← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 237

Sashe 188

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ba tunda ba zaman kanta take yi ba. Zan bar yaran a wajenta in tasa mun lokaci sai inje mu je " Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke. "Allah ya nuna mana. Ina fatan ku sameta cikin aminci in sha Allah. Sannunku Allah ya bar zumunci a huta gajiya" Da haka suka yi sallama ya ajjiye wayarshi sai ga Hadiza firit ta fito tayi tsaye a kanshi tana jijjiga. "Burinka ka kaso auren tsohuwar matarka dai kai ka sake aure abinka. Ta dai tabbata Iyabo dai asiri tayi maka. Bata ƙarƙashin inuwar aurenka ma adda'ar aminci kake yi mata. Allah zai saka mana mugu azzalumin banza" A fusace Gwadabe yayo kanta gadan_gadan dan idanunshi sun rufe hannu yasa ya tureta ta faɗi. Da dukanta ma yaso yayi tausayinta yake ji ga tiyata a jikinta, ga rashi babba da akayi mata. "Wayyo Allah ka kasheni a kan tsohuwar makirar tsohuwar matarka." Da sauri Gwadabe ya juyo me zai gani Hadiza face_face a cikin jini tana riƙe da wajen da akai mata tiyata. Ranga_ranga suka nufi asibiti a motar Yaya Tasi'u. Tun daga gida Yaya Tasi'u yake faɗa har suka isa asibiti. Kuma Hadiza yake ma faɗa duk da a sume ma take. Gwadabe kuwa ya shiga tashin hankali mai zurfi. Hadiza ta riga data kaishi maƙura shi gani yake yi zai sauwaƙe mata kawai ya huta gudun kar watarana tasa ya aikata aikin dana sani. Yanzu jibi baƙin kishinta abinda ya ja. Suna isa asibiti aka karɓeta Dr sai faɗa take yi akan ya za'ayi irin wannan saken ɗinkin da akayi mata ya warware." Ɗakin sabuwar tiyata aka shige da'ita ga jini data zubar sosai. Wajen Malam duk suka ɗunguma suka je. Yana kwance kamar mamaci ko motsi bayayi. Duk mai tausayi inya kalli ɗakin da malam ke ciki sai ya zubar mishi da hawaye. Sun fi minti talatin a wajen kafin Yaya Tasi'u ya shiga wajen Dr ɗin Malam su kuma su Gwadabe suka koma ƙofar ɗakin tiyata. "Yanzu duk faɗan da akaima Hadiza bata ji ba sai da ta sake takalarka da wani jidalin? Wannan yarinya dai bata ji. Amman fa Gwadabe sai ka zama tsayayye sosai a gidanka kar ka kuskura kayi saken da kan yaranka zasu rabe. Wallahi matsawar haka ta faru Shikenan ni dai na faɗa maka. Kaduba gidanmu sai yanzu ne yake shirin farfaɗowa a haɗe kai. Tun su Yaya Tasi'u suna ƙananu ake abu ɗaya yau shekarata ni kaina nawa? Mata basa taɓa tsufa da kishi shine matsalar balle kace zasu watsar dan kansu. Barinma irinsu Hadiza masu zafin kishi. Itafa tun tana yarinya haka take da wannan baƙin kishin. Duk abinda aka siyo mana sai Hadiza tayi kuka in dai ba da ita za'a siyo ba. A makaranta akwai yarinyar da hadiza ta tsana kasan dalilin?" Auwala ya tambaya. Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace. "Sai ka faɗa" "Sabida yarinyar a ko da yaushe ita ke zuwa na farko a ajinsu. Daga ƙarshe sai da Hadiza ta ƙwace wannan ragamar ta hanyar nacin karatu da dena bacci sannan aka zauna lafiya. Kai itafa tafi kab ƙawayenta kyau bata ƙawance da wacce tasan ta fita dan masifa. Kai Gwadabe yake ta karkaɗawa yana sauraren Auwala tare da tunanin yadda zai shawo kan lamarin Hadiza. Lallai akwai gagarumin aiki a gabanshi to zaima iya gyara Hadiza kuwa, ko dai rabuwa da'ita shine a'ala a gareshi? Idanu ya lumshe kanshi na yi mishi zafi. A haka Yaya Tasi'u ya dawo ya tarar dasu jikinshi a mugun sanyaye da irin yanayin da yaga jikin malam ɗin. Shi kam ma har ya fitar da rai da tashin Malam. Almajiran malam kullum a cikin yi mishi sauka suke suma suna cikin wani hali. Likitane ya fito daga ɗakin da aka shiga da Hadiza a lokacin wajen biyun dare. Yaya Tasi'u da Gwadabe ne suka bi bayanshi har zuwa ofishinshu, ya basu waje suka zazzauna. "To mun samu nasarar sake yi mata ɗinki sabo. Tana buƙatar ƙarin jini dan ta zubar da jini sosai. Dan Allah a rinƙa kiyayewa koma menene dai ya faru a lura da'ita sosai tana buƙatar kulawa" "Doctor mun gode sosai. Zamu iya zuwa du mu biyun a gwada jinin namu in yayi to, akwai ƙaninmu a waje ma in namu bai kai adalilin abinda ake buƙata ba." A gurguje dai Hadiza kwananta biyu kafin ta samu ta farka hannunta ɗaure da ledar jini. Yaya Zara tana gefenta a zaune, sai Amaryar Malam. "Yaya Zara ina ƴata?" Da abinda ta soma kenan. Da sauri Amaryar Malam tace. "Zara maza kirawo likita. Sannu kinji Hadiza kai Allah mun gode maka" Yaya Zara ce ta miƙe ta je ta kirawo Dr suka tawo tare. Ya duba jikin Hadiza tare da yi mata tambayoyi" "Ku kula kar a bata abinci, sai tea ko kunu zuwa kwana biyu a kula. Sannu Allah ya ƙara lafiya' Idanu Hadiza ta lumshe hawaye suka zubo mata tana mai cike da nadamar yadda da auren Gwadabe. Data sani tun wuri ta fita sabgarshi yaje ya auri Shafa ita kuma ta auri wani mijin da yafi mata. Da Yaya Zara, da Amaryar Malam, da Hadizan ko wanne cikinsu da damuwar dake damunsu. Ɗakin ya ɗauki shiru na lokaci mai tsayi sosai kafin isowar Isuhu da matarshi da yara. "Isuhu kune a tafe?" Baiwar Allah ga waje zo ki zauna" Zama matar Isuhu tayi da ɗan goyonta a bayanta. "Sannu Hadiza ya jikin, ya kuma ƙarin haƙurinmu na Baba, ya jikin Malam? Ai daga can wajen malam ɗin muke kafin Auwala yai mana kwatancen nan ɗakin shi da maigidanki" A daƙile da wulaƙanci Hadiza tace. "Jiki da sauƙi. Haƙuri mun gode Allah " Yaran nata ta kalla daga kwance sun wani canja sun yi kyau sosai. Isuhu ne yace. "Amadu kuje ku gaishe da Mamanku. Hadiza sannu da jiki. Yaranne suka isa bakin gadon Hadiza ta riƙe hannun mai sunanta gam tana kallonta fes da'ita cikin kaya masu tsada. Gaisheta da jiki suka yi, tare da ta'aziyya. Su gwadawa ne suka shigo ɗakin. "Gwadabe kun dawo? Sannunku. Zara muje daga waje mu basu waje ko? Amadu Hadiza ƙarama kuzo muje" Amaryar Malam ta riƙe hannun yaran suka fice. Ɗakin ya rage daga Isuhu da matarshi. Sai Gwadabe da Auwala da Hadiza da take kwance. "Kiyi haƙuri ban kawo yara sunyi ta'aziyya ba. Bama nanne munje umara. Shi yasa, jiya muka shigo Maraɗi muka tadda labari shine muka tawo. Ga yaran su miki kwana biyu Furare zata zo ta ɗaukesu. Zan sa a kawo musu kayansu. Auwala yayi dariya yace. "Kako kyauta Isuhu sosai muna godiya da wannan zumuncin, baka duba halin gyatukarsu ba dan da an daka ta tata da zumuncin lalacewa zaiyi" Isuhu ya sosa kai yace. "Irin riƙon da Malam yayi mini shi kaɗai ka iya riƙe igiyar wannan zumunci ko da ban taɓa shiga rayuwar Hadiza ba. Mu kam zamu wuce Furare muje" Hadiza zamewa tayi tamkar mutum mutumi dan mamakin kuɗi da Isuhu yayi harda zuwa Umara. Yanzu yaranta sun taka ƙasa mai tsarki kenan, tare da ƙazamar Furaren data raina? Daman hausawa sukance ɗan hakin daka raina shike zamema gagara gasa. Auwala ne ya takama su Isuhu Gwadabe ya ƙaraso wajen gadon yace. "Yaya jikin naki Hadiza?" Banza tayi mishi ta tafi duniyar tunani dan batasan ma Gwadabe na tsaye a kanta ba. Shiru yayi kawai yana karantar yanayinta. Can Hadiza tace. "Tabb wai Isuhu ne ya je Umara shi da Furare, kuɗi yayi kenan?" Wannan zancan zuchiyane ya fito fili. Ringing ɗin wayar Gwadabe ne yasa ta juyo da sauri ta ganshi tsaye bisa kanta. "Bara'u kaddai har kun isa garin su Iyabo tsuntsun soyayya?" Da sauri Hadiza ta dubi Gwadabe shima ita yake kallo. "Gwadabe kai kaga irin ƙauyen da tsuntsun soyayya ya kai Iyabo kuwa. Haƙiƙa wannan tsuntsu bai mata adalci ba. Iyabo ta ƙare ta komaɗe ta zama bagidajiya sak. Yanzu haka ma tana asibiti ta haifi yaranta biyu du maza" Turus Gwadabe yayi yana sauraren Bara'u dake mishi bayani. Idanu ya lumshe a gaskiya baiji daɗin jin labarin Iyabo a haka ba. "Kana ji yarannan in aka barsu a wannan ƙauyen akwai matsala fa" "A'a Bara'u kar kace haka ka barsu kawai" Yana faɗar haka ya juya ya fice ya samu gefe guda suka gama tattsunawa da Bara'u. Daga nan ya fice a asibitin ma ya koma gida. Shafa na zaune tana hutawa Gwadabe ya shigo da sallama fuskarnan tashi cike da damuwa. Kwanciya yayi kawai yana kallon sillin damuwa da tunani sun caza mishi kai. Da sallama Shafa ta shigo hannunta riƙe da ruwan sha a kofin silba. "Jikin Yayanne kuma? Yanzu na gama girki kenan nake son zamu je ni da matar Mammada da matar Sabitu" Kuyi haƙuri gobe ba posting sabida akwai aiyukan turaren amare da aka bani kwangilar yi har show glass biyu manya, to kunga aikin da yawa. Masu son turare su tuntuɓeni ranar asabar zan turo kaya arewa nagode
Chapter 188 · 0% Book details