Sashe 165
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Inaso Malama a tawo mun dasu in zaɓa. Kuma inason jar hoda in akwai" Ta ƙarashe zancan tana Dariya. Nima dariyar nayi mata na miƙe. To Allah ya raya zan tawo miki dashi Uwani tawo muje ko?" Muna fitowa sai ga matar Baɗejo ta shigo barka. "Ah Malama ashe kina nan, yanzu nake cewa in nayi barkar zan shigo miki mu samu muje mu dawo da wuri." Kinganni nazo barka, muma dama daga nan gidanki zamu je, shiga kiyi barkan muna ƙofar gida" Shiga tayi mu kuma mu kaima wannan tsohuwa sallama muka fito. Uwani ina cikin matsala. Matsalata ta dawo" Uwani tace. "Hamma ya faɗa miki dama zata dawo ne?" Kai na girgiza mata halamar a.a ta kwashe da dariya tace. "Maza mutananmu ɗan munafurcinnan ba'a rabasu dashi. Ni damuwata ɗaya wannan halin da kike ciki ke kaɗai zaki dinga kwana kenan? Bari inje in ajjiye wannan kayan wankin in fito tukunna." Ni dai har Uwani taje ta dawo ina tsaye kamar gunki ina tunanin yadda za'ayi in kwana ni kaɗai a wannan ɗakin. Bazanma taɓa iyawa bane wallahi sai dai Hamma yasan yadda zai yi dani ko mu haɗu mu kwana tare a ɗaki ɗaya ba. "Iyabo harna dawo baki ma san na dawo ba. Almurar da danginta sunata shigar mata da kaya. Harda sababbin kujeru na gani a tsakar gidan irin marasa hannunnan. Sai wani bina suke da ido, inajin shegiyar tana musu yare nasan dai gulma ce." Fitowar matar Baɗejo ne ya hanani tankawa muka rankaya inda zamu hau abun hawa. "Ashe Hama har ta dawo? Jiya inajin Baɗejo suna zancan dawowar tata da daddare da Hamma ya shigo. Akan maganar motar da zata je ɗebo kayanta" Namiji tuwon ƙaya miyar allura, duk yadda kake da namiji in yaso yin munafurcinshi sai yayi, shi da yace magani yaje ya sha a wajan Baɗejo ashe ƙaryace. Murmushi nayi nace. E haka yake sanar dani batun dawowar tata nima." Babu daɗi babu ragi naja bakina nayi shiru. Ina kan acaɓa ina mamakin maza har muka isa wannan ƙauye. Yau bamu tarar da layi sosai ba, malamin ya bani rubutu a gora, ya bani tofi shima a gora sai hayaƙin habbatussauda da yace dana ga dare yayi in banke ɗakina dashi, bayan na gama komai sai in yi alwala in sha wannan rubutu, shi kuma tofin in tsiyaya in shafe jikina dashi in sha Allah matsalata ta kau. Godiya nayi mishi sosai muka sake kamo hanya kafin mu iso magriba har ta kawo kai. Ina saka ƙafata a ƙofar gidan ɗago ɗayar da zanyi in ajjiye a inda zan ajjiyen sai naga wani farin ƙyalle. Allah ya taimakeni ban taka ba sai nayi tsalle na shiga gidan. Uwani ta kewaye ƙyallen ta wuce. Allah al hakim wai wannan bala'in duk akan ɗa namiji akeyinshi wai shin me na tare ma Hama ne da take haɗa mun masifa da bala'i haka?" Uwani ce tai bismillah ta ɗauki ƙyallen muka shige. Ina jiyo surutun mata a kitchen anata shewa. Baɗɗo kuma fitowarta daga bukkarta kenan. "Adda sannunku da dawowa. Ai kuwa yanzu wannan matar mai sarin kaya tazo nace mata bakya nan. Amman tace gobe da wuri ma zata zo dan nace mata kin kawo kaya." Wallahi in yi magana na kasa sakamakon haɗa idanu da nayi da Hama. Taci uwar kwalliya ta sha sabuwar atamparta dal. Tayi wani irin kyau har baƙin ƙunshi tasha hannu da ƙafa, ga kitso an yarfa mata zai iya fin guda ɗari ya zuba kawai a kafaɗarta. Wani kishine ya tsargamun da ganin kyan da Hama tayi. Wanda yake da Hama banga abinda zaiyi da Iyabo ba, ba dai kyau na fuska dana fata ba sai dai diri da tsoka kawai za'abi. Ta gabana tazo ta wuce tana kwarkwasa da sabon filas dinta a hannunta. Hama ashe har kin dawo tun ɗazu, da Yaya Hamma ya faɗamun nayi tunanin sai da yamma zaki dawo shi yasa ma ban ajjiye miki abinci ba, sannu da dawowa " Da sauri ta juyo ta kalleni, nifa da ƙyar na danne kishina harna saurareta sai cemun tayi. "Kinsan da dawowar kenan ya faɗa miki ke?" Ai sai naji wani farin ciki dana lura kura zan kunto mishi. Kwarai na sani sosai ma. Ai dani akaita komai har zuwa wajenki da yake yi nice nace ya dinga zuwa, ya kuma dinga miki kyauta" Ina faɗar haka na yi shigewata ɗakin Baɗɗo na ajjiye kayan magungunana, nayo alwala muka yi sallar la'asar, muna kan sallah akayi kiran magriba. Na idar ina zaune a dadduma na yi tagumi Uwani fa sai magana take mun naƙi kulata. "Adda akwai ruwan wanka a madafi a murhu ko zaki kwatsa ruwa?" Zan watsa Baddo. Uwani wani tunanin na lula ina jinki ke dai bara in fito" A gurguje nayo wankan haɗe da alwala. Hama fa sai giggiwa take yi kamar sabuwar bera. Murmushi nayi a raina nace. Yau zaki sha mamakina wallahi Allah saina saki zubar da hawaye zan nuna miki bariki yau." Ɗakin Baɗɗo na shiga nayi sallata a nitse duk ƙuncin da nake ciki ya yaye, na jawo bokitin wannan tofi na soma amfani dashi sannan na shafa na wannan malamin. Uwani tawo muje ɗakina maci tuwon acan. Baɗɗo kiyi haƙuri in Yusufu yazo ki loda mishi wasu kayan ya kai gidan Dada na cika muku ɗaki da shirgi" Hannun uwani naja muka fito, Hama na kofar ɗaki ta kafa ta tsare za'a amshi miji muka zo muka wuce da gaushina cike da kasko, da bismillah na shiga na lalubi tocilata a saman kujera na kunna haske ya game ko'ina uwani ta samu ƙasa ta bararraje da tuwonta. Zauna kici tuwon yau za'aga jarfa a gidannan uwani ke dai zaki sha labari. Hayaƙi na zuba a gaushi na tafi sib ina nemo kaya ina addu'a tsigar jikina sai tashi suke kaina na buɗewa. Doguwar rigar gumama na saka mai baiyana shape gata da sulɓi ta sama ta kamani tayi caras a jikin nawa, ta ƙasa ya buɗe ta baya daidai mazaunaina rigar tayi ɗare_ɗare saman mazaunaina. Na fesa turaruka kala_kala harda wanda ma ban taɓa fesawaba na ɓaresu a kwali. Baɗɗo ce tayi sallama ta shigo da nono a hannunta ta dure a gaban Uwani. "Adda ɗalibai sun gama cika fa ke muke jira yau naga harda sababbin fuska ma". To Baɗɗo Yaya Hamma nake jira har yanzu naji shiru na jiyo ɗuriyar su Nasiru amman shi har yanzu shiru" Ɗan murmusawa tayi tace. "Ya dawo tun ɗazu fa Adda. Ya jima a cikin gidanma ai" Murmushi nayi mata na fice na barta nan. Karatun kanshi baifi na minti talatin akayiba hankalina na ɗakin su Hama da nake ta jiyo dariyarsu. Magunguna da kayan kwalliya dana fito musu dashi warwaso suka yi ma komai. Magani kam ya ƙare tas in banda wanda na cire ma kaina, da wanda na cire ma Baɗɗo, da me jego. Kayan kwalliyarne su kai ragowa nai musu bayanin da bai wuce minti ashirin ba na sallamesu. Ina zaune a turmi ni da uwani da Baɗɗo muna hirarmu, yaya Hamma ya fito suka gaggaisa da su Uwani yace "Jabu ina ɗaki ina jiranki" Ya nufi ɗakina nabi bayanshi da uwar muguwar harara, na miƙe. Sai da safenku Uwani ma ƙarashe gobe" Na shiga na sameshi a tsaye yama kasa zama ina kallonshi ai saina danna ihu na rungumeshi ƙam na rufe idanduna ruf, basai na hau ɓarɓarɓar da jikina ba halamar matsanancin tsoro ba. Gogan naku duk yabi ya rikice sai tambayata yake yi, wallahi naƙi bashi amsa saima wasu surutai da sokiburutsun zance dana shiga yi mishi kamar zautacciya. Zan mutu Shikenan zan mutu in barka, ga danƙa a cikina ashe babu rabon zaka ɗauki ɗanka wanda nice uwarshi ka yafe mun" Naita ɓarin zantuka ras fa nake nayi rantsuwar bai isa ya kwana a ɗakin Hama bane yau inaso in nuna mata shegen birni gaba yake da shegen ƙauye kuma shima duk bala'in kwaɗayinshi saidai ya haƙura. Da ƙyar Yaya Hamma ya iya jana zuwa bakin gado muka faɗa gadon tare na wani sandare kamar na mutu. Ai a guje ya danna a guje ya fita. Idona na buɗe nace. Kaɗan ai ka gani ma ba kai munafuki ba. Bai jima ba sai gashi ya dawo tare da Yafendo, da Hama, Baɗɗo da Uwani. Ruwa ya yayyafa mun nayi ajjiyar zuchiya mai ƙarfi, naƙi buɗe idanuna ma balle mu haɗa idanu sai kuka. "Allah ya bata lafiya. Yanzu abinda za'ayi kai ka kwana tare da'ita kaita mata adda'a inaga wannan abun harda junnu. Gobe sassafe zanje in karɓo mata magani. Ku mu jenku. Jabu Allah ya tashi kafaɗa. Allah yasa ba sabida juna biyun dake jikinta bane aljanu ke son shafarta ba" yaya Hamma inaji yana tambayar Yafendo dama juna biyu gareni shi bai sani ba? To kunsan kunya irinta fulani sai ma ta fice a madadin ta kulashi sai Uwani ce ta bashi amsa. "Juna biyu gareta ai Hamma. Dan Allah ka kula da'ita gashi gobe ni zan koma da sai in zauna da'ita. Duk da dai tafi bukatarka fiye damu. Baɗɗo muje ko" Suka fice, duk ina ganin komai na ƙanƙance idona duk ina kallonsu. Hama da Hamma ne suka rage a tsaye ta cika ta batse fam kallonshi tayi tace. "Kana nufin a nan zaka kwana kenan alhalin kasan kwananane yau. Sannan kasan yaufa na dawo duk yadda kake cewa kayi kewata haka zakayi mun?" Ta ƙarashe maganar tana huci. Kallonta yayi ranshi a ɓace yace. "Amman ba zaki tausayama halin da Jabu take ciki ba? Firgita fa take yi kina gani a gabanki fa na yafa mata ruwa ta farfaɗo zan tafi in barta a wannan halinne ga juna biyu a jikinta? Kuma a gabanki Dada tace ke kiyi haƙuri lalurace kema inya kamaki na tabbatar Jabu zata iya bar miki kwananta. Me yasa kike haka?" Tsaki ta doka tace. "Munafurcin banza da wofi, akanta aka soma juna biyu ne Hamma, ko ba haihuwata uku da kaiba. Nii ban taɓa gani ko a cikina na fari kayo haka ba. Shikenan tunda abun rashin adalcine" Ta fice fuu. Ni dai inata nunfarfashi, ban buɗe idanuna ba saida naji Yaya Hamma ya tattagoni ya rungumeni yana shafar kaina yana mun karatu a kunnena" Lumshe idanuna