakisan motar ina kika shiga ba har kika biya kuÉ—i?" A_a ba haka bane" Iyakar abinda nace kenan. Idanuna na lumshe na dinga hawaye. Motarmu ta fice a tasharnan duku_duku muka kama hanya, tafiya muke yi, muna wuce Æ™auyuka, da garuruwa. Mune har azahar muna tafiya sai lokacin na ji zuchiyata tana É—an rage nauyi da sanyi haka. Da muka shiga wani gidan mai inda zamu yi sallah muci abincine ma sai naji inajin yinwa musamman da naga balangu, da zire, da abinci anata siye. Sallar na soma yi, sai na sai tuwon sakwara da miyar egusi, da ruwa na koma mota. Kari É—aya naci tuwon É—ayan kar n na ba Æ´an biyu suka ci suka sha ruwa. Nabkin É—in jikinsu ya jiÆ™e sharkab. Sake fita nayi na sayi ruwa na cire musu nabkin É—in na wanke musu kashi, na Æ™ulle tsummokaran a leda a wajen na barshi. Ina shiga motar direba ya tashi mota dama ni ake jira. ÆŠankwalin kayana na zare na keta shi biyu dashi nayi musu sabon Æ™unzugu. Gaga_gaga mukaita tafiya kiki_kiki mune la'asar magriba, isha. Ni dai ina zaune ina kallon titi wani irin sanyin ni'ima da kwanciyar hankali na saukarmun wanda bai da tamka. Yarana na kalla suna cinyata suna wasansu. Murmushi nayi na shafi kansu, bana iya tuno kowa da komai, yarannan dake cinyata su kaÉ—ai na sani abun mamaki ko? Wallahi babu mamaki a duniyarnan babu abinda ba'ayi sai in bai zo kan ka ba ko kan wani naka ba shine zaka yi mamaki, ko kan ka yaÆ™i É—auka ma. Misalin Æ™arfe taran dare motarmu ta shiga gareji mun iso cikin yardar Ubangiji. Duk muka sakko Æ™afafuwanmu a kumbure. Ni