← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 237

Sashe 14

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Tabalbalin:.
A guje ta shiga gidan, tana shiga É—akin Iyabo taga matan gidan a É—akin cirko_cirko. Turus tayi da ta gansu, suma kansu sun dibibice da ganin Uwani. A zatonsu babu mai dawowa, sun shigo gulmar ganin gyara. Tsaki Uwani tayi ta shige ciki tare da cewa.
"Aikin banza wallahi duk matar dana fito na sameta uwarta zanci danni ba Iyabo bace."
Karo taci da Laila a cikin uwarÉ—akin gaban sib ta É—auko sabuwar atampa tana hannunta.
"Sata ce ta shigo dake ɗakin kenan? Iko sai Allah wai na kwance ya faɗi. Amman dai su Kulu anyi asara, an yi faɗuwar baƙar tasa, ko kuma ince ƙarkon kifi daga ruwa izuwa wuta, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta." Laila kuwa ba bakin magana ai da kunya an kama uwar miji na sata a ɗakin suruka. Fisge Atampar Uwani tayi. Sum_sum ta fice, Uwani kuma ta rufo ƙofar ta fito ba kowa a falo, tsakar gidanma data fito duk sun yashe. Abundai ba haka akaso ba, wai an yi gulmar uwar miji ta ji. Tana shiga motar suka ja sai asibitin nasarawa."

Asibitin Nasarawa.
Da taimakon Allah, na haifi yarana biyu, mace da namiji da kaina, sai ƙari da akaimun kaɗan. Tubarkalla yaran manya kamar ba ƴan biyu ba. Sai dai fa ina sauka ma'aikatan kiwon lafiya suka soma tambayar dangina kayan da za'a saka ma jarirai, da abubbuwan da ake buƙata. Ko allura bamu da'ita. Burodami kokodeen ne ya ba matarshi Antimi Mulka kuɗin dukkan abinda ake buƙata aka kawo babu ɓata lokaci. Cikin ƙasa da awa guda yarana an kintsasu tsab a cikin seti me ruwan toka, sun yi kyau sosai. Ɗakin hutu aka dawo dani. Da iyaa Debisi na soma haɗa idanu, tayi kicin_kicin da ranta, da gani kasan ta cika ta batse ƙiris take jira. Ko ma dama can haka take, kullum a cikin faɗa da kumfar baki take.
"O ye koju ti e ( Kinji kunya) Ki duba kin haihu a wulaƙance, babu mijinki, babu dangin mijinki, babu kayan jarirai, ba kuɗin asibiti, jibi ramarki. Da ace kinji abinda aketa faɗa miki daba haka ba, da ɗan uwanki kike aure yarenku da kin fi haka daraja, kuma babu mai ƙyamatarki, ballema ya tsangwameki." Duk wannan maganar da yare take yi mun. Tana yi tana buga cinya, tana ɗaga murya tamkar faɗa, bil haƙƙi ita ba faɗa take yi ba maganarta ce haka, ko kuma ince mafi akasarin yarenmu suna da ƙarfin murya, da ihu a cikin magana. Ni dai bani da bakin cewa, dan nasan Gwadabe na ƙoƙari sosai, banso zuwa asibitin ba sabida gujema tashin hankali da tarzoma irin wacce ta afku lokacin haihuwar Toye, an yi ɗauki babu daɗi sosai. Dan ranar suna anci dambe an gode Allah. Burodami kokodeen ne ya katse Iyaa Debisi ta hanyar cewa.
"Yarinyar nan Iyaa Debisi ya kamata a barta haka, ko dan rabon dake tsakani, ni ina ganin dukan yayi mata yawa" Miƙewa tayi tsaye, ta tafa hannu tace.
"Ahhhh Ahhhh kokodeen Oya were ( baka da hankali)" Nan fa ta sake shiga wani babin, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shigo da yaran da ma'aikatan kiwon lafiya suka yi ne yasa ta yi shiru. Ɗakin kuwa Hausawa sai kallonmu suke yi. Iyaa Debisi take ta soma rera waƙa tana rawa na murnar zuwan jikokinta. Suma su Burodami kokodeen nan suka soma rawa suna mata tafi. Tana rera waƙar yarenmu ta musamman da akema ƴan biyu.
Gabaki ɗaya ɗakin hankalinsu yana kanmu. Murmushi kawai nayi musu, Uwani kuwa sai zolayar Iyaa Debisi take yi dama sun saba. Taiwo Iyaa Debisi ta riƙe, Burodami kokodeen kuma ya karɓi Kahinde. Sai murna suke yi, domun a ƙabilarmu babban abune haihuwar ƴan biyu, mun ɗaukesu a matsayin wata babbar baiwa da Allah ya bamu. Kuma yarenmu su kansa yaƙinin rayuwar ƴan biyunnan mai albarka ce. Ni dai a haka baccin gajiya ya kwasheni, bani na farka ba sai jefin la'asar. Ƴan uwana sun cika asibiti danƙam sai tayani murna suke yi. Ga abinci iri_iri an kakkawomun. Burodami Debisi ya zubo mun amala da miyar ewodu, da miyar wake, da jar miya dukka, ga ganda haka_haka.
"Ga abinci kici ko zaki samu ƙwarin jikin naki, gida zamu tafi" Karɓa nayi na mishi godiya. Ƴan uwa kuma aka shiga yi mun ya jiki, tare da murnar zuwan Taiwo da Kahinde duniya. ( Hassana da Usaini ) Amalata naci nayi ƙat na kora da kunun akamu me zafi, take naji na yi gyatsa mai ƙarfi, bana jin komai garau nake jina tamkar ba ni bace na haifi ƴan biyu ba. Wajajen shidan yamma aka sallamemu muka fito asibiti mota biyu. Duk tare muka ɗunguma mazanmu da matanmu zuwa gida. A tsakar gidan muka tarar da matan gidan kamar dai kullum ana zaman gulma da kace_nace.
"Ahh Æ´an biyu aka samu kenan? Kai masha Allah barka da arziki Iyabo." Cewar Yaya Haula.
Yauwa sannunku" Iyakar abinda nace kenan. A Æ´an uwana kuwa babu wacce ta kulasu, suma basu kula kowa ba, mu kai shigewarmu ciki. Mazan a falo suka zauna, mu kuma muka shige cikin uwar É—akin. Anty Mulka tace.
"Abun girkin ki na ganshi a falo. Anan zan dafa miki ruwan wankan ne, ko zan iya fita ƙaddararren tsakar gidan naku?" Sai da na ja numfashi nace.
Zaki iya fita dashi ki sa ta gefen É—akina, kafin Gwadabe ya zo ya kawo itace" Sai lokacin Bose tace.
"To wai shi gogan bai san kin haihu bane?" Kafin in yi magana Uwani tace.
"Na kirashi na sanar dashi. Yana hanyar dawowa daga legos ne, da ƙyar ma na samu wayar tashi ba sabis. Amman yace abokinshi Bara'u zai tawo daga ƙauye, duk abinda ake buƙata zai yi kafin shi ya iso, dan yace mun zasu iya kaiwa ma ɗayan dare basu shigoba, wata ƙila sai Asuba ma zasu shigo kanon." Tsaki Iyaa Debisi tayi tace.
" Isokuso asan. ( Banza marar amfani)"
Haƙiƙa naji zafi ainun, kuma maganar ta dokeni, ai ko banza Gwadabe uban ƴaƴanane." Anty Mulka ta fita bakinta a taɓe. Bose ta fita da zanin jini da muka dawo dashi daga asibiti, Uwani kuma ta ci gaba da mun gyaran ɗaki, sauran ƴan uwa kuma suka fita falo wajen su Burodami.
Zuga su Yaya Haula su ka yi, suka shigo da sallamarsu, Iyaa Debisi ce ta basu izinin shigowa. Suna shigowa ta miƙe ta koma falo"
"Iko sai Allah, Iyabo dama kunsan ƴan biyu ne a cikin naki, ko kuwa sai da kika haihu tukunna?" Cewar Gude uwar son jin ƙaƙa aka haifi mutum.
A'a dama tun cikin ma yana wata huÉ—u da akayi mun sikainin akace Æ´an biyu ne. Kun gansu mace da namiji. Taiwo da Kahinde kenan" Yaya Haula tace.
"Au suma sunan yarbawan za'a liƙa musu, babu ko karar a saka sunan Mahaifin shi Gwadaben, ita kuma macen asa sunan Babala, sai wani Taiwo da Kahinde?" Uwani ce ta juyo tace.
"Ba tana nufin sunan yarbawa za'a saka musu ba. Taiwo da kahinden yana nufin Hassana da Usaini kamar yadda muke cewa a Yaren Hausa. Tunda ai kunsan ba ko waÉ—anne Æ´an biyu bane ake sake musu suna ba, ko a cikin hausawa "
"To wannan ko dole a sake musu wallahi. Kun mayar da Gwadabe sai kace sususu kawai" Cewar Yaya Haula wacce da gani ta fusata. Uwani ba kanwar lasa bace na santa sarai shi yasa na katse zancan dan gudun kar su kira mun ruwa, dan ƙyas su Bose suka ji wata hayaniya zasu shigo ayi ɓatacciya, dan kowa cike yake da haushin kowa, sai kace ba Allah ɗaya muke bautama ba.
Ya'isa haka Uwani dan Allah. Yaya Haula Gwadabe na da ikon ya zaɓama jininshi duk sunan da yake da buƙata. Ni bani da ikon sashi yayi abinda baya so. Ko Toye ma shi ya zaɓi ya saka domin yai na mahaifina Allah ya jiƙan rai takwara"
"Tunda ya kasa yi ma nashi Allah ya ji ƙan ran takwaraba. Ai baki zo kin ganshi da mahaifinshi a raye ba. Dama yarbawa akuyarku ai tayi kuka wajen juya miji da jarabar bin baba lawo" Ta sake faɗa da karfi . Na riga da nasan tarzoma take son tayarmun, ayi rikici su sake kafa hujja akan jarabar yarbawa, da ƙin zaman lafiya. Haka dai suka fice a ɗakin bayan sun yi mun barka. Ni dai ban basu yaranba, dan a al'adarmu bama ba da yaro jariri ga mutane aita jagwalgwalashi. Suma sun sani tun a haihuwar Toye, kuma sun yi rantsuwar ko yara ɗari zan haifa ba wacce zata sake yinƙurin ɗaukar jaririn. Cikin ikon Allah a ƴan uwana babu wanda yaji kace_nace ɗin data faru, bayan fitarsu Uwani tace.
"Iyabo sai fa kin yi da gaske dangin Gwadabe zasu iya barinki kici gaba da rayuwa a gidannan, wannan ƙiyayyar ta yi yawa. Wallahi ko ahalul kitabi ce ke ya kamata su sarara miki haka. Duk da su kansu Iyaa Debisi sunƙi su zubar da makaman yaƙinsu. Amman ɗazu fa kinsan ina dawowa rufe miki ƙofa da kikace. Su Haula suna falonki suna kallon ɗakin. Ita kuwa baƙar kadararcan a Uwar ɗakin ki muka ci karo tana miki bincike a sib, har ta ɗakko wata atampa mai ruwan malmo, kai gaskiya kina cikin wani yanayi." Shigowar Sakina ne ya katse mana hirar.
Ah Sakina kune a tafe da yamma sakaliya haka? Maraba" Na faÉ—a ina dariya. Uwani tace.
"Kaga uwar gida, kuma Amarya a gidan Bara'u, Sakina lale." Cewar Uwani.
"Lale Uwani, ashe Iyabo uwar biyu an samu kai. Sannu fa mai jego. Bara'u yana falo yace a kawo mishi yarin zai musu huɗuba." Miƙewa nayi na saka mayafi, Sakina ta riƙe Taiwo ni kuma ina riƙe da Kahinde muka fito falon. Bara'u yana kujera shi kaɗai, babu kowa a falon, duk yanda akayi su Burodami kokodeen sun tafi gida ne, ko sun je su dawo. Sakina ta miƙa ma Bara'u Taiwo.
Ina wuni Bara'u. Da wannan yammar Gwadabe ya taso ku?"
"Haba dai ai Gwadabe ya wuci haka a wajena. Kuma dama muna shirin shigowa cikin garin jikin Babala yaƙi yanzu haka tana asibitin Murtala. Yaya Hambali da Sukairaju suna wajenta, amman ƙila ba gado za'a bata ba dai."
Allah sarki, ai ban sani ba. Zan shirya in je zuwa bayan magriba in dai basu dawo ba." Sai Sakina tace.
"Ke da kike fama da kan ki kuma?" Bara'u daya fita sanin dawar garin yace.
"A'a in dai akayi magriba sai ki rakata ta je ta dubo jikin ai dai ba za'ace bata nuna kulawarta ba ko ba gaskiya ba" HuÉ—uba yayi ma yaran da suna Hassana da usaini kamar yadda yace Gwadabe ya bashi umarni.
"To yara na yi musu huɗuba da asalin sunayen da ƴan biyu suke zuwa dashi, wato Hassana da Usaini. Taiwo da Kahinde a yarenku kenan. Sabida haka a ɓangarenmu Hassana da Usaini suke. A naku ɓangaren kuma Taiwo da Kahinde Allah ya raya su da imani" Miƙo mun yaran yayi na amshi ɗaya Sakina ta amshi ɗaya muka shiga ciki.
"Me za'a É—aura na dare ne Iyabo magriba ta kawo kai ma?" Cewar Uwani kafin in bata amsa Iyaa Debisi ta shigo da ruwa a bawo na wankan yara ta dasa kujera.
"Fun mi ni omo ( Bani yaron) Ta furta ranta a mugun haɗe. A sanyaye na miƙa mata ina fatan kar a kuma samun matsala makamanciyar ta haihuwar Toye.
Uwani ai inaga ba sai an yi girki ba, ga Amala a kuka da faten wake, ai ya ishemu, gobe a É—aura girkin."
Nabata amsarta. Anty Mulka ce ta leƙo tace dani in je in yi wanka ta kai mun ruwan. Wanka nayi na gargasa jikina sosai na ji daɗi. Ina fitowa Su Anty Mulka suna shirin tafiya gida Burodami kokodeen yazo zai kaisu gida. Godiya nayi musu sosai, mu kai sallama suka fita ni kuma na koma ciki. Anan naga kayan abincin da su Sakina suka kawo mana, garin tuwon masara, kuka daddawa, busassun kayan miya, albasa, shinkafar hausa, da gyaɗar miya harma da man ƙuli jarka guda, da bushasshen kifi" Godiya nayi sosai gami da yaba ƙwazon Bara'u, ya kuma yi dace da macen da bata hanashi yin aikhairin sai ma taimakonshi da ƙara ƙarfafashi da take yi."
Chapter 14 · 0% Book details