Sashe 2
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Iyabo:.
Tunda Gwadabe ya fito jikina yake ɓari, domin nasan danginshi kab ba ƙaunata suke yi ba, kuma ƙiris suke jiran kuskure na. Sai gashi yau azal ta hau kaina. Daman daren jiya cike na kwana da fargabar zuwa ƙauyansu Gwadabe da zamu je yau biki. Ina tsoron Allah ina tsoron abinda zai haɗa taron biki, ko suna a ƙauyensu Gwadabe ace kuma zanje nima. Ina muzanta, da takura fiye da tunani. Furucin da Gwadabe ya fesarma da Baban Nazifi ya fi firgitani fiye da dalilin rikicin. Ba shiri na buɗe labule na fito ina tura tsohon cikina gaba. Saye nake da leshi riga da zane. Rigar ɗinkin buba, zanin kuma ciki da alako irin ɗinkin yarenmu kenan. Idanu mu ka haɗa da Gwadabena tausayinshi ya sake dirarmun a zuchiyata, har nake jin ko ratayeni danginshi zasu yi, ni da Gwadabe mutu ka raba. Dan shi ɗin cikakken jarumin masoyine na haƙiƙa tunda ya aureni bai sake samun kwanciyar hankali da salama ta ɓangaren iyaye da dangi ba. A zamantakewata dashi kuma haƙiƙatan bai taɓa yi mun wani abun ashsha ba, riritani yake yi, gami da tarairayar zuchiyata tamkar ƙwai, hakanne yake ƙaramin ƙarfin zuchiya da jumurin shanye duk abinda danginshi suke yi mun. Sai dai irin zaman bashi da daɗi, yana raɓa rayuwata da dukkannin farin cikina. Damma Gwadabe na ƙoƙarin sharemun dukkan hawayena.
Dan Allah Baban Nazifi kayi haƙuri. Umman Nazifi dan Allah ki gafarceni wallahi bansan kina cikin banɗakin bane, ban watsa miki da ganganba" Na faɗa ina mai ƙoƙarin haɗiye kukana tare da shanye fishina. Idanu Gwadabe ya lumshe mun cikin sigar ban haƙuri, nima nawa idanun na lumshe mishi cikin bashi amsar shima yayi haƙurin. Idanunshi ya rufe ya buɗesu tare da ɗan zare su, halamar ya samu sassauci a zuchiyarshi. Dukkan wannan maganar kuramen masoyan dake gudana a tsakaninmu babu wanda yasan me muke nufi, amman dai suna kallonmu, idanun kowa a kanmu yake.
"Ke Iyabo kar ki sake zubar mana da kashi ta magudana, nan ba gidan yarbawa bane, dama ku yarbawa a cikin ƙabilu wama ya kaiku ƙazanta, da ɗaukar kashi ba abun ƙyama ba?. In banda ƙazanta yama zaki zubar da kashi ta magudana. Mu dai ana cutar damu da wannan kafirar ƙazantar ta yarbawa." Cewar Gude matar Yaya Sukairaju Kenan. Dama tafi kowa tsanata da caccaɓa mini maganganu kaifafa. Na ji zafin abinda ta faɗa a kan yarbawa, dan ina kishin yarena ina kuma alfahari da kasancewata Beyerabiya."
"Gwadabe da mun dawo daga Takai biki ka tattare matarka da É—anka ku bar mun gidana, na gaji da ganinku dukkanku." Da sauri na dubi Gwadabe, shi kuma ya kalli Baban Nazifi. Ba mu kaÉ—ai mu ka jijjiga da furucin Baban Nazifi ba, sauran yayyen Gwadabe da matayensu, harma da yaransu wanda suke fahimtar abunda akeyi sai da su ka girgiza.
"Haula mu je ki sake kayanki mu kama hanya banso takwas ta yi mun a gida ba. Sukairaju ku kama hanyar tafiya muma yanzu zamu kama hanyarmu" Take kowa ya watse ya barmu jijjunanmu a sanyaye sosai. Hannuna Gwadabe ya ja a hankali mu ka koma ɗaki. Muna shiga na zauna a kujera daɓas sai da kujerar ta yi ƙara kasancewata mai ƙiba da ɓaka_ɓakan mazaunai. Kuka mai gunji na fashe dashi. Gwadabe ya zauna a kusa dani ya dafe kanshi da hannu bibbiyu, idanunshi yayi jawur. Ya kasa furtamun kalma sai tubka da warwara kawai yake yi, tare da neman tudun dafawa. Mu da mu ke cin abinci da wuya ta ina zamu iya kama hayar muhalli? Dama dai burin dangin Gwadabe su ga mun tagayyara ne yau na sake tabbatarwa.
"Ki yi haquri Iyabo da duk abubbuwan da kike gani, kike ji, da wanda zaki sake ji in mun tafi Takai. Ina mai ƙara baki haƙuri kuma ki sani ni Gwadabe ina tare da sonki, ina sonki Iyabo fiye da son da uwa take ma ɗan cikinta. Ina mai baki haƙuri Iyabo bisa abinda dangina da naki dangin suke yi miki duk sabida Aurenmu. Ina alfahari da soyayyar da ni Gwadabe nake yi miki. Wallahi Iyabo kece sanyi da farin cikin ruhina. Ki share hawayenku mu kama hanyar Takai Sukairaju ya ɗakko mana bus zamu tafi baki ɗaya." Hawayena na share jikina a mugun mace murus, kalaman Gwadabe sun kashe mun jiki. Haƙiƙa Gwadabe na yi mun soyayya mai yawan gaske. Amman ko ƙafar inda nake son shi bai kama ba, gashi a kullum zuchiyata sake jarabtuwa da Gwadabe take yi.
Gwadabe yanzu in Baban Nazifi yace mu bar mishi gidanshi wanne tudu zamu dafa, ina zamu bi mu ga haske? Ka duba ka gani abinci da ƙyar muke ci. Wanke_wanke da sharar da nake zuwa yi albashin nera dubu biyu ne a wata, kuɗin ba yawa bane dashi. Kai kuma ba ko da yaushe oganka yake samun lodi ba balle mu samu ɗan kuɗin sallamar iyali da ake baku. Gwadabe ya zamu yi dan Allah?"
"A'a Iyabo Allah zai yi mana mafita. Zamu tattauna maganar a gaban Babala in mun je Takai. In ta goyi bayan Yaya Hambali kan mu tashi mu bar mishi gidanshi. Ba makawa zamu tashi duk da nasan bani da ko ficikar da zan iya kama mana haya. Dukkanmu a ƙasanta mu ke tunda ita ta haifemu, kinga tsohon ciki gareki damuwa da kuka ai ba naki bane ƴar yarbawata. Oh Allah yayi ba Debisi bane mijinki, ni ɗin dai da basa so ni na yi sa'ar samun ki, Alhamdulillah. Ko mutuwa na yi nasan na zaɓarma yarana uwa ta gari, ba zasu tuhumeni ba." Dariya nayi harda ƙyaƙyatawa, shima dariyar yake yi. Muka shiga tuno gwagwarmaya da muka sha kafin mu kawo wannan matakin. Duk da dai har gobe tsugunne bata kare mana ba. Tuni nasa ƙafa na shure matsalolin dangin Gwadabe na miƙe na shiga ciki dan ɗakko mana jakar kayanmu. Toye yana kwance sai baccinshi yake yi a shirye yake tsab. Mayafi na ɗauko na jawo ƙaramin akwatin kayanmu da jakar kayan Toye. Ni banso tafiya ma dashi ba naso in Kai shi gidanmu, sabida nima fama nake da kaina cikina wata bakwai amman girmanshi yasa ake mun kallon haihuwa ko yau ko gobe. Toye shekararshi shida da haihuwa sa'anninshi na gidan duk sun shiga makarantar islamiyya mu bamu da kuɗin saka shi a makaranta, in yaje ma ana koroshi kuɗin laraba, inna samu ko ni ko Baban sai mu biya. Amman da zaran laraba tayi bamu biya ba ake koroshi, sai Gwadabe ya yanke hukuncin ni na dinga koya mishi Abacada, Gwadabe kuma yana koya mishi baƙin arabic. Shigowa yayi ya saɓa Toye a kafaɗarshi ya zari akwatin kayanmu.
"Zaki iya ɗaukan jakar kayan Toye ko in kai wanna in dawo?" Murmusawa nayi na ɗauki jakar kayan da jakar hannuna, na bi bayanshi. Gaba su ka yi, ni kuma na tsaya na kulle ƙofata na biyo bayanshi. Da ƙyar fa nake tafiya gashi duk na yi kumburi, ga hawan jini na masu juna ina fama dashi. Ko da muka fito, sai muka tarar Bus ɗin ta cika duk sun ɗaura yaransu a kan kujerar sun babbake.
"Motar ba zata isaba Gwadabe abinda za'ayi ku je ku hau motar haya zaifi." Cewar Sukairaju yana gama faɗar haka suka ja motar fu, Bus ɗin na gaba motar Baban Nazifi na biye, kana motar Harisu ta rufa musu baya. Yawu Gwadabe ya haɗiye muƙut jijiyoyin kanshi suka fito raɗa_raɗa.
"Mu je tasha Iyabo" A daƙile yayi maganar. Ni kam ina biye dashi ko gani bana iya yi sosai tsabaragen tashin hankali da damuwa. Shikenan na yi sanadiyyar raba kan wannan zuriyar masu son juna da son zumunta? Gwadabe tunda ya aureni ya zama saniyar ware a dangi. Ina jin rashin daɗi da na zame mishi silar zama mujiya a cikin dangi. Har mu ka isa tasha banji Gwadabe ya ce komai ba, hakan ya sake damuna ainun gashi muna hanya babu damar in rarrasheshi ko zai samu ɗan sassauci. Ga wani ruguntsumin ma yana jiraye damu a Takai. Mota ya sama mana Bus ni da shi ne a can baya ta ƙarshe wajen window, Toye yana rungume a jikinshi yana baccinshi. Yaron na ƙura ma idanu ina mai cike da tausayinshi da abunda yake cikina ta yanda zasu rayu cikin rashin gatan dangi ɓangaren uwa da uba, Toye ko cikin yaran gida ya shiga bashi da damar yin wasa dasu, yaran zasu shiga yi mishi waƙar da iyayensu suka saba rerawa a tsakar gidan. Suna tafi suna cewa Yarbawa masu kwalo_kwalo da ɗuwawu suke tuƙin tuwo. Toye sai yai ta kuka abunka da yarinta, wataran ma da gudu yake dawowa ya faɗa jikina. Ta bangaren dangina ma suna adawa da aurena da Gwadabe sosai da sosai kasancewar shi Bahaushene ba Beyerabe ba. Rabon ƴaƴane da ƙudurar Allah ya tabbatar da aurena da masoyina Gwadabe.
"Tunanin me kike yi haka Iyabo mai zurfin gaske. Kaddai akan furucin Yaya Hambali ne akan mu bar mishi gidanshi? Iyabo ni kaina inaso mu tashi a gidan ba tun yau ba. Ko dan kema ki samu yancin yin rayuwar Æ´anci irin wacce ko wacce mace take fatan samu. Na yi imanin dangina ba zasu zo har gidanki su takura miki ba, ko zasu takura miki ba kamar in gidanmu É—aya ba. Ni da na zame musu dole zanyi zumunci dasu..."
A'a Gwadabe wannan ba zai ma yiwu ba. Babala ba zata bar Baban Nazifi ya tozartamu ba. In muka bar gidannan ina zamu shiga a ina zamu dinga samu kuɗin da zamu biya haya? Sannan yarannan zasu sake rasa dangin mahaifansu ta dukka ɓangarori biyu. Amman in dai muna taren a gida ɗaya su Toye zasu taso da sanin lallai su Nazifi ƴan uwansu ne danginsu ne, a gida ɗaya akayi tarbiyyarsu. Kar ka mance Babala ma burinta kenan ganin kun haɗe kawunanku da na iyalinku baki ɗaya. Ka yi haƙuri da batun tashinmu,madamar ba Babala bace ta goyi bayan Baban Nazifi akan tashin namu ba. Kasan sai ka ƙara mun baƙin jini a wajen danginka" Idanu ya lumshe kawai sai girgiza kanshi yake yi. Ɗan guntun siririn hawayen daya surnano mun na yi maza na share gudun kar Gwadabe ya buɗe idanunshi ya ga zubar hawayena. Har Bus ɗinmu ta cika muka fito daga tasha bamu sake magana ba. Ko wanne cikinmu aikin tubka da warwara kawai yake yi a zuchiyarshi. Motarmu sai gudu take shararawa bisa titi, tun muna wuce titinan cikin gari muna wuce manyan gidajen sama, da manyan shopping mall har mu ka soma wuce ciyayi da fasassun kwalta, jagab_jagab ɗin hanya ne yasa Gwadabe yai ta mun aikin sannu har muka shiga cikin ƙaramar hukumar Takai.