Sashe 62
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
da wani auren ruga, kiyi fatali da wani Hamma. Kinga ƙasar zamu bari Iyabo soyayya ba taki bace. Shigowar Yaya Hamma da Hafizu ne ya dakatar da tattaunawar tamu. Sun zauna babu daɗewa nace. Uwani Hafizu mu kam zamu tafi gida. Sai gobe kuma in Allah ya nuna mana." Tare su kai mana rakiya izuwa titi har sai da Bus ɗinmu ta tashi sannan suka juyo. Kwatsam su Iyaa suna tsakar gida suna wannan hira tasu mai kamar faɗa muka shigo. "Ah Ah ah ah Iyabo. Ikabo ( sannu da zuwa)" Nan ta miƙe ta soma rawa harda guntuwar waƙarta su Iyaa Beji na mata dariya. Dukkansu saida na bisu ɗaya bayan ɗaya na dinga zubewa a gabansu ina kwasar gaisuwa bisa ga al'adarmu. Yaya Hamma dai duk abinda yaga nayi shi yake maimaitawa. "Lekan, Lekan woo ah" Lekan ya amsa da karfi sai gashi harda gudu. "Ahh Antimi Iyabo Ikabo o ti dara osale ( Anti Iyabo Sannu da zuwa Ina wuni?)" Owo bawo ni o se n se? ( Yaya kake Lekan)? Nima na tambayeshi da yarenmu. Hannu ya miƙa suka gaisa da Yaya Hamma kana yace mun. "Owo mo dara Antimi ( Ina lafiya Anti) "Mu u lo si yara re ( Kai shi ɗakun ku) Cewar Iyaa. Ni kuma ta jaye hannuna muka shige ciki. "Ashe dai zaki zo Iyabo? Nayi kewarki sosai. Sai inta mafarkin ki. Har sai da Debisi yaje ya dawo ya tabbatar mun kina lafiya sannan na samu nutsuwa. Sai kika ga Debisi ko?" Murmushi nayi mata nace. Sai gashi Iyaa babu zato" Dariya tayi kawai kana tace. "Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba. Dama dan ya samu nutsuwa ne yasa na ce ya aureki dan zaki fi ganin darajarshi da kimarshi sama da ko wacce mace. Amman sai ya nuna shi baya so. To wacce yake so din gasu can kullum cikin faɗa, ko jiya uwar haka suna gidannan anata shari'ar da ni na gaji da'ita. Yanzu dan Allah da ke ya aura hankalinshi ba kwance ba?" Kasa amsata nayi, dan da kunya Debisi dai ita ta tsugunna ta haifeshi. "Shi wannan ɗin da ya rakoki ko shine oko omo obirin ɗin nawa? (Sirikina). Kai na sauke ƙasa nace. A'a yaron Ƙanwar Dada ne. Dama zan tafi saudiyya aikataune shine ya biyoni in mun tashi sai ya koma shi kuma" "Ah Ah orira ( abun mamaki) Saudiyya fa kika ce?" Sai ta miƙe ta shiga rawa tana jero mun waƙoƙin sanya albarka. Har sai da ta tara mun matan gidan. Nan take kowa yaji abinda ke faruwa. Nan gidan ya kacame da waƙoƙi da murna. Bayan sun tafi ne Iyaa ta bani Amala tace. "Ki kaima Ɗan uwanki amala yaci abincin yarbawa" mayafina nasa na ɗauki kwanon na fice zuwa ɗakin lekan. Da sallama na shiga na samu yana kallon wani film na yarbawa. Shi kaɗaine a ɗakin sai lemun kwalba na limca dake gabanshi.