Sashe 217
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
yarinya yake son Aure. Yayar Usman Anty Sumayya ce ta buƙaci ganina Hajja Mama tasa aka kawota ɗakin maƙotanmu dana je na ɓoye kaina ina risgar kuka. Shigowarta yasa nayi shiru Tayi matuƙar kama sosai da Usman dake ita macece harta fishi haske. Ina ganinta na gane itace cikin girmamawa muka gaisa harma ta kira Usman ɗin take faɗa mishi ai kuka ma ta taddani inayi dai haka. A ranar suka bi jirgi suka koma Gombe akan ɗaurin aure a Kontagora za'aje ayi can asalin gidan iyayen Hajja Mama. Ta nunar musu can ne family House ɗinmu. Haka dai mukaita shirye_shirye Usman ya turo ma Hajja Mama wadatattun kuɗi akan ta sai mun kayan ɗakina masha Allah, bata siya ba tace mun in muka je Gombe ma siya acan a jera mun komai. A cikin lefennan na dinka kusan rabin kayan dan Usman yace yana dawowa kwana uku zaiyi mu koma India, kunji fa wata ƙudurar Ubangiji. In aka kaini Gombe Anty Sumayya zata kaini aimun paspo. To kar ku mance na taɓa yin paspo a baya fa. Ranar juma'a aka ɗaura aurena da Usman a Kontagora gidan su Hajja Mama. Muma duk can muka ɗunguma muka tafi dan ana ɗaura aure zasu jiya da Amarya dalilin da yasa aka tawo da mata kenan ƙannen mahaifin Usman. Ina ɗaki kaina na mun wani irin ciwo kamar zai tsage, ga wani irin faɗuwar gaba dake damuna. Ni a tunanina yana da nasaba da aurena da aka ɗaura sai ga kiran Usman ya shigo wayata. Da ƙyar na ɗauka dan jikina har rawa yake yi na kara wayar a kunnena. Sai na fashe mishi da kuka kawai. "A_a Gimbiya kar ki karya mun zuchiya kisa inyi tunanin ba sona kike yi ba mana. Kiyi shiru kinji ko? Yanzu za'a kai mun ke gidana a matsayin mallakina. In sha Allah zan tallafi duk maraicinki da rashin gatanki. Daga yau kin zama mai gata. Ki nutsu ki mana adda'ar samun dukkan alkhairai ina dawowa zamu tafi zaku je ayi miki paspo ke da Anty Sumayya zata rakaki. Nan ma sai faman rarrashi nake yi, itama Suhaila inata fama duk da dai nata da sauƙi. Kiyi shiru ki tashi kisa kaya masu kyau kar ki bari dangina da dangin abokan zamanki su raina shigarki uhm?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. To Shikenan zanyi yadda kace nagode sosai da kulawa. Ina fatan ka kula da rayuwarmu sannan Allah ya bamu zaman lafiya da fahimta a tsakanmu baki ɗaya mu huɗun" "To Ameen. Daɗina dake kin iya sarrafa harshe kamar wata marubuciya. Allah yayi albarka" Da haka mu kai sallama sai naji dama_dama a jikin nawa. Hajja Mama ce ta shigo mun da kayan da zan saka wani farin lace ne fari tas mai tsadar gaske, da takalmi da jakata suma na gasken, da mayafina duka farare. Dama sarƙa da ɗan kunne dake wuyana silver ne. "Saka kaya maza mu je ashe a jirgi zamu je mu bamu sani ba. Goggona da ƙanwata su ne zasu kaiki a matsayin iyaye. Iyabo kiyi ƙoƙarin birne wannan sirrin dan Allah. Kinsan Allah bayyanuwar rashin asalinku barazanane babba. Kinga famaly babba kika shiga kuma mijinki na da ƙanne maza duk masu aure ne. Saka maza ki fito" Saya kayannan nayi Hauwa ta sake gyara mun kwalliyata na fito shar dani kunsan masu ƙiba ba yabon kai ba kwalliya da ado yafi karɓarsu, gashi na sha ƙunshi ja da baƙi, ga kitso ƙananu irinna matan kanuri an yarfa mun. Ƴan biyu na wajen su Hauwa muka fito, sai shatar motoci aka ɗauka zuwa filin jirgi. Misalin biyu na rana jirginmu ya ɗaga zuwa Gombe ƙarfe 3 da minti goma muka sauka a filin jirgin Gombe motoci daga ɓangaren ango suna waje suna jiran Amarya. Ni dai ni da Hauwa da yarana muna bayan wata ƙatuwar mota sai ajjiyar zuchiya kawai nake sauke wa, da kuma hawayen da ke sakko mun lokaci zuwa lokaci har muka iso cikin unguwar fediral kwatas a wani katafaren gida motocinmu suka tsaya. Ni dai sai ƙare ma unguwannin kallo nake yi ina mamaki har muka shiga cikin gidan mai yalwar tsakar gida. Dangin Usman ne cike da gidan ashe nan gidan mahaifinshi ne ba can gidan shi ba. Ɗaki aka bamu sukutum mu da su Hajja Mama akan zuwa gobe kuma sai su shiga kasuwa su siya mun kayan ɗaki. Dangin Usman sun karramani sosai, sai tururuwar zuwa ganina ni da ƴan biyu suke ta yi, daga ƙarshe ma ficewa akayi da ƴan biyu zuwa can ɓarayin Alhaji Baba kamar yadda suke kiranshi. Lokacin ne na samu na ɗauro alwala a ban ɗakin cikin ɗakin na yi Sallah. Ina idarwa sai ga kiran Usman ya shigo wayata. "Gimbiya barka da shigowa Family na. Kiyi haƙuri kinga an wuto dake family House ko? Alhaji ne yace sai dai ku sauka a ɓarayinshi abinda bai taɓa yima wata suruka ta gidan ba kenan. Yanzu dai ki sake sauya kaya zaku fita da Anty Sumayya yanzu batun paspo." To Shikenan muna godiya da wannan karramawar Allah ya saka da Alkhairi" "Ameen daɗina dake abinda bai taka kara ya karya ba sai kiyi ta godiya da shi albarka" Hirarmu dai ba ta yi nisa ba muka ajjiye wayar. Da zallan soyayyun kaji da aka tsoma a jajjagen attaruhu da albasa aka tarbemu da jus na kwali masu daɗi gaske na gwaiba sai daga gidan uwargidan Usman aka aiko tuwon sakwara da miyar egusi lafiyayyen gaske. Ni bamma ci abincin ba wanka kawai nayi na sake kayana muka fita ni da Anty Sumayya a mota har zuwa ofishin paspo. "Hajiya menene sunanki, sannan shekarunki nawa" Sunana Iyabo." Tofa kafin ya gama rubuta sunan sai ya dubeni yace "Iyabo Adetoye? Ai kin taɓa yin paspo ɓata yayine?" Shiru nayi ina zare idanu a ƙoƙarina na son tunawa. Kafin in yi magana Anty Sumayya tace. "Tunda kaga munzo kuma tasan ta taɓa yi ƙila ta rasashi ne a bamu sabo kawai. Ko Iyabo?" Ta yi maganar tana murmushi nima murmushin nayi mata wanda bai kai ciki ba. Inata tunani da ƙoƙarin ko zan tuno ɗan wani abun ko da babu dai yawa. Wannan ma'aikaci yace. "Babbar Yaya gobe zan kawo muku in sha Allah har gida kuje kawai. Ai da munsan ta taɓa yi ma da ba sai kunzo ba suna kawai zata faɗamun" Sallama mu ka yi mishi muka koma gida. A babban falon gidan muka tarar da Alhaji Baba ya sakko daga sama da matarshi surukanshi sun zagayeshi da jikoki. Fari kyakkyawan namiji mai cikar haiba. A gabanshi na durƙusa na gaisheshi. Ya amsa mun da fara'a tare da shi mun albarka. Da kanshi ya dinga nuna mun matan ƙannen Usman. Mazajen nasu daga lauya, sai ɗan siyasa, sai likita gasunan dai gwanin ban sha'awa. Matan kuwa tamkar zaɓosu akayi dan kyau. Ko wacce da gani tana ji da asali da dukiya. Ai saima na raina kaina ƙibatace kaɗai ta ɗan ceceni ma na cika musu idanu. "To kuje na sallameku zanje masallaci. Sumayya abar Iyabo ta Zauna har zuwa lokacin da Fodiyo zai dawo. Munyi waya dashi ɗazu yake sanarmun bazai samu tasowa jibinnan ba sai sati mai zuwa. To ta zauna kawai in yazo ya ɗauki matarshi su wuce daga gidannan. Ko kuwa Hajiya Iya?" Matarshi kenan. Amman ba ita ta haifi kusan manyan gidan ba, ƴaƴanta sune ƙanana a gidan. Amman a halin yanzu itace kaɗai a wajen mijin nata. "Hakan yayi Alhaji Baba. Sai ta zauna ai tunda ga waje" Nan kowa ya watse ni nayi ɓarayin da aka bamu, suma duk suka kama gabansu. A zazzaune na shiga na samu su Hajja Mama sunata hirarsu cikin nishaɗi ga ƴan biyu a gefen Batula. Gaskiya ƴan biyu zasu yi kewar Batula sosai itace uwar renon nasu dama. Haka dai muka raba dare muna hira Washegari bayan mun karya kowa yayi wanka, sai su Hajja Mama suka nufi kasuwa bisa jagorancin Anty Sumayya. Ni kuma Hajiya tazo ta kirani na koma ɗakinta dan anata zuwa ganin Amarya. Nice har azahar ina takure gashi Batula da ƴan biyu suka tafi. Matan ƙannen Usman sai ɗan jana da hira suke yi barin ma Maman Usman da take cewa itama mijinta yana india yaje yin wani kos. Tare ma zasu dawo da Usman. Kuma in mijin nata zai koma tare zasu koma ma dinga haɗuwa. Ni dai sai ɗan murmusawa kawai nake yi. Sai wajajen magriba su Hajja Mama suka shigo gidan. "To Iyabo kije ga ƴan uwanki can sun dawo ko?" To Hajiya nagode sosai sai da safenku Maman Usman " Dariya tayi tace. "Muma yanzu duk zamu tafi, sai kuma an kwana biyu zamu leƙo kafin uncle ya dawo." Ina shiga cikin ɗakin da su Hajja Mama suke sai naga jikinsu duk a mace. Gabana a faɗe nace. Hajja Mama lafiya?" "Ina fa lafiya Iyabo. Ke dai ƴannan Allah dai yasa Usman ba da niyyar cutarki ya aureki ba, ko kuma da mummunar manufa ba. Domin magana ta gaskiya mun tsorata sosai." Gabanne ya yanke ya faɗi ras" Kafin ta gama rabe ɗayan biyu Nima nake cewa sai ranar tilitin in Allah ya kaimu Mrs Bukhari