← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 237

Sashe 114

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me yasa wacce take da miji ba zata zauna ita kaɗai da mijinta ta samu nutsuwa su ciyar da juna abinci a baki cikin shagwaɓa da soyayya ba? Ɗan guntun tsaki ta yi kana ta fito rannan nata a mugun ɓace. Ɗakin ya cika dam da hayaƙin turaren wuta ko ina yanata bulbula ƙamshi masha Allah. A gefe guda ta zauna tana fuskantarsu tare da ƙarema tiran abincin Shafa kallo. Itama Shafar ita take kallo tun futowar tata. Sanye take cikin riga da zane na atampa ɗinkin wasila. "Yaya ina kwana, an tashi lafiya?" Kallon Shafa tayi sai ta saki fara'a a zahiri, a baɗini kuma ji tayi kibiyar kishin Shafa ta soki murfin ruhinta. Gani tayi a idanunta shafa tayi kyau kaalar atampar ta amshi fatarta, sai kishi ya bijiro mata. Ta bangaren Shafa ma fitowar Hadiza saida ya faɗar mata da gaba, take ta raina kwalliyar data kashe minti talatin tanayi. Kuma ƙamshi Hadiza ya goge tarihin turaren akwati data fesa ta fesama Gwadabe ma. (Ire_iren wannan ke hana zaman lafiya a tsakankanin kishiyoyi. Shi yasa akeso mace ta yarda iya wuya tafi kishiyarta. In tasa hakan a ranta ta huta da kaso hamsin. Muddin duk abinda zai faru kina hango cewar an fiki, to akwai matsala. Anya gidan Gwadabe zai zauna lafiya kamar yadda yake tunani kuwa. Mu dai je zuwa mahaukaci ya hau kura) "Lafiya lau Amarya. Mai gida takobin yaƙi ina fatan kabi da'ita a hankali kaga yarinyace kuma kai ɗin baka da dama" Ta ƙarashe zancan da wata mayaudariyar dariya mai sukurkuta kan mai gida. Sai murmushi yayi dan shingin kaɗanma ya ƙware da tean da Shafa ta zuba mishi yana kurɓa. Dariya kawai yayi, ita kuma Shafa kunya ta mamaye illahirin jikinta. Taliyar Hausa ce da miyar stew ta zuba musu ta caɓa miyar akai sai ruwan bunu mai citta. A plate ɗaya ta zuba ta saka cokula uku. Murmushi Hadiza tayi tace. "Ayya ai da baki zuba dani ba. Kinga abincin karyawata na riga dana kammala." Kallonta Gwadabe yayi bayan ya kai lomar taliyar bakinshi. "To ba sai mu haɗu muci duka ba Hadiza. Ita Shafa ai ba zata ji daɗi ba in baki taɓa abincinta ba." Ɗan gajeren murmushi tayi tace. "Shafa zuba mini shayin in sa albarka. Doyar na tashi ina sha'awar ci, dan da zazzaɓi ma na tashi" Kalmar zazzaɓi ne yasa Gwadabe ya sarara baice da Hadiza uffan ba, duk da yasan lafiyarta ƙalau abincinne ba zata ci dasu ba kamar yadda tayi rannan. Doya da farfesun ta raba biyu ta ajjiye musu rabi, ta soma cin nata. Ɗakin yayi tsit baka jin motsin komai saina lokula da tauna. Su ukun duka ko wanne da abinda ke ƙunshe a ranshi. "Hadiza kece babba ina mai ƙara baki haƙuri dan Allah ku daure ku wanzar da farin ciki a wannan xamantakewar. Kunga ni a zaman da nayi da uwar ƴaƴana bamu taɓa samun saɓanin da har za'ace mun kwana muna rikici, ko gaba da sauransu ba. To ina fatan kuma zan sameku kamar Iyabo, koma fiye da ita dan a zahirin gaskiya Iyabo mutum ce guda da ɓari. Ina fatan mu zauna Lafiya " Take kishin Iyabo ya turniƙe Hadiza ta yanda ya kusan rufe mata idanunta tayi ɓaranɓarama. Allah ta ambata a zuchiyarta taja bakinta ta yi shiru. Abincin dake gabanta ma rufewa tayi dan sai taji bakinta na wani irin ɗaci. A cikin zuchiyarta tace. "Niko zanso ganin wannan Iyabo ido da ido inga me ta mallaka wanda yayi tsaye cak a zuchiyar Gwadabe da har mu yake ma ishara da muyi koyi da ita wajen kyautata xamanmu a tsakaninmu dashi " "Bakice komai ba ke Hadiza " Gwadabe ya katse mata zaren tunaninta. "Allah ya bamu ikon haɗe kanmu mu baka nutsuwa" A haka dai suka kammala cin abincin Shafa ta soma kwashewa. "Meye ya ɓata miki ranki haka Hadiza. Wai me yasa kike yin hakane Hadiza ta? Haba gimbiyar mata tauraruwar zuchiyar Gwadabe " Harara ta watso mishi tace. "Iyabo tana numfashi na zama tauraruwar zuchiyarka?" Dariya yayi kafin yace wani abu Shafa ta shigo. Dole shima ya miƙe yai mata sallama ta bisu da idanunta sai ga hawaye sirara sun zuraro mata. Da sauri ta share hawayen nata ta miƙe ta soma gyara wajen da akaci abincin, duk da dai ba datti a wajen. Sallamar Ine Hadiza ta jiyo daga ƙofar ɗakinta. "Ah su Ine manya kune a gidan sassafe?" Zama Ine tayi tace. "Ke dai bari yanzu na shiga cikin gida na tarar da Malam na rikici da Baba Suwaiba, da Amaryar Malam. A taƙaice a kan idanuna duk Malam ya koresu sun fice da akwatunansu. Gaskiya ban taɓa ganin ɓacin ran Malam irin na yau ba." Daɓas Hadiza ta zauna a kujera. "Malam ya koresu fa kika ce, to me suka yi haka?" "Tabb wallahi ban sani ba, kinsan Baba ba faɗamun zata yi ba kona tambaya. Ni ban tambaya ba. Babace tace in koma gida kawai, shine nace baro in shigo mu gaisa zan shiga wajen Anty Badi'a ma" Hadiza tayo jigum kana tace.." "Zanga sanda gidanmu zai daidaita. Kishine ko wacce ya cika mata ranta fal. Amaryar Malam na jima ina ɗauke da cikinta ba dan tana cin albarkacin mahaifina take aureba da tuni ta gane kuranta. Sabida tana da fitina da yawa fiye da sauran iyayen namu." Nan dai suka ɗan taɓa hirarsu Ine tai mata sallama ta tafi. Sai wajajen azahar Sai ga Sailuba tazo kiranta. Wayarta ta ɗaga ta kira Gwadabe ringing biyu ya ɗaga. "Gimbiya lafiya dai ko?" Murmushi tayi tace "Lafiya lau. Dama Anty Badi'a ce tace tana son ganina shine nace bari in sanar maka" Sai da yayi murmushi yace. "Masha Allah kije ba damuwa. Ni bana gidanma muna wajen Malam, an ɗan samu kacaniyane a cikin gidan. Sai dai inna dawo zakiji komai" "To Shikenan saika dawo ɗin." Wayarta ta kashe suka fito ita da Sailuba. Su Yaya Jazuli da su Nazifi suna ɓarayin Yaya jamilu. Suma zancan korar mahaifiyarsu da Malam yayi a gidan suke yi. Karaf a kunnen Hadiza Nazifi yana cewa. "Dole zamu je mu dawo da uwarmu babu inda zata je, tunda ta haifemu muna da gado a gidan" Hadiza ta kalleshi shima ya kalleta yana muzurai. "Dena kallona dan ta abu kazan..." Ya danno wani zagi ya dannawa Hadiza tare da ɗorawa da cewa. "Ku gaku ƴaƴan so, yaran mowa shafaffu da mai. To wallahi wannan abun masifa da bala,i kawai zai haifar dam mahaifiyarmu ba zata koru ba" In kun tanka Hadiza ta tanka. Inda sabo ta saba da jin waɗannan zagi da waɗannan furuci na cewar sune ƴaƴan so a idanun Malam. Haka zalika dukkan abinda ya faru a wannan gida nasu gani akeyi dasa hannu Baba Fhatsima da Yaya Tasi'u da suke ganin kamar suke juya Malam. Hadiza ta shiga tunanin yanzu haka suma in suka ƙi samun zaman lafiya a tsakaninsu yaransu zasu taso a cikin ƙiyayyar jininsu? Wai to wake da Matsala ne mazan dake auro matam su haɗe su. Ko kuma matan da aka aurone masu matsalar? Ita dai tasan matsalarta ɗaya kishine, kuma kishi shine matattakalar data rusa ahalin gidansu da duk gidajen da aka kasa samun daidaito da fahimtar juna kuma ba mace ɗaya bace a cikin gidan. Duk kishi shine sababin dake sa uba ya tsani ƴaƴan cikinshi, uwa taji kamar ta kashe ɗan da kishiyarta ta haifa, kishiya da kishiya su kasa samun zaman lafiya. Gida ya zama gidan rikici da hayaniya kullum. Wannan lallai babbar matsalace da Hadiza take ganin bai kamata ta bari sheɗan yaci galaba a kanta ba. Take zuchiyarta ta sassauto mata dangane da zafin kishin Shafa. Duk da bata da burin yin zaman doya da manja da Shafa. Amman ta ɗaura ɗamarar saita zama tauraruwa sarauniya a birnin zuchiyar Gwadabe ta yanda zata ture har matsayin da Iyabo take dashi. Da wannan tunani ta shiga falon Anty Badi'a. Suna zaune a ƙasan kafet an barbaza kayayyakin mata na ado da kwalliya kyawawan gaske Anty Badi'a sai ɗagawa take yi. Hadda manyan zannuwan gado ƴan kwali irinna saudiyya ɗinnan masu laushin gaske. "Kinga yadda kayannan suka amsheki kuwa Hadiza? Ga wasu samfurin masu wando, da gajeren siket an kakkawa zo zauna." Cewar Anty Badi'a. Zama Hadiza tayi da hanzari suka soma ɗaɗɗaga kayayyaki harda wasu rigunan bacci na garari . "Kinga zaɓi kaya Hadiza. Ba'a bori da sanyin jiki. Kinga waɗannan dana zaɓar mana ni dake, duba kiga kalolin sunyi" Anty Badi'a ta miƙo mata kayayyakin ta soma waresu tana gani, dogayen ruguna, da riga da wandone, sai kuma mai gajeren siket wanda zaka saka daga kai sai mijinka. Kaya dai kusan guda takwas_takwas harda zanin gado na kwali mai ɗawisu irin na da. Hadiza rabin kuɗin kayannan ta biya, Anty Badi'a ta biya mata kuɗin rabin. Ta sake yin mata kwalimar nata ƙananun kaya. Ta bata wasu surruka masu ƙarfi tace ta riƙesu tayi amfani dasu zata ci ribar zaman Aure. "Fatanmu shine mutuwa itace zata rabaki da mijinki. Kinga maza kullum su babban birinsu shine mace ta zama musu tamkar hawainiya wajen caccanja salo_salo na komai nata ta yanda zamanku bazai zama ya gundureku ba. Ki tabbatar a ranar dazai bar ɗakinki kin mishi abinda zaiji yana ɗoki da mararin sake shigowar girkinku. Ki riƙe talaucinshi kuita mishi adda'a Allah zai buɗa mishi Gwadabe yana da zafin nema ba malalaci bane muna mishi fatan nasara. A ido haka Shafa bata da wani matsala kiyi ƙoƙarin janyo ta a jika, karki bari wasu daga cikin gidan su janye miki ita da hakanne gulme_gulme ke ratsowa. Hadiza ai Baba ya kamata ta zame miki allon kwaikwayo. Dan har gobe kinga yadda ruwa yake maganin dauɗa. Anty Badi'a ta jima tana bawa Hadiza surrukan da zasu tallafi zamantakewarsu daga ƙarshe sukai sallama Hadiza ta koma ɓarayinta. Gaga gaga haka rayuwa taci gaba da matsawa, duk safiya da irin shiga da Hadiza take yi na alfarma, ga ƙamshi. Itama fa Shafa bawai a baya aka barta ba itama tana yin nata salon kwalliyar, amman ita tafi ganewa atampa, leshi sai dogayen riguna ƴan kanti. Itama suta riƙe a matsayin makaminta. Ko wacce cikinsu rigegeniyar take yi wajen ganin ta zama ta gaban goshi. Rayuwar gidan babu
Chapter 114 · 0% Book details