← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 237

Sashe 166

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nayi a raina nace kyaji in da daɗi ni da kikai mun a daren amarcina inaji ina gani. Rama cuta ga macuci ibadane" A wannan dare ni dai dangane da matsalar dake damuna akwai sauƙi da canji gaskiya. Sai tambotsai da na dinga yima Hamma duk ya fice a hayyacinshi yanata faman yi mun sannu. Karku mance banci abinci ba, wajajen ɗaya na dare sai nayi kamar irin abun ya lafa na laɓe a jikinshi da sanyin murya nace. Yaya Hamma yinwa nake ji sosai" Zaburar da yayi wajen tambayata abinda zanci saida ya bani tausayi na kanne nace. Sha'awar taliyar Hausa nake ji ta manja da ɗanyan kifi" Ba shiri ya zare idanu yana kallona. "Yanzu ina za'a samu kifi ɗanye Jabu? Taliyar Hausa dai naga Hama ta tawo dashi a cikin garar data dawo dashi, kifinne? Zaki ci haka ba kifin in tasota ta dafa miki?" Ai saina shige jikinshi na saki kukan kissa na sake tashin kanshi. Yaita rarrashi daga baya nace. Haɗa mun tea kawai in sha kawai gobe ka karɓo mun taliyar uwani ta dafa mun" Ajjiyar zuchiya ya sauke ya tashi faka_faka ya hura rushona da bana rabo da kalanzir cike da tanki, bana rabo da kayan tea ma da ɗan kabin biskit ko in mishi sallahun biredi. Tea ya haɗa mun na sha da biskit sannan na kwanta riƙe dashi ƙam. Albishirinku a wannan daren ba ƙaramin bacci mai shegen nauyi nayi ba, dan garin ma saurin waye mun yayi, alhamdulillah sumul nayi baccina. Ai yana tashina da asuba saina zabura na soma rikeshi ina ni karya tafi masallaci tsoro nake ji" "To naji zanyi sallar a gida. Kije ki ɗauro alwala kiyi sallah" Sai dai ai ka rakani, gani nake yi kamar wani abun zai kamani" Dole ƙanwar naƙi ya rakanu banɗaki tare fa muka shiga. Allah cikin amincewarshi muna fitowa muka tarar da Hama a tsaye a gefen banɗakin tana jiran a fito ta shiga bata ma san mu ne a ciki ba. Ga Hamma ya tallafoni hannunshi na ƙuguna ina dai jikinshi sosai. Wani dogon tsaki taja ta wuce banɗaki fu dariya ta kusan suɓucemun na dai kanne da ƙyar. Tare muka yi sallah a takure yana gaba ina bayanshi. Juyowa yayi ya kalleni yace. "Yaya jikin naki, kunje wajen mai maganin kuwa kun karɓo rubutun, ko jikin bai bari kunjeba?" Munje harma nasha nayi hayaƙin duka" Fuskata ya shafa yana murmushi yace. "Jabu nayi matuƙar farin cikin jin labarin cikina da kike ɗauke dashi zaki haihu dani mu sake zamewa abu guda. Ƴan ɓakin ciki su Ummu nabeeha, da M Farida Ammar, da Fadila Abdul, da masu mun fatan maciji ya sareni sai dai su mutu. Amman nasan su Khadija maidoki, Ramlex, A_A nafaɗa, da Mamanmu Hajara duk zasu taya mu murna. Nayi farin ciki sosai Allah yasa ki haifamun aboki da zai dinga tayani kiwo. Sannan ki dinga yin komai a hankali. Tunda Hama ta dawo zata taimaka miki" Idanuna na ƙanƙance nace. Ashe kasan Hama zata dawo jiya amman ni ka kasa sanar mun, baka iya ɓoyema Baɗejo abokinka ba. In ka faɗamun ai ba hanata dawowa zanyi ba face in mata adda'ar dawowa lafiya. Hala shine dalilin da yasa jiya kaƙi sakewa dani abinci ma loma biyu kaya ka ture" Shiru yayi yana kallona. Sai naga ya girgiza kai yana murmushi. "Mata a barku da kishi. Yanzu Jabu fishi kikeyi dan ban faɗa miki dawowar hama ba? Gimbiyar mata aimun afuwa gani a gabanki kuiwa a ƙasa banyi tunanin rashin faɗan zai ɓata miki rai ba" Sai naga ya dena annuri ya ci magani halamar yana son yin magana mai mahimmanci dani. "Jabu jiya a cikin damuwa nake ne. Sakamakon rasa aikina da nayi. Na saba da Alhaji mun kai shekara goma a matsayin masinjanshi, muna tare kuma yana kyautata mun tare da matarshi ma. Wannan shine dalilin da ya hanani sakewa inci abincin. Kuma wallahi Allah shine dalilin daya sha'afar dani wajen faɗa miki Hama zata dawo. Jabu ki yarda ni Hamma san da nake miki in zaki tara mazan duniya wallahi Allah ba zasu miki irin son da nake miki ba. A jiyan damuwace taimun yawa shi yasa" Jikina sai yayi sanyi shi yasa akeson a ko wanne yanayi kaima mutum uziri, sannan ka bashi dama kaji ta bakinshi kafin ka yanke hukuncin da zaka yanke. Meya faru ka rasa aikin ka Yaya Hamma, shine jiya ka ɓoye mun baka sanar dani mun haɗu munyi jimamin tare ba?" Hannayena duka biyu ya riƙe ya fuskanceni sosai. "Ritaya me gidan nawa yayi, zuwa jibi ma zai kwashe iyakinshi ya tattarasu su bar ƙasar baki ɗaya. Kinji abinda ya faru. To sai naga ya dace in mayar da hankalina wajen kiwo, da damuna kuma in yi noman abinda zamu ci a shekara ko da bai kai harda wanda za'a fitar a siyar ba ko? Amman ke meye shawararki?" Kai na girgiza nace. Wannan shawarace mai kyau. Allah sarki Hajiya ashe ƙasar zasu bari to Allah ya haɗasu da mutanen arziki a duk inda zasu koma. Amman ya kamata muje mui musu sallama ko?" Dariya yayi ya sauke ajjiyar zuchiya yace. "Ke da kike fama da rashin lafiya ina ke ina wani fita gari, yadda hanyarmu bata da kyau dinnan ga karamun ciki a jikinki. Ni kaina yau a cikin ɗakinnan zan wuni ina kulawa dake" Idanu na zaro ina mamaki, shi kuma ya soma mun cakulkuli ina dariya ina turmusheshi. Sai ganin Hama mukayi a kanmu. "Ai dama nasan babu ciwon dake damunki. Makirci ne jiya saida kika gama komai naki ni nama dawo gidan bakya nan, kina ganin Hamma kika narke. To ta Allah ba taki ba, kai kuma ka wuce muje ka karya." Murmushi nayi mai cike da kirsa, inna kalleta sai in kalleshi amsar da zai bata nake jira kafin in koreta a ɗakina. "Hama meke damunki haka wai, kar ki bari kishi ya sa ki aikata shirme fa. Kije zanzo inci abincin. Bai kamata kina shigowa ɗakin abokiyar zamanki sasakai haka ba. Musamman in ina ciki gudun kar kiyi gamo da abinda bazai miki daɗin gani ba. Kije ganinan" Ficewa tayi bata tanka ba. Ni kuma saina shiga yi mishi abinda nasan bashi da juriya ta wajen. Fisgoni yayi jikinshi yanai mun raɗa. "Zo muje a bani hakkina tunda abun hakane" Uwar ɗakinmu na labule muka koma anan komai ya gudana cikin soyayya da kwanciyar hankali. Babu abinda ke mun daɗi sama da inga Yaya Hamma ya samu nutsuwarshi dani, kuma a fuskarshi ina ganin farin ciki da annashuwa. Rigarshi ya zura ya fice. Ganin fitarshi, sai matan gidan Yafendo tasa sukaita leƙowa suna gaisheni da jikina harda mazajen nasu. Can sai ga Yafendo da kanta ta shigo da kwano a hannunta cike da farfesun zabuwa ta dure mun. "Jabu Yaya jikin naki da sauƙi ko?' Cikin kunya nace mata da sauƙi miƙewa tayi tace. "To Allah ya ƙara sauƙi ga nama nan ɗan romo romo kisha bakin ki yayi daɗi. Zamu je duba Cubu ni da Baɗɗo. In Yusufu yazo abincinsu yana madafi sai ya ɗauka" Tai mun sallama suka tafi. Suna tafiya na ɗaura ruwan wanka a risho yanayin zafi na juye na je nayo wanka na dawo, na ɗanyi kwalliya mai sauƙi ina zaune na kunna turaren tsinke ya cika ɗakin da ƙamshi sai ga Uwani ta shigo cikin shirin tafiya. "Kaga masu ciki mata a gidan Hamma. Kin haddasa musu fitina gasu can sunata cin uwar sabada muryarsu har tsakar gida. Matan gidanku akwai munafurci duk sun nutsu suna saurarensu ƙauye garin su kare" Dariya nayi muka tafa. Uwani hankali kawai na koya mata matsayina na gwada mata a wajen mijin da take takamar ita ya soma aura. Sannan bansan ta ina zan iya kwana ni ɗaya ba. Uwani Alhamdulillah jiya na samu sauƙi sosai wallahi nayi bacci me kyau yanzu ma ɗakin Baɗɗo nake son inje in sha magungunan. "To Alhamdulillah haka muke so, da izinin Allah wannan dai ya kau. Maza jeki kisha ba'a wasa. Kixo muyi sallama danni zan kama hanya. Na wanke ma Cubu kayanta tas in sun bushe a kai mata. Zuwa nayi ɗakin Baɗɗo na sha rubutu na shafe jikina da tofin da nayi na fito. Har zuwa wannan lokacin Hama sai ihu take harda kuka, Yaya Hamma dai bana jiyo muryarshi. Matan gidan duk sun watse gidan kuwa kamar kitchen ɗin ƙazama sai tarin tulin ƙudaje sunata bin Nono da madarar da suka zuzzubar a ƙasa da kayayyakin da akayi aikin nonon. Farfesun zabonnan na tarar Uwani na ci sanda na shigo. Nima na zuba inaci ina bata labarin yadda muka kwashe daren jiya. Uwani tayi dariya tace. "Ko kefa in ka fiye shiru shiru sai a raina ka. Amman da zaran kana ɗan tabukawa wani abun ma ba za'aima ba. Ya batun siyan kayan mata Iyabo? Akwai mai motar daya shigo damu Girei daga tasha. Ya sanar mun shi ɗan ƙauyannan naku ne wai yaron gidan malam Idi ne mai shanu, ko kun sanshi?" Kai na gyaɗa mata. Na sanshi ƙanin Baɗejo ne. Sunan mahaifinsu kenan" Uwani tace. "To bari Hamma yazo mu tabbatar. Ni da tunanina me zai hana in shi dinne kinga ai gidane, sai in dinga sa lambarshi a jikin kayanki in kaya suka iso Adamawa kinga shi za'a kira yaje ya karɓi kaya. Kinga zai kawo miki har gida. Ke kuma in kaya sun ƙare saiki fita gari kije ki samun kuɗi a banki, zan baki lambar account ɗina. To zamu yi waya kafin ki dawo ƙauyanku ki faɗamun duk abinda kikeso. Naga halama wannan kayan zaki samu alkhairai sosai." Haƙiƙa naji daɗin wannan shawarar taki uwani. Bari Yaya Hamma ya shigo muji. In akwai wasu kuɗaɗen ma a hannunshi zan ara a saro mun kayan da yawa in ajiye kinga guri ba kusa ba" muna cikin tattaunawa Yaya Hamma ya shigo. "Kawayen juna anata hirar ne." Yana daga tsaye a gefe suka gaisa da Uwani. Yaya Hamma. Gidansu Baɗejo shine gidan Modibbo Idi mai Shanu ko?" Kai ya ɗaga mun halamar e, sai na kuma tambayarshi. Suna da ƙani da yake tuƙun mota daga birni zuwa Girai ne Yaya?" "Juma kenan. Me ya faru?" Uwani ta mishi bayanin yadda muka tattauna. Shima yayo na'am da
Chapter 166 · 0% Book details