← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 237

Sashe 50

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 É—inki kuÉ—in karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundati
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm

NAMA YA DAHU
ROMO ÆŠANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

15
Kafin tace.
"Ba dai shekara biyu ba, dan a ƙalla ba a ƙasaru ba, zaku iya kaiwa shekara guda kuna biyan kuɗin jirki da duk abinda aka kashe muku. Sai dai in babban gida kuka samu suke biyanku kuɗi da kyau, amman in ba haka ba shekararnan sai kun yita. Babu rufa_rufa sai kun gama biyan kuɗin jirgi zaku samu damar yin aikin hajji da umara baki ɗaya. Amman muddin kuka zama masu hazaƙa da kazar_kazar to gidan da za'a kaiku aiki zasu soku, kuma in dawowarku najeriya tayi, su hadoku da goma sha tara na arziki." A nan na fahimci Saudiyya zata turamu, sai naji hankalina ya ƙara kwantawa. Kafin mu baro gidannan mata da tsofaffi a ƙalla mutane fin ishirin sai da suka shigo, duk akan batun tafiyar. Ni dai mun tsayar da magana akan gobe da safe in zo mu je hajj kam aimun fasfo kafin in koma garinmu, nan da wata ɗaya da kwana goma jirginmu zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki.
Muna tafe muna ɗan tattaunawa har bus ta saukemu a unguwar su Uwani. Muna sauka muka ci karo da mijin Uwani yana zaune a wata majalisar maza ƴan sa ido. Zumbur ya miƙe da ganinmu ya nufomu gadan_gadan.
"Ke Uwani daga ina kike?" Ya faÉ—a a fusace. Tsaki uwani ta ja tace.
"Aikin banza aikin wofi, ka dai ji kunya ka kuma yar da zuchiyarka kare ya cinye. Maza majiya ƙarfi masu zuchiya, ka gansu a titi suna aikin sufuri dan su rufa ma iyalinsu asiri. Banda kai Hafizu baka da aiki sai zaman majalisa, duk matar data wuce kuna ƙarema surarta kallo, ka barni da buga_buga mata a layi duk sun rainani" A faɗace take maganar tana yi tana kumfar baki. Shima zabura yayi ya ce.
"Duk macen da take fita dai ba da sanin mijinta ba mala'ikun Allah har taje ta dawo suna tsine mata. Shashasha kawai." Tsaki ta buga fuu ta wuce ta barmu a tsaye.
Hafizu ka ƙara haƙuri dan Allah. Dama har yanzu irin wannan zaman na rashin daraja kuke yi ma junanku? Ga yara sai sake girma da mallakar hankali suke. Ko dan su ya kamata ku sarara dan kune allon kwaikwayonsu, kai tunda kaine babba ka dena biye mata"
"Shikenan Iyabo. Amman Uwani da kike gani bata da daÉ—i. Kwananta goma cib tana gaba dani, bansan sam abinda na aikata mata ba. Motsi kaÉ—an sai habaice_habaice"
"Iyabo wai ki zo mu tafi kin kuma tsaya wani lallaɓashi" Ƙwafa tayi ta kawar da kanta. Har muka isa gida tana zazzago mun mita.
A falo na kwanta ni da yaran, kafin gari ya waye kuwa suka jiƙani shakab da fitsari sai da nayo wanka kamar mai kwanan turaka dan har kaina sai da ya jiƙe da fitsari. Ai kuwa Uwani ta shiga jibgar yarannan kamar Allah ya aikota, haya_haya tsakaninta da Hafizu bai tsaya ba sai da ya gaji ya bar mata gidan tukunna. Ni na fitar musu da katifar na zuba ruwa katifar ta hau yarari tana gudana a tsakar gidan. Uwani kuma ta wanke musu kayan tas ta goge ledarta tsab da ruwan toka, gabaki ɗaya zarnin ya ɗauke. Dumamen tuwo tayi mana bai ma isaba saini na ba da hamsin aka siyi gasara da siga Uwani ta dama mana. Muna karyawa Hafizu ya leƙo
"Ki kawo mun abincina ina tsakar gida" Yana faɗa ya saki labulen tare da jan dogon tsaki. Kai mishi abincin tayi ta dawo muka ƙarashe namu, a gurguje muka fita a gidan bayan ta sallami yara ƴan islamiyya.
Ni ko Uwani kin je kin dubo su Toye kuwa?" ÆŠan murmushi Uwani tayi tace.
"Na yi tunanin Hamma ya goge miki tunanin Gwadabe ne ai Iyabo da baki tambayesu ba" Dariya nayi nace.
Ko kusa meye tsakanina da Hamma da har zai ture matsayin uban ƴaƴana a zuchiyata? Shi fa Gwadabe Mijinane, shi ko Hamma ɗan uwanene kuma wa a gareni mai kulawa dani. Uwani kinsan Allah son Gwadabe nunkuwa yake yi a duk ranar duniya, bana jin zan iya sauraren wani da sunan aure a zahirin gaskiya" Ajjiyar zuchiya na sauke take ƙirjina su kai mun nauyi.
"Naje kusan sau uku dubo Æ´an biyu. Allah cikin ikonshi ban samu ganinsu ba, har shi Gwadaben. Sai da mu kai zageni in zageka da wanna figaggiyar matar wan Gwadabe Haula take ko Zuriya oho" Gabana ya yanke ya faÉ—i nace.
Shikenan duk yanda akayi rayuwar yarannan ta koma ƙauye, ni da naso yaran su samu ilimin zamani tunda ni da Baban nasu iyakarmu kammala sakandare. Yarana sun zama ƴan ƙauye shikenan" Kuka na saka a hanya muna tafe kafin mu samu abun hawa. Da ƙyar da siɗin goshi Uwani ta shawo kaina. Amman fa har muka isa gidan Hajiya Salamatu bana cikin hayyacina, muna zuwa aka kwashemu a golf kusan mu tara zuwa hajj kam, anan muka amsa tambayoyi dai haka bamu jima ba duk yawanmu kuma akwai sanayya sosai tsakaninsu da ita Hajiyar. Muna bakin ƙofar Hajj kam ɗin a tsaye Uwani na kuma tausata wata mota fara sol tayi tsaye a gabanmu, ita bata wuce ba, gashi ta tare mana ganin gari" Wani dattijone baƙi mai haiba da kwarjini ya fito. Saye da yadin boyel mai ruwan ƙasa, kansa saye da hular zanna bukar, ga zobe ga agogo, ga takalminshi sau ciki irin na ƴan gayun maza. Abun almara sai muka ga ya tsaya a gabanmu. Gemu mai shi kombineshon ɗin fari da baƙi na kalla
"Assalamu alaikum ƴan mata" Ya furta da muryar kamana muryarshi da kauri irinta tsayayyi dakakkun maza, sai buso ƙamshi yake yi"
"Ba dai ƴan mata ba. Ko wacce da yaranta, kuma ai ko da wasa ba mui kama da ƴan mata ba" Cewar uwani balbalin kenan, ni ko fa bance komai ba. Wannan dattijo yayi murmushi har haƙorin makanshi fari ya bayyana.
"Allah ya ba manyan mata haƙuri. Dan Allah kuna da aure ne?" Ya tambaya, sai naga fuskarshi ta cika da fargaba.
"Ni dai ina da aure. Amman Iyabo a kasuwa take" Sai ya sauke ajjiyar zuchiya tare da murmusawa yace.
"Alhamdulillah. To Hajiya in ko babu damuwa inaso mu É—an yi magana a gurguje, dan gudun kar in katse muku hanzarinku" Carab uwani Tabalbalin tace
"Babu komai bari in matsa in baku waje" Ai kuwa sai ta karasa wajen matan da muka zo tare dasu tayi tsaiwarta
"Sunana Buhari Namoriki. Nazo shiga Hajj kam ne Allah yasa nai tsuntuwa dake. To a gurguje zanso jin sunanki da unguwarku sai in zo gida in sameki yafi mutunci" Ajjiyar zuchiya na sauke. Idanuna suka cika bam da ruwan hawaye, sai nake jin kamar tsaiwa da wani namiji da sunan soyayya tamfar cin Amanar Gwadabe ne"
"Malama Iyabo baki ce komai ba" Na ji sunana raÉ—au a bakinshi.
Sunana Iyabo kamar yadda ƙawata tace. Unguwarmu kuma ni ba ƴar garin bace ma, zuwa nayi gobe zan koma ina mai baka haƙuri" Murmushi yayi yace.
"Ai mai son É—an tsuntsu shi ke binshi da jifa. Kuma garin masoyi baya nisa, in kika bani dama ko adireshi zaki ganni"
Ba ko wanne garin na masoyi bane baya nisa. Ka ganni ƴar ƙauye ce a jeji nake rayuwata, babu wutar lantarki balle har sabis ya isa mana, gashi ban shirya aure ba. Wallahi ko zan yi aure bazan auri ƙabilar da zata zama tana ƙin ƙabilar dana fito ba" na ƙarashe zancen cikin rishin kuka. Hajiya Salamatu na hango ta fito, a wajen na tafi na bar Buhari a tsaye. Har motarmu ta fice fit yana tsaye yana ƙarema motarmu kallo.
Ko da muka isa gida Uwani Tabalbalin ta balbaleni da faÉ—a akan me zance ma Buhari haka? Ta tambayeni ne na bata labarin yanda mu ka yi.
Uwani ai ni da Bahaushe sai dai zumunci. Amman bazan sake auren Bahaushe ba. Bama yanzu zan yi aure ba kin ganni nan. Mu da muke da tafiyar da zamu yi har tsawon shekaru uku, da dakon soyayya kike son inje inyi wanna shekaru? Dame zanji, da mutuwar aurena, ko da mayar mun da yara ƙauye, ko da matsalar Dada?" Da rishin kuka na masifa nake maganar. Uwani sai ita ta sakko, zama tayi ta dafani.
"Kina da gaskiya ƙawata. Amman da ba irin rabuwar da kuka yi ba kenan. Rabuwa salamun_salamun yafi, domin bakasan inda rana zata faɗi ba. Batun yaranki da zan baki shawara ki ɗauka da kin sa ƙafa kin yi fatali da sha'anin, domin yafi ƙarfinki. Ba dole sai sun yi karatun boko darajarsu zata ɗagu ba, akwai arzikin da yafi noma ne? Babu shi da noma yaranki maza zasu iya azurta Iyabo, ita mace aure dama ka iya kaita jeji ma, ki bisu da adda'a zata bisu har gadon baccinsu Gwadabe kuma nasan ya cika jarumi, kuma yayi miki halacci. Amman cireshi a zuchiyarki wajibun ne saki ukune a tsakaninku. Ke ko saki ɗaya yayi miki yaci ki haƙura kema kiyi fatan samu sabuwar rayuwa a gaba. Kawo ɗari a siyo taliyar murji mu ɓararraka ina da maggi da ragowar manja. Kullum aikin kenan nike faɗi tashin neman abun rufin asirinmu, ke Iyabo har wanki da guga inayi a cikin gidannan, yawon wanke_wanke a gidajen masu hali ko shagunan cin abinci har ya zamemun jiki" Ɗari da hamsin na bata dan yara ma in suka dawo sa lasa. Ita da kanta ta fita ta siyo, tare mu kai hidimar komai muka baje a tsakar gida, Maman Shamsu tana zaune a kan turmi tana fige kasa tana waƙoƙin neman masifar da ta saba. A tukunyar muke ci, mun ɗebama yara nasu, Hafizu kuwa nayi roƙon duniya ta dibar mishi Uwani tace bai isa yana zaune a majalisa yana aikin bin matan mutane da ido ta ajjiye mishi abinci ba.
"Amman iyaa Debisi da shi kanshi Debisin basu san kin shigo Kano ba?" Sai da na haɗiye taliyata na tsotse yatsuna daya jiƙe da romon da ya ji kafi zabo kafin nace.
Babu wanda yasan na shigo. Gobe zan daka sammako in koma. Zanje inci gaba da jiran lokaci in Allah ya kaimu. Kuma inaso in tattauna sosai da Dada ta san ƙudurina, ta goyi bayana akan tafiyar da kuma batun Mahaifin su Baɗɗo. Zan soma zama dasu Boɗɗo tukunna mu tattauna in ji ra'ayinsu. Kuma naso in ɗan dinga ba matan Rugar ilimin addini iyakar abinda na sani, ko dan karatun sallarsu ta yi kyau. To basu ma da lokacin kayinsu ne shine matsalar. Amman su ƴan uwan nawa zan tsaya a kansu kafin in tafi in ɗan gyara rayuwar tasu"
Washe gari asubar fari Uwani ta rakani tasha, ta ɗan tsintomun kayanta kala biyu da wanda na sauya a jikina uku kenan. Naso in mata turjiya amman taƙi sam dole haka na karɓa. A tashar na ɗan sai maganin ciwon kai, da maganin ciwon ciki, da maganin zazzaɓi , dana rage zugi ko wanne kati_kati. Inaso in bayar a kaima Dada ta ɗan dinga sha, sauran kuma in ajjiye a wajena. Taran safe motarmu ta ɗaga.
Chapter 50 · 0% Book details