← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 237

Sashe 79

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

muka haɗa ido da Khalifa. Ganin hawaye a fuskata caɓe _caɓe yasa shi saurin miƙi hannunshi yana son ya share mun. Da mugun sauri na miƙe na fita da gudu a kitchen ɗin. Baya na fita naje na saka wanki a injin jikina har rawa yake yi mini. Dana dawo kitchen ɗin na tarar baya ciki. Ajjiyar zuchiya na sauke, kana naci gaba da aikina. Sai na sake tsananta adda'a nice kullum cikin tsaiwar dare ina roƙon Allah ya tsare mun mutumcina, Allah kar yaba kowa damar iya tunkarata dai dai da maganar iskanci. Kullum cikin kuka da miƙa lammurana ga Allah. Khalifa bai daina shigowa ɗakinmu tsakar dare ba. Sai dai kullum zai shigo ya same ni ko ina sallah, ko da carbi a hannuna dai. Wasa_wasa lokacin sai tafiya yake yi. Yau da gobe rayuwa sai garawa take yi. Kamar wasa yau wata na shida cib a gidan aiki. Yau na tashi da farin ciki marar misaltuwa. Uwar ɗakina ta faɗamun tun jiya akan in shirya zanje ( Ijaza) Ma'ana zan tafi hutu can Riyahd. Tun safe na gama aiyukana tsab. Misalin ƙarfe Takwas na Safiya muka kama hanya, harda Khalifa ni dashi muna bayan mota, Uwar ɗakina da mijinta suna gaban mota. Zuchiyata a cike take dam fa farin ciki da ɗaukin son tozali da Uwani. Ko ba komai mayi hira muji daɗi ai. Tafiya mu ka yi sosai, ni sai yau ne naga nisan wajan sosai. Muna isa bakin kofar gidan na gane gidanne. Khalifa ne ya miƙo mun wata takadda a cikin gidan saka wasiƙa. Yaimun nuna da idanunshi akan in karɓa. Hannu nasa na amsa ni dai jikina bai bani ba. Tare da ƙunshin kayana dama nake. Sallama nayi da uwar ɗakina anan take shaidamun nan da sati guda zata aiko khalifa ya dawo dani. Cikin zumuɗi nake ta haura benen, sai dai bayana wani irin riƙewa yake yi tamkar bayan tsohuwar data gaji da duniya. Ina yi ina hutawa harna ƙaraso hawanmu. Ɗakin da Hajiya Babba take na soma shiga. Naje na sameta da baƙin wasu Larabawa da nake tunanin masu ɗaukar ƴan aiki ne. A wulaƙance ta amsa gaisuwata, abun ya dake ni sosai, domin wulaƙanci ba abin so bane. "Ke kika matsa musu kina son kizo hutu ko? Dan uwar ɗakin ki ta kawo ƙararki har sau biyu. Tace baki da aiki sai kuka. Dukanki suke yi, ko wani abun yaran gidan suke miki? Gashi naga kin lalace har kinfi kyau sanda kika tawo daga Najeriya" Duk wannan maganganun cikin ɗaga murya da harara take yinsu. Ajjiyar zuchiya na sauke tare da cewa. Ina zaune tace in shirya zanje Ijaza, ni ba roƙo ba. Maganar kuka kuma damuwa da kaɗaici ne suke sani kokawa, ai bawa ba'a iya rabashi da kuka. Imma na farin ciki, ko kishiyar hakan" "To uwar tsari. To zan kirata inji Allah yasa ba sallamarki tayi ba. Kin samu gidan mutanen kirki, duk cikin ƴan uwanki da kuka tawo daga Najeriya albashinki yafi nasu tsoka. Wata huɗu ya rage miki ki gama biyan kamfani kuɗinsu, daga haka kuɗi zasu dinga zuwa hannunki ya rage naki kisan yanda zakiyi dasu." Jin wannan daddaɗan labarin ya sani a farin ciki dan haka da murna na fita a ɗakin zuwa ɗaya daga cikin ɗakunan. Ina buɗewa naga Hadiza na kwance tana hutawa. Ganina yasa ta washe bakinta. "Ƴar halak kin ƙi ambato. Ko awa guda Uwani bata yi da yin maganarki ba sai gaki" Zama nayi a katifar dake kusa da tata. Uwani tazo kenan yaushe?" Na tambayeta. "Ai inajin zata kwana biyar haka. Tama kusan komawaa da rabon zaku gana ne, ni gobe ma zan koma" Gaisawa mu kai da juna. "Iyabo wannan rama haka. Kaddai kema a cikin tsaka mai wuyar fita kamar ni kike?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Hadiza a tsaka mai wuya nake. Ni fa a gidan aikin da nake ko baccin kirki banayi, sabida bargaba, ga aiki kamar zan mutu, bayana da ƙirjina ciwo suke yi" Hadiza ta share hawayenta tace. "Talauci da neman na rufa ma kai asirine ya kawo ni wannan ƙasa. Akwai wata ƴar maƙotanmu bazawarace bayan ta baro gidan mijinta sai ta tawo Saudiyya aiki. Iyabo a cikin shekaru biyu kacal iyayenta suka sauya, mahaifinta har mota yake ja, gashi ta gyara musu gidansu. To shine mahaifiyata ta matsa mun akan nima in tafi, haka na bar mata yaron da nake goyo na tawo. A gidanma nike aikatau ina lura da marayun ƴaƴana da iyayena. Sai gashi a gidan aiki saurayin gidan har wuƙa yake nuna mun, akan sai na bashi haɗin kai. To bani da zaɓi dole haka na bashi haɗin kai yake biyan buƙatarshi dani dan dole. Gashi ni bansan hanya ba bare in gudo. Iyabo na dawo Ijaza sai nake sanarma Hajiya Babba halin da nake ciki akan a sake mun gidan aiki. Hmm kar ki so ganin zagin tsaman naman da tayi mun. Da ƙyar ta yarda akan za'a sake mun gidan aiki. Ni gobe zan kama wani aikin." Kukane da tausayinmu gabaki ɗaya yake shirin cin ƙarfina. Haƙiƙa na tausaya ma Hadiza matuƙa gaya. Dan kawai kana aiki a ƙarƙashinsu sai su nemi tilasta maka akan abinda sun san haramcinshi. Taya yaron gida zai hakkema mai aikin gidansu, dan kawai ta tawo ƙasar da ba tata ba, tana neman guminta? Ya Allah ka dubi bayanka ka kawo mana ɗauki. Allah kasan zuchiyarmu ba iskanci ya kawo mu wannan ƙasa ba, neman kuɗi ne ya kawo mu ya Allah ka karemu da karewarka. Hadiza na tausaya mana duka. Ni kaina ayau ba sai gobe ba zan faɗa ma Hajiya Babba inason sake gidan aiki. Tun kafin Khalifa ya samu nasarar keta rigar mutuncina. Yaron gidan da nake aiki ne yake kawo mun hari. Kullum bashi da aiki sai kawo kala_kalan ƴan mata" Hadiza ta share hawayenta tace. "Gara mu sake gidan aiki. Ko Allah zai sa mu yi dace da irin gidan da Maryam ta samu. Baki ga Maryam ba yadda tayi kyau ba. Gashi da zata tawo Ijaza sababbin abayoyi aka sai mata gwanin sha'awa" Ɗan murmushin tausayinmu na kuma yi. Uwani ina suka je ne?" "Hmm sun tafi miƙe ƙafa da ganin gari ita da su Maryam. Uwani ma baki ga ramar da tayi ba, juyin duniya taƙi faɗin matsalarta sai kuka ba dare ba rana" Ana cikin haka p'a ta rako wasu mata su huɗu, ƴan ƙasata najeriya biyu, sai ƴan nijer suma su biyu. "Iyabo ijaza kika zo yaushe banga shigowarki ba?" Ɗan murmushi nayi na miƙe muka fita da p.a Yanzu zuwana p.a Hajiya Babba ta sallami baƙinta kuwa?" "E sun tafi yanzu haka ma Airport take son tafiya zata ɗebo baƙin Najeriya. Ince dai ba cewa zakiyi a sake miki gidan aiki ba, dan abinda Hajiya Babba ta tsana kenan." Kai na girgiza tare da cewa. Gidan aiki kam zan canja, domin samun tseratar da mutuncina. Ni bazawarace ina da yara har uku, ga iyaye da ƴan uwa. Ai bazan so in ɗebo musu abun kunya ba, daga zuwa aiki, in bari tarbiyata ta taɓu ba" Murmushi p.a tayi mun tace. "Wani hanzari ba gudu ba Iyabo. Da dirinki da kyanki ni nayi mamaki ma da kika zauna a gidan aikatau harna tsawon wata shida. Nayi tunanin harkar samun maƙudan kuɗi cikin sauƙi shi zaku ɗauka daga ke har Uwani na ganku tubarkalla. Da a fita ɗaya ma zaku biya bashin da kamfani take binku, kuma ku zama ƴan lele a wajen Hajiya " Da mamaki na dubeta. Dama akwai hanyar da ake samun kuɗi cikin sauƙi shine ba'a nuna mana ba?" Dariyar cin nasara p.a tayi mum ta dafani. "Yanzu ki koma. In Hajiya Babba ta fita zanzo ɗakinku mu tattauna kafinnan Uwani sun dawo" Da wannan zancan muka rabu da p.a. Ina juyawa da zummar komawa ɗaki na jiyo muryar uwani. "Iyabo" Ta kirayi sunana. Da sauri na juyo muka haɗa idanu, ba ƙaramin ramewa Uwani tayi ba, sai naga tayi wani irin haske. Take gabana ya faɗi. Tana ƙarasowa muka rungume juna sai kuka kamar ƙananun yara. Su maryam kuma su kai shigewarsu. Ɗago Uwani nayi na riƙe kafaɗarta. Uwani kin rame da yawa. Sai naga kinyi ɗanye kamar me yaron ciki" Sai ta sake fashewa da kuka. Ɗakin da babu kowa a ciki ta jani muka shiga. "Iyabo ina cike da nadamar baro ƙasata Najeriya, ina mai cike da fargaba da tashin hankali marar misalin da za'a musalta balle har a fahimta. Iyabo ciki ne dani na tsawon wata biyu" Da sauri na toshe mata bakinta tsabaren tashin hankalin dana tsinci kaina a ciki. Matar aure da cikin da bana mijinta ba Na faɗa a cikin raina, a fili kuma nace. Uwani baki faɗa mishi ke matar Aure bace to?" "Na faɗa mishi da kwaɓaɓɓen turancina. Amman Iyabo yaƙi yarda. Kullum cikin dare sai ya baro matarshi yazo ya tare a ɗakina. Kuka da majiya baya hanashi aikata komai. Na dawo da tarin kuɗin da bansan iyakar yawanshi ba. Musamman da nace mai cikine dani. Ya bani kuɗi masu yawa yace in na tafi kar in dawo, in matarshi ta gane shi yai mini ciki dani dashi zata haɗa ta kashe. Iyabo abinda bakai da ƙuruciya ba, sai da aure a kan ka. Me zance da Hafizu, me zance da su Hajiya?" Kukane yaci ƙarfinta. Niko sai kallonta nake yi ina auna girman abun. Cikin dauriya nace. Da Hadiza tace jibi zaki koma, can gidan kike son komawa?" Kai ta Girgiza. "Inata tunanin ta hanyar da zan ɓulloma da Hajiya Babba ne. Naga irin ɗibar albarkar da taima Hadiza data buƙaci sauya gidan aiki. Ni Iyabo yaya zanyi da cikinnan?" Wallahi Uwani ban sani ba, ƙasa ba taka ba. Amman bari Hajiya Babba ta dawo, ya zame mana dole mu tunkareta ko dafamu zata yi taci. Ki share hawayenki Allah zai kawo mana mafita. Taso mu koma cikin mutane" Hannunta na kama muka koma ɗakinsu Hadiza. Duk cikinmu in aka cire Maryam babu wacce take walwala, sai kuma baƙi da basu san dawar garin ba. P.a ce ta leƙo ta yafitoni ni da Uwani. Ta shigar damu wani ɗaki kamar na ajjiyar kayane haka, amman da halamu anan ita take kwana. "Ku zauna ga katifa" Zama
Chapter 79 · 0% Book details