Sashe 111
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
tara kuɗin da zan sa Dada murmushi ya zama tarihi. Wajajen ƙarfe biyar na yamma saiga Amaduyal da matarshi, da Jatau da Hari. Sun tawo dubiya. "Amaduyal sai yanzu?" Na tambayeshi, shida ya dace sassafe ace ya tawo. Matar tashi ma sai yanzune taga damar zuwa, surukarta bata da lafiya" "Baffane ya riƙeni Adda, kuma tun duku_duku yasani a gaba muka tafi kiwo. Kari kuma sai nace tayi abinci ta jirani muna dawowa sai mu tawo. Kiyi haƙuri Adda amman wallahi jiya ga Kari ko rintsawa banyiba. Tunanin halin da Dada take ciki ya dabaibayeni" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. To Shikenan Allah ya kyauta. Kaje ka dubo du Cubu kuwa, a wanne hali suke?" "Naje, suna cikin damuwa sosai. Baffa dsi yana ƙarfafasu, a bakinsu naji labarin anyi ma Dada tiyata" Hari ta katse mana zancanmu ta hanyar gaisuwa. Jatau yace. "Amaryarmu Yaya jikin Dada?' Ɗan dariya nayi mishi kawai. Hari sai zolaya take faman yi. "Jabu wannan matar Amaduyalce sunanta Kari. Kari wannan itace yar Amaduyal" Matsowa Kari tayi ta tsugunna muka gaisa tare da tambayar me jiki. Jiki da sauƙi Kari muna jiran farkawarta tukunna." Sai ɗa su Kari su kai magriba sannan suka ɗau haramar tafiya gida. Nera dubu goma Amaduyal ya zaro ya bani. Jatau kuma ya bani nera dubu biyar. Sallama dasu suka tafi. A hanyata ta dawowa daga sallar isha na hango Yaya Hamma daga nesa yana tafe kici_kici da manyan ledoji a hannayenshi. A gaskiya Yaya Hamma mai ƙoƙarine sosai. Tunda muka zo asibitinnan yake ta faman hidima damu, da ajjihunshi, da jikinshi, da lokacinshi baki ɗaya. Bayan munyi sati guda a asibiti Jikin Dada ya soma yin sauƙi duk da har zuwa wannan lokacin bat gane suwaye a kanta. Yaya Hamma ya koma bakin aikinshi a asibiti yake kwana ko za'a buƙaci wani abun, da sassafe saiya shirya ya wuce wajen aikinshi dama a cikin birni yake aikin. Ni da Baɗɗo nakanje gida, in huta in yo mana girki sai in dawo, itama takanje ta wuni a gida ta dawo. Miyar stew nayi mana mai yawa sai muke siyan farar shinkafa dafaffiya a bakin asibiti, ko kuma mu sai biredi mu dangwala da miya tunda bama rabo da ruwan zafi, dan abincin da ake kawowa gashi ga kamarshi miya ce kamar an wanke kan mahaukaciya. Anan zan dakata sai mu tara gobe in Allah ya nuna mana.