← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 237

Sashe 93

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ga wani irin ƙunci daya aureni ko da yaushe saina zubar da hawaye. Zuchiyata ɗaci take yi mun ainun. Nayi iya yina dan ganin nabar wannan gidan aikin. Wallahi abun yaci tura, sunƙi saurarata fu, sai suturu da ɗan kuɗi suke bani. Dan a zahiri basu da matsala barsu dai da fi'ili irinna tsofaffi. Haka na share wata huɗu, a lokacin harna fidda ran barin gidan, na kuma san Uwani ta riga da ta tafi Najeriya ta huta abunta. Sai fa in keɓe kaina inta aikin kuka. Ana haka tsohuwar da nake ma aiki tazo ta sameni a kitchen tace in haɗa kayana zata kaini wani gidan in zauna zasu tafi yawon buɗe idanu ƙasashen turawa wata biyu zasu yi. Na dubeta na ɗan cakuɗa mata larabcin ina nunar mata ta mayar dani can inda ta ɗakkoni ni Najeriya zani. Ai nan ta shiga faɗa tana zagina. Shine take faɗamun Hajiya ce tace karta barni in sake komawa gidan, ta siyar dani sun biyata kuɗina dan haka na zama baiwarsu wacce suke da iko da'ita. Kunji wata ƴar duma_dumar fitina. Wasu zafafan hawayene suka gangaro a kumatuna take na soma ambaton Allah. Na kwashe kayana tsab na bi bayansu. Ina bayan mota a zaune ina ambaton Allah. Gabana yanata tsananta faɗuwa dai haka. To da safe ne lokacin, amman bamu muka isa ɗan ƙauyannan ba sai wajajen sha ɗayan dare. Wani ƙauyene me kyau muk iso, gasu da awaki masu ƙoshi da buzu buzun gashi. Wani gidan laka muka shiga, ta cikin gidan me kyau an ƙawatashi da abubbuwan gargajiya masu ƙawa. Babban falon gidan wata iriyar kujerar larabawace wacce babu katako, kamar fulo take irin manyannan da bango ake jinginata. Da wasu riɗa_riɗan Mata naci karo suna zazzaune. Sai naga wata baƙar yarinya a cinyar wata balarabiya. Yarinyar zata kai shekaru sha takwas haka, da na ɗauka ƴar Najeriya ce, ashe irin baƙaƙen kenya ne. Gata da buɗaɗɗen idanu. Abinda ya tsoratani yarinya babu kaya a jikinta daga ita sai ɗan diras da rigar nono, shigowarmu ne balarabiyar ta cire hannunta daga rigar maman yarinyar. Sai naji duk na ruɗe hankalina ya tashi ainun. Nan duk suka miƙe suna ma iyayen gidana sannu da zuwa. Ɗaya daga cikin matan ta nuna mun wajen zama, na ɗan dofana jikina. Madara aka kawo mana da romon nama babu magi sai warin tafarkuwa kawai. In da sabo na saba da wannan cima. Ni dai dan tsoro nace na ƙoshi. Iyayen gidana suka ɗan taɓa dai haka, kana suka fice abinsu.Ɗaya daga cikin larabawan sai ta mun maganar kurame tana mun nuni da in ɗakko kayana muje ta kaini ɗaki. Na bi bayanta zungui_zungui har zuwa wani ɗaki madaiaici da gado, harda durowar ajjiye kaya me kyau. Da larabci tace dani. "Wannan shine ɗakin ki da safe zan zaga dake kiga aiyukan da zaki dinga yi. Zamu biyaki sosai. Kuma zamu siyo miki kayan sawa bama son ƙazanta muna yawan yin baƙi sannan bama son hijabi, iyakarki dashi Sallah, irin wannan kayan zaki dinga sawa." Ta nuna mun zatinta. Gajeren wandone mai kwalliyar tsagu hagu da dama, sai ficiciyar rigarshi ko hannu babu duka mamanta a waje fa suke. A daren ranar na shiga damuwa mai tarin yawa. Bayan na rama sallolina ina zaune ina roƙon Allah sai ga wannan baiwar Allah ta shigo. "Ga kaya ki saka, saiki sameni a falo, zan Kai ki kitchen ki dafa ma baƙinmu Shayi" Kai na gyaɗa mata kaina kawai. A lokacin ɗaya na dare zata yi. Ban ɗaki na shiga nayi wanka na fito. Ina buɗe kayan sai naga wata yaloluwar riga gajera mai hannun shimi sai hular gashi. Na juya rigarnan yafi sau a ƙirga, da ƙyar na saka yadda ta fitomun da zatina sai naji kunya du ta kamani rigar ta matseni ainun iyakarta kuma guiwa. Ina tsaye wannan balarabiya ta shigo. Nayi sauri na kifa wannan hular gashi a kaina. Takowa tayi kusa dani tana ƙamshi cikin harshen larabci tace. "Kinyi kyau ƴar aiki. Dole a haka zaki dinga aiki a gidannan. Wuce muje in nuna miki kitchen" sim_ sim_ sim nabi bayanta har zuwa kitchen. Kayan shayin da kofuna duk dai ta nuna mun duk yadda zanyi. Na ɗaura shayin sai na soma wanke_wanke dan naga uban wanke_wanken dake kitchen ɗin sai naji gara in yishi in rage aikina na gobe. Shayi ya dahu na zuba a wata ƙatuwar buta mai kofuna guda sha biyu harda tiranta. Na ɗauka ina tafe ina harɗewa gabana sai faɗuwa yake yi. Tun kafin in ƙarasa falon nakejin waƙar larabawa na tashi, ga ihun mata inaji. Na jima a tsaye ina tunanin taya zan ratsa cikin mutane a haka. Ina hawaye na shiga. Kutsa kan da zanyi naga mata cike da falon. Wasu suna tsaye sunata rawa, kuma fa daga su sai rigar mama da ɗan diras masu wasu wawalniya sai rawar ƙugu suke yi. Wasu kuma suna zaune a kujeru suna ta shafar jikin junansu. Wani tashin hankali da na gani anayi, wallahi ba shiri na dire tiran shayin na zura a guje sai ɗakina. Na fige hular gashinnan na durƙusa ina kukan tashin hankali. A fusace naji an buɗe ƙofar ɗakin, wannan dai wacce ta bani kayane. Cikin zafin nama ta zabgamun mari ashe wai na fasa kofi ajjiye tirannan da nayi da ƙarfi. Ta dinga zagina tana mun barazana masu nauyiin faɗe. Haka ta figeni bata sakeni ba sai a tsaƙiyar falonnan. Jikina na rawa na dinga binsu da shayi, wasu su ɗauka, wasu su ɗaga mun hannu. Kunji wata ƙaddara kuma. Dana dinga aikin dafa shayi sai wajajen ukun dare suka barni naje na kwanta. Idona ƙyam kamar an soya gyaɗa. Abubbuwan da naga mata nayi a tsakankanin junansu ne ya tsaya mun daram a raina. Kenan nan gidan ƴan maɗigone, ko gidan karuwaine aka kawoni? Ni dai cikina ya ɗuri ruwa, akan sallaya na kwana ina roƙon Allah ya kareni. Da asuba inayin Sallah na tsiri aikin gidan ko ina kaca_kaca. Sai kwashe rigunan Mama da ɗan diras nake. Na samu leda na tattare na gyara ko'ina na tsabtace komai, wajajen sha ɗayan rana na dafa tea na haɗa da biredi na karya. Har wannan lokacin babu wanda ya fito ni kaɗai naketa ɓuruntuna, sai wata ƙatuwar mage da take ta guje gujemta ita kaɗai. Bayin Allah'annan basu suka fito ba sai wajajen ƙarfe biyu da rabi na rana. Mutum biyu suka zauna, sauran huɗun suna tsaye sunyi shigar banzar data wuce ƙa'ida sai suka ɗaura abaya a saman kayan. "Zamu fita, kafin mu dawo kiyi abinci, kuma ki gyara mana ɗaki, wanki ma duk yananan mun tara" Cewar ɗaya daga cikin matan da naji ana kiranta Basma. Da harshen larabci take maganar. Tana dasa aya suka fice. Biyun dake zaune a kujera suna kallon wani shiri na batsa suka ce in haɗo musu Karin kumallo. Da sauri na fita, matane a cikin akwatin talabijin ɗin sirara suna rawa. Ni dai ina hawaye na dafo musu shayi na turara musu gurasa na kai musu. Ɗakunan kwanansu na wuce, nan na shiga aiki ka'in da na'in dan Komai a zaune yake daram, ni na kintsa komai. Na buɗe sib duk na hallage musu dogayen rugunansu. Ina wannan aikin fa na kunna injin wanki ina wankewa ina busarwa. Sai la'asar na kammala. Ba zama na soma guga, ga girki ina tashi ina dubawa, kafin magriba dai na gama komai, da nayi Sallah sai na ɗan kwanta. Gabɓaina babu inda baya nishin ciwo. Ƙofar ɗakin aka turo da ƙarfi. Idanuna na sauke ganin irin kallon maitar da take yi mun tamkar mage taga ɗanyen kifi. A hankali take takowa duk takunta sai inji gabana ya sake tsananta bugawa. " Anti jamilatun wallah, A ti hibbina ni? ( Kina da kyau wallahi kina sona?) Kalmar sai naji tayi mun wani gingingin a kaina, tunda nake ban taɓa tunanin mace zata iya irin wannan muryar mai kashe jiki ga ƴar uwarta mace ba. Ɗan manuniyarta ta ɗora a wuyana tana mun tafiyar tsutsa izuwa wushiryar data raba mamana. "Ma qulti shai'an Jamilatun? ( Baki ce komai ba) "A ti hibbina ni? ( Kina sona) Ta sake maimaitamun. Ni dai na kasa furta dai_dai da kalma, jikina ya mutu tuɓis rokon Allah da nadamar baro ƙasata ta gado ya sake ɗarsuwa a zuchiyata, tsanar wannan mata sai ninka kanshi da kanshi yake yi. " Khus mala bi si ki ( Karɓi kayanki) Ta miƙo mun babbar ledar dake hannunta. Nasa hannu cikin ƙosawa na amsa. Shukran jazilan ( Nagode sosai) Iyakar abinda na faɗa kenan, harta kai bakin ƙofa tace. "Ismi Kariya" ( Sunana Kariya) Sai ta fice, na saki wawuyar ajjiyar zuchiya. Na kasa tsaye na kasa zaune, da dai naga babu sarki sai Allah saina fita falo da zummar zuwa kitchen ɗakko abincina. Da wannan riga fa iya guiwa da aka bani fa kar ku mance duk nake wannan zurunkaɗanar. Ina shiga falon naga Kariya da Aliya suna aikata ɓarna. Gyaran Murya nayi musu, ko a jikinsu ina waige harna isa kitchen. Tsabaragen takaici a kitchen ɗin nayi zamana naci abincin wallahi nayi kwanciyata a kan tayil a wajen na kwana bani na farka ba sai asuba. Nan ciwon bayana fa ya tashi kunsan sanyi yanda yake tada ciwukan ƙashi ( khadija maidoki wai sanyi na tada ciwukan ƙashi?) A taƙaice sai Aliya ce ta taimaka mun na iya miƙewa, Sallah sai a zaune nayi ta. Ranar dai banyi aiki ba sai washe gari da na ɗanji dama_dama. Haka rayuwata taci gaba da gudana cikin wannan kazanta da tashin hankali. Babu irin abinda ni Iyabo idanuna basu gane mun ba. Suturar banza ni kaina dole haka nake sanyawa inta hidimar aikina a hakan. Allah ya ga zuchiyata ba"a son raina bane. Tsorona Allah tsorona kar in gudu in faɗa mummunan hali, amman wallahi da zan gudu, kuma ina tunanin Uwani ko tana can tana jirana kota koma najeriya ne, duk ban sani ba. Babu rana mafi muni da tashin hankali data wuce ranar da Kariya ta zo ɗakina cikin dare da burin kasancewa tare dani. Dama ta jima tana tattaɓani haka tana bani kuɗi. Tayi tayi in saki jiikina da'ita amman Allah yana kuɓutar dani daga sharrinta. Sakamakon adda'a dana tsananta yi babu
Chapter 93 · 0% Book details