Sashe 64
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
ÆŠAURIN AURE.
Su kuma da safe akeyin É—auri in dai na budurwane. Sannan ana fitarma da maza Æ´an É—aurin aure abinci waje aci asha a goge wuya.
*WATSI*
Wannan ɓangaren gidan ango ke yi.
Bayan isha ko bayan magriba za'a shinfiɗa tabarma a zaunar da ango a tsakiya. Ai ta mishi watsin cingom da kudi shima ya danganta da ƙarfin dangin ango, amman a wannan watsin ango na samun kudi ainun.
ÆŠAUKO AMARYA
Bayan an gama watsi kuma dangin Ango zasu je su É—auko Amarya a kaita É—akin mijinta.
Iyaye suna yin hidimar kayan É—aki sosai, gado biyu suke yi, banda kafet_kafet da manyan daddumai.
*YININ BIKI*
Shima bikine rigi_rigi ake yinshi, sannan a yinin bikinnan suke sa anko dangin ango dana Amarya. Ayi yinin biki a watse shikenan biki kuma ya ƙare.
Daga cikin wannan sha'ani na biki babu wanda aka raga. A zahirin gaskiya an kashe kuÉ—aÉ—e sosai, duk wata hidima da akayi Tasi'u da matarshi ce suka gudanar da duk wani kashe kuÉ—i.
Gwadabe kuma a lokacin sha'anin bikinne ya karema ragowar ƴan matan gidan kallo tsab. A tsahirance sunfi Hadiza kyau ta fuskokinsu, sai dai ita kuma Hadiza ta fisu diri da kiba, dan shi kuma baya sha'awar mata sirara sam. Da wannan dalili nashi ne ya ƙudurce a ranshi da zaran an watse biiki zai tunkari Baba Magaji da batun Amincewarshi ga Hadiza. Ga Tamu ko da yaushe su kai waya yakan yi mishi tuni da batun ƙanwarshi da take zaman jiran Gwadaben. Harma sun yi waya sau biyu haka. Yanda ya ɗan taɓa hira da'ita sai yaji babu dai wata matsala a tattare da'ita ko na rashin tarbiyya, ko na fitsara irin ta wasu matan. Ƙarshen wayarshi da Tamu a cikin hidimar bikinnan yake cewa da Gwadabe.
"Gwadabe duk ɗan abinda ka rarumo na kudin moya kazo ayi aurennan kowa ya huta. Bara'u yace ya ɗauke maka sadaki. Ni kuma zanyi mata akwati da kaina. Aure kawai zaka zo a ɗaura, sabida manema sun soma damunta, duk da dai bata ƙarashe karatun ba amman ƙiris ya rage' Jin wannan batu ne yasa Gwadabe kiran Bara'u yai mishi bayanin halin da yake ciki akan ɗiya da Baba Magaji ya bashi harma da kyautar wajen zama. Bara'u shi kuma ya tafi kafa da ƙafa har Habuja su kai magana da Tamu. Ya nuna ai wannan ba komai bane, Gwadabe mijin mace huɗu ne bama biyu ba. A take suka kirashi suka tsaida magana kan da zaran yarinyar ta gama karatunta za'ayi auren. Ƴan biyu dake hannun Tamu sai wayau suke yi, suna karatunsu hankali kwance. Ayashe tana riƙe dasu da amana ta game yaran da nata ta maishesu tamkar yaran data tsugunna ta haifa. Haka ma Toye yana zuwa makarantar boko data allo, suna zuwa gona yin noma. Dan Bara'u ya siya musu ƴar ƙaramar gona da yaron wajenshi, harma bana sun noma gyaɗa na kwano uku, da taimakon Sakina dake rakasu gona tana kuyi wannan ku bar wancan
Amare sun tare a gidajen mazajensu lafiya, hankalin iyaye ya dawo jikinsu kuma kowa ya ci gaba da sha'anin gabanshi. Wata ranar talata da daddare bayan su Gwadabe sun gama karatun dare sai ya nemi ganawa da Baba Magaji kan batun Hadiza. Dan yaga tun bayan da aka yi bikin gidan. Sai zawarawa suka shiga zurubtu akanta, suka shiga hidimar kashe mata kudi. Dan samarin nijar jaruman gaske ne akan matansu.
"Baba Magaji dama akan maganarmu ne da kai. Shine nace na zaɓi Hadiza kamar yadda kaima ka zaɓa mun tun farko. Sai dai akwai ƙanwar abokina Tamu da shi Tamun ya bani tun kafin in tawo nan ɗin. Shine nake tunanin in ka amince sai a haɗa tare ayi bikin lokaci guda. Tunda ita yarinyar kafin lokacin da aka kintata na bikin zata kammala karatun da take yi." Ƙur Baba Magaji yayi yana kallonshi ya jima baice komai ba yanata jujjuya maganar Gwadabe a kanshi. Yana kuma hango irin gagarumar matsalar da ka iya bullowa. Wanda ada ita ya guda, sai gashi ta kuma biyoshi.
Bayan dogon nazari da Baba Magaji yayi sai yace.
"To Gwadabe naji duk bayaninka. Kuma na gode da nuna sonka da auren Hadiza. Wani hanzari ba gudu ba Gwadabe. Hadiza macace mai ɗan banzan kishi ainun. Kaga kishi? Shi ya hallaka igiyoyin aurenta na baya. Abinda yasa na soka da Hadiza, yarinyace mai biyayya batta da kishi dai. Nayi tunanin kuma ba lallai ka rakito wani auren nan kusa ba, duba da sana'ar taka ma da kake yi har yanzu baka da ido akanta. Kila ko da zaka yi auren sai nan gaba, kila a lokacin Hadiza ta zama babbar mace ka samu sassauci. Kaga mahaifiyarta ko? A lokacin dana auro Asshi sai da muka shafe tsawon shekaru biyu da rabi bata haɗa shinfiɗa dani ba. Kai ƙafarta bata sake taka turakata ba, har sai da santa yaimun lahanin da ya kusan rabani da rayuwata kafin. Gwadabe ina son Fhatsima fiye da yadda kake tunani, kuma ina matukar girmama duk lamarinta. Bata taɓa yin hayaniya ko musu dani ba.
Shawarar da zan baka shine. Kaje ka auri ƙanwar Tamu ɗin, ita kuma Hadiza Allah ya fito mata da wani mijin. Gudun kar zumunci ya taɓu dukkanku ƴaƴanane. Tashi kaje Allah yai maka albarka".
Gwadabe yaso Baba Magaji ya bashi dama yace ko da wani abune. Amman sai ya ki bashi wannan damar haka dole ya tashi ya tafi. Kuma tsakani da Allah Hadiza ta kwanta mishi fiye da yanda ƙanwar Tamu ta kwanta mishi. Dukkansu a cikinsu baiga na ajjiyewa ba, abu suka haɗe mishi goma da ashirin, ga tunanin Iyabo wanda yake ɗamfare a zuchiyarshi babu dare bare rana. Da Hadiza yaci karo a zaure zata fita taci kwalliya da bakar lafaya ta zubo gashinta gaba. Murmushi ta sakar mishi da ganinshi. Shima yai mata murmushin tare da cewa.
"Sai ina da wannan kwalliyar kamar zaki gasar sarauniyar kyau?" Dariya kalaminshi suka bata, sai da ta dara kana tace.
"Sallama akeyi dani a waje Yaya. Bansan ma ko waye ba" Sai yaji nan nake kishi ya lulluɓeshi dan ai Gwadabe gwanine na ƴan kishi mun sani tun a baya. Ƙin magana yayi da yaga tana shirin wuceshi ne yace.
"Ke daga an aiko ana kiranki sai ki fito harda caɓa kwalliya haka? To maza ki koma Baba batai miki bayanin suna son haɗamu aure bane, ko ni dinne bakya so talaka?" A zabure ta ɗago ta kalleshi cikin maɗaukakin mamaki. Shi kuma yai tsai yana karantarta. A madadin yaga damuwa sai yaga akasin hakan. Dan bata san sanda ta kwashe da dariya ba, ta juya ta shige gida da sauri halamar dai itama fa tana ra'ayinshi yayi mata.
Kanshi ya dafe tare da jin haushin kanshi kan furta wannan kalma mai nauyi. Tsoronshi Allah, tsoronshi kar sanadiyyar aurensu zumunci ya taɓu. Dan ƙasan zuchiyarshi gurbin son iyabo ne, tsakiyar zuchiyarshi kuma na ƴaƴanta ne. Ko wacce irin macece zata rayu dashi sai dai ta rayu dashi a saman zuchiyarshi. Yana tsoron rashin adalci, yana tsoron fitinar mata biyu da rabe_raben kan ƴaƴa irin na gidan Baba Magaji. To wacece ta cancanta Gwadabe ya aura a cikin mata biyunnan? Wani shashe na zuchiyarshi yace.
"Ka ba ko wacce daga ciki lokaci ta fayyace maka irin sonta, a ciki sai ka zabi guda, guda kuma ka bata haƙuri. Cikin rashin tunanin abinda hakan ka iya haifarma ɗaya daga cikin matar da za'a ba hakuri Gwadabe yai na'am da shawarar zuchiyarshi ba tare da yayi hangen nesa ba. Wannan shi ake kira nama ya dahu romo ɗanye.
Nan Gwadabe ya raba lokacin shi ta hanyar rabashi a tsakanin Hadiza, da Shafa, Hadiza suna keɓewa suyi zance, yayin da Shafa kuma yake kiran wayarta su sha hira. Yana auna kalaman ko wacce a zuchiyarshi, yana nazari dan gano wacce tafi sonshi da nuna tausayinshi. Tun Baba Magaji bai san Gwadabe na zance da Hadiza ba har mata suka tsegunta mishi. Kuma Baba Fhatsima, da yaya Tasi'u, harma da su Auwala sun aminta da wannan haɗin kuma sun yi farin ciki sosai. Baba Magaji ranar yaso su tattauna da Baba Fhatsima akan batun Hadizan da Gwadabe, kasancewar ranar ita ke da miji.
"Fhatsima naga kamar Hadiza ta amince da soyayyar Gwadabe ko?" Ya jefo mata tambayar yana daga kwance, ita kuma tana kasa a zaune tana dama mishi furar da duk daren duniya sai ya sha kafin ya kwanta.
" Kwarai ko. Nima kuma na daɗa ƙarfafarta naga Gwadabe yana da hankali." Kai Baba Magaji ya gyaɗa yace.
"Hmm Hadiza kenan. To abinda ta guda a gidan uban yaranta shine ya sake biyota. Kishiya ba? Dan abokin Gwadabe Tamu ya riga ni ba Gwadabe ƙaunarshi, kuma ya riga ya karɓa tun kafin yazoshi. Ni da naso dakatar dashi neman Hadiza dan harna sanar dashi dalilin mutuwar aurenta na baya. Amman bamu san me Allah yake son nunawa ba akan hakan, ƙila wata ayar zai saukarma mata masu kaso aurensu sabida kishiya. Allah ya daidaita tsakaninsu" Shiru Baba Fhatsima tayi kawai. Furar da take damawa ta dakatar da damata. Lokaci guda ta jagule. Hakan yai sababin sawa Baba Magaji ya mike zaune ya sakko ƙasa daf da'ita. Yayi ƙasa da muryarshi yace.
"Fhatsima kiyi haƙuri a bisa kalamina. Allah ya sani ba dake nake yi ba, da ita Hadiza nake yi. Amman kiyi haƙuri"
"Hmm Malam kenan. Ashe nuna kishi ga abinda kake so matsalane a wajen maza mu bamu sani ba? Tunda nake kishina a gidannan tsawon shekaru fin talatin ka taɓa kamani ina shirka, ko na taɓa tayar maka da hankali ne?
Ai ko Hadiza batai kishi na hauka a gidan mijinta ba. Allah yayi ƙarewar aurenne dan ku maza in kuka auro wata macen kukan juyama wata baya na wani lokaci kafin ku gama shan romonta. Abunda Hadiza bata da ilimi akai kenan shi yasa aurenta ya mutu a wannan gaɓar. Amman Nagode da wannan furuci naka" Ta ƙarashe maganar tana shessheƙar kuka mikewa tsaye tayi tana shirin barin ɗakin. Malam yayi carab ya cafe hannunta. Tayi sauri ta runtse idanunta tare da fashewa da wani irin kuka mai ɗaci. A wannan daren Baba Magaji ya sha rarrashi da ban baki. Dan har kuɗi ya debo da baisan iyakarshi ba ya bata da safe kafin ta koma ɓarayinta.
A haka soyayyar Gwadabe da ƴan matanshi biyu taci gaba da kasancewa. Ko wacce cikinsu na ƙoƙarin ganin ta nuna bajintarta. Danma ba wacce ta san da zaman ƴar uwarta, iyaye sun bar zancan a tsakaninsu. Domin shi Baba Magaji a ganinshi Gwadabe ai bazai haɗe mata biyu a lokacin guda ya aura ba, dole da ɗaya za'a soma.
Ta ɓangaren neman Gwadabe kuwa, Allah yasanya mishi albarka a harkar neman. Dan yana da ido sosai na ganin zinariya. A zuwanshi har ya samu zinariya sau biyu, kuma ba laifi madaidaita ne. Hakanne ya bashi damar yi ma Babala aike, ita da Bara'u abokinshi na amana.
Da yamma lis yau su Gwadabe suka shigo gidan, sun shawo gajiya sosai. Harda Æ´ar ledar kayan kwalliya a hannun Gwadabe. Æarayinsu suka wuce dai kamar kullum, sai da su kai wanka suka sake kayan jikinsu. Yayi daidai da lokacin Sallah sai suka wuce kofar gida dan gabatar da sallah.
Ta ɓangaren Hadiza kuma tayi kwalliyarta me ƙayatarwa sai ƙamshi take faman zabgawa, ga abinci ta ajjiye da kwanukan zubawa, shigowar su Gwadabe kawai take jira. Baba Fhatsima kuma tana zaune daga gefe tana jin wani shiri da ake gabatarwa a gidan rediyo hankalinta yana wajen shirin. Amman idanunta na kan Hadiza wacce tun ɗazu sai gyare_gyaren gashin kanta data bazoshi ya sauka kafaɗarta take yi. Irin wannan ganɗoki ko a aurenta na fari ma bata yishi ba, duk da shima wancan auren Malam ne ya haɗashi almajirinshi ne mijin.
"Hadiza sai nake ganin kamar kin zafafa soyayyar da kike ma Gwadabe. Kibi a hankali kinsan halin maza da karya ma mace zuchiya. Ƙila ma bake kaɗai bace a ranshi" Ƙur ta zuba mata idanu tana karantar yanayinta, dama ta soko zancanne taji irin amsar da zata bata. Dan tana son auna kishinta da Malam yake ta ikirarin ita ta biyo"
Ƙasa tayi da kanta, lokaci guda sai ta jagule har idanunta ya kawo ruwan hawaye.
"Baba abinda ya faru a baya kuskurene wanda bana mafarkin ya sake faruwa dani a gaba. Nasan an yi mun laifi, amman nima na nuna rashin hakurina ƙarara. Wallahi a lokacin da Tsalha ya dinga nuna mun ni ba cikakkiyar mace bace, sai da yayi amarya ya gane kanshi. Banyi tunanin a daren zan rayu ba, wani abune yake dannemun harshena izuwa moƙoshina. Baba ina da kishi mai yawa, anata cewa wai ke na biyo. Ni kuma in sha Allah zanyi koyi da salon kishinki, da dabarun kissarki ta hanyar gina babban matsayi a zuchiyar Gwadabe. Ta yadda ko mata ɗari zai auro bai isa ya haɗemu a matsayin abu guda ba" Kuka ta fashe dashi mai ciwo.
MRS BUKHARI