← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 237

Sashe 120

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Iyabo da wuya ta kasheki gara daɗi ya kasheki. Ki tuno da irin taimakonmu da Saleem yayi mana a lokacin da muke da buƙatar taimakon . Dubi Ahalinshi yadda suka karɓeki duk da kina matsayin baƙar fata, beyerabiya. Ki duba kuɗi da Saleem ya kashe miki. Kayanmu gashi sun iso suna gidana. Ki duba Saleem ya baro ƙasarsu yazo gareki Iyabo. Irin sakayyar da zaki mishi a ƙasar taku kenan?" Uwani ta ɗaureni tamau da dukkan jijiyoyin jikina. Illahirin jikina a mace yake murus. Gaskiya Saleem bai cancanci irin wannan tarbar daga gareni ba. Ɗan murmushi nayi na dubeshi. Ya riga da ya gane akwai matsalane, dan yanayinshi ya sauya, jikinshi kuma yayi sanyi. "Zuwana ya haifar da matsalane Zauja? Ya tambayeni da larabci. A'a Saleem. Ya hanya ina fatan kazo lafiya?" Murmushi yayi tare da sauke ajjiyar zuchiya har yana dafe saitin zuchiyarshi. Hararata Uwani tayi, ta miƙo mun wata jakar kwali wadda sabida ruɗu ni ban ganta tare da jakarnan ba sai yanzu. "Gashi wannan tsarabarki ce daga surukarki" Fizgewa nayi dan a wuya nake da Uwani. Dariya tayi kawai tace. "Iyabo kenan. Baƙin halin naku na yarbawa masu kwalo_kwalo ya motsa kenan?" Banza nayi mata, na mayar da hankalina ga Saleem tare da yi mishi godiya da tsaraba, na tambayi lafiyar mahaifiyarshi da danginshi duka. "Duk suna lafiya kuma sunce a miƙo miki saƙon gaisuwarsu gareki. Kuma sunyi mun fatan nasara. Meke damun Mamane haka, sannan me yasa aka kawota wannan asibitin, kuma ɗakin duk mutane." Ɗan murmushi nayi. Duk wannan abun fa hankalina yana ga Hamma. Babu komai asibitin yana da kyau. Kuma jikinta ya warware an kusan a sallamemu mu koma gida in sha Allah." "To Shikenan zanje in yi sallah inna dawo sai mu tattauna, kuma a gabatar dani ga magabata ayita ta ƙare ko zan samu nutsuwar zuchiya." Kwatancen hanyar da zaiga masallaci nayi mishi. Yana tafiya na dubi Uwani nace. Yanzu Uwani yaya zanyi? Ni da Hamma lokaci kawai muke jira, ina tabbatar miki da ba dan ciwon Dada ba da yanzu wata maganar akeyi ba wannan ba. Wallahi Uwani ni zuchiyata tafi nutsuwa da Hamma fiye da Salim batun ƙauye ko ƙauyanci kuma ni naji na gani zan rungumi aurena in zauna a ƙasata ni yafi mun rufin asiri. Ki tuno irin baƙar azabar da muka sha a hannun larabawa. Shi Salim ɗinnan kinsan mazinacine gangaran, tantirin mazinaci ma kuwa, dani dake da Faty duk fa mun sani. To ina sane bazan auri mazinaciba, ni abun hannunshi bai tsole mun idoba, Uwani kiyi tunani. Zina yaɗo take yi ta lashe zuriya, ki duba mazajen larabawa da yawansu kamar Ayu suke dan tsabaragen son mata" Jim Uwani tayi can ta dubeni tace. "Yanzu ke dai kinji kin gani Hamma dai kike so zakiyi haƙuri da duk abinda in kika shiga zaki gani, shin tunda kin kawo hujjojinki na ƙin auren Saleem shin Iyabo me zai hana ki nutsu ki yi kasuwancinki da sannu Allah zai ɓullo miki da wani, shin ko a matse kike?" Sosai kuwa, muna fatan ganin alkhairi. Nifa na tsorata da sha'anin larabawa ko karen hauka ya cijeni bazan auri Salim ba. Uwani ki mishi bayani an riga an haɗani auren zumunci da ɗan uwana wanda suka gaisa saura sati ɗaya ma ayi bikin in samu mu rabu lafiya" Mun daɗe muna tattaunawa, Uwani ta jima tana bani baki akan nayi nazari kafin yanke hukunci. Ita a tunaninta dan gudun dana sani. Ni kuma babu dana sani a soyayyata da Hamma. Har Salim ya dawo bamu tsaida matsaya ba. Ciki na shiga na kawo mishi madarar shanu a gora yasha sosai sai santi yake yi mana. Uwani ce ta nutsu ta soma yi mishi bayani da larabci kasancewar ta fini ƙwarewa a yaren. Salim hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba har ƙwalla saida ya zubar wallahi. "Allah shine shaidar son da nake yi miki. Ni nasan harda tsoro yasa kika ƙi aminta dani Iyabo. Yaya zanyi da sonki, kinsan sonki zai iya zautani kuwa?" Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna. Salim duk ya birkice abinka da farin mutum har fuskarnan tashi ta Zama jawur da'ita haka ma idanunshi. Salim kayi haƙuri bazan iya saɓa ma iyayena domin faranta nawa ran ba. Yayana suka zaɓa mun. Ina mai baka haƙuri , Allah ya ɓillo maka da wacce ta fini alkhairi a rayuwarka da addininka. Na yaba nayi godiya da soyayyarka a gareni kayi haƙuri " murmushi yayi mun yace. "Ina sonki Allah. Amman na haƙura har ga Allah kuma ina roƙon Allah ya baki zaman lafiya da mijinki ya baki zuriya ɗayyiba. In na haifi yarinya zan saka mata sunanki Iyabo" Sai zuchiyata naji ta tsinke ainun. Babu shiri hawaye ya shiga gudu a kumatuna. Billah da zan iya amsar son Salim da zan amsa. Amman kash ko wacce zuchiya da abin sonta, kuma ko wacce ƙwarya tana da abokin burminta. Jabu zaka saka ma yarinyar taka. Sunana kenan ta ɓangaren mahaifiyata." Dariya yayi yace. "Jabu what a nice name" Miƙewa yayi tsaye hannayenshi a cikin aljihun jallabiyarshi yana kallona yana nazartata, ko kuma karanta wasiƙar jaki. "Zan koma Kano. Jibi zan koma inda nafi wayau. Zaki ga saƙona inna koma ga wannan gudunmawatace ki sai gadon da angonki zai hau ku raya sunnah nayi imani zan samu lada. Kiyi alƙawarin siyan gadon kar ki saɓa Jabu.' Kuɗi masu kaurin gaske ya bani, wanda a wannan lokacin inna canja kuɗin zasu iya kaiwa dubu ɗari biyar irin ta da bata wannan zamanin na tinubu ba. Godiya nayi mishi har tashar mota ni da Uwani muka rakashi dan ita tace zata kwana biyu ta tayani jinyar Dada. Sai da muka ga tashin motarsu yanata ɗaga mun hannu idanunshi fal ruwan hawayen bankwana. Kuka na saka rikitaccen gaske na runtse idanuna tsigar jikina sai tashi take yi. Tausayin Salim ya dirarmun sosai." "Ki dena kuka Iyabo, na fahimci ke kanki bawai son Saleem bane bakya yi ba A'a. Son da kike yima wancan figaggen ne yafi na Saleem. Kamar yadda Hamma yake sonki fiye da Saleem ɗin. Muje magriba ta kawo kai, kiyi haƙuri ki fuskanci yadda zaki fahimtar da gogan naki naga ya ɗauki zafi, fulani dama suna da tsantsar kishi gaskiya. Nifa mamaki iskancin Hamma yake bani " Wallahi Uwani ni tausayi ya bani. Jibi yadda yake kuka kamar ƙaramin yaro fa. Uwani ni nasan raɗaɗin son maso wani. Sannan ni ina gujema matsaltsalun rayuwane. Na tsorata da auren mijin da ba yarenku ɗaya ba. Fulani da yarbawa kuma suna da daɗaɗɗen tarihi na zamantakewa da auratayya. Bugu da ƙari Hamma jininane, ina tsoron kada son abin duniya yasa in zaɓi Saleem harga Allah Hamma nake so" Uwani ta ja gwauron numfashi tace. "Iyabo na fahimta, ni kaina waɗannan tunane tunanenne du banyi su ba. Duk da dai masu iya magana suna cewa abinda aka gasa shi yaji wuta" Fitowa mu ka yi daga tasha muka tari abin hawa zuwa bakin asibiti. Gogan yana tsaye a bakin asibiti da halama ya kafane ya tsare yana son ganin ta inda zan ɓullo. Gabana ya yanke ya faɗi ganin irin kallon tuhumar da Hamma yake yi mun. "Uwani baƙon ya tafi ne?" Ya tambaya yana kakkafe ita uwanin da ido. "Ya tafi Hamma. Dama dai ya matsa ne yana son yaga Jabune, sabida kayan da yawa bazai yiwu ace ya tafi ba tare da ya ganta ba." Murmushi yayi kawai ya kalli tsakiyar idanuna, saiya soma kallon ƙwayar idona da ɗaya da ɗaya. Ta gefena Uwani ta shige. "Wannan soyayyar taku inna tsaya anan Hamma sai zuchiyata ta buga" Cewar Uwani data yi shigewarta ciki. "Me yazo nema a wajenki, kuma me yasaki kukan da har fuskarki da idanunki suka sauya launi?" Wannan tambaya tashi ta sake rikitani, bansan me zance mishi ba. "Ki shiga ciki su Hama da Daso suna ciki. Ni zanje masallaci inna dawo zan raka Hama gida" To Shikenan sai ka dawo" A gurguje na wuce tare da sauke ajjiyar zuchiya a haka dai kamar fishin nashi ya sassauto. A wajen gadon Dada kuma su Daso suna zazzaune a tabarma suna fira ita da Hama ƙawarta. Gefensu kwanukan abincine da suka kawo. Uwani kuma tana zaune a kujerar roba inda nake zama. Ina isowa Hama ta dena hira ta haɗe girarta ta ƙasa data sama. Ita kanta Daso na ga canji sosai a yanayinta. Nasan yana da nasaba da tsaida lokacin aurenmu da Hamma. Sannunku Daso ashe kunzo, ina wuninku?" Daso ce ta amsa babu yabo babu fallasa dai, Hama kuwa bata ce um ba, wasa take da hannun ɗiyarta dake kwance a cinyarta. Uwani wannan itace Daso yarinyar ƙanwar Dada Yafendo Jabu me sunana. Wannan kuma Hama ce matar Yaya Hamma " "Ayya, ai mun gaisa kice itace uwargidanki. Hama Allah ya sanya alkairi Allah ya haɗe kawunanku" "A gaskiya baiwar Allah baki kyauta ba ai ba'ayin haka. Sanin kanki ne babu macen da take son kishiya, ita kanta Jabun da ita za'aima kishiyar aka mata haka ba zata ji daɗi ba" Daso ce tayi maganar cikin fishi da fishin Hama. Sanin halin ƙawata Tabalbalin yasa nace. Kuyi haƙuri itama bata faɗa da niyya ba" Tsaki Hama tayi, Uwani tace. "Allah sarkin girma inji kishiyar mai Ɗuwayya. Allah ya baku haƙuri ni ba baƙuwar zafi bace. Amman fa ku iya bakunanku in kuma ba haka ba sai dai kuji jini na zuba, ƴan iska ƙauyawan banza duk kun cika waje da ƙarni." Duk wannan abun da akeyi Dada bacci take yi. Fulatanci da Hama ta soma zazzagowane ya farkar da'ita. Nasan dai ba alkhairi Hama take faɗi ba. Ɗiyarta ta goya tana ta huci. "Daso meke faruwa ne?" Dada ta tambaya. "Babu komai Dada" Amsar da Daso ta bata kenan. Ana cikin haka sai ga Hamma ya iso. "To muje ko dare nayi. Dada saina dawo zan kaisu gida" "To dama ka zauna a gida. Jabu da ƙawarta zasu kwana anan. Kaima ka huta. Ka sanar da Baffa Musa, inason ganinshi gobe da sassafe. "Haba Dada. Kona koma gidan ma ni bazan iya bacci ba. Likita ma ya tabbatar mana zuwa gobe ko jibi zai sallamemu mu koma gida. Hama muje" Fuuu Hama ta fice ko sallama batai mana ba, Daso ce kawai taima Dada sallama
Chapter 120 · 0% Book details