← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 210 OF 237

Sashe 210

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai a naka dawa kaga yafi dacewa kaje a babin adalci a cikinsu wacece tafi kyautata maka tafi son abinda kake so?" "Kai tsaye Shafa ce. Hadiza fa dan dole nake zaune da'ita. Jibi jiya ana hira ana dariya sai taɓe bakinta yarinyarnan take yi. Ta ɗauki kishin duniya ta ɗaura akan Iyabo. Ita tana gidan ɗan fulaninta abunta." Bara'u yace. "To a gaskiya ka tafi da Shafa kawai, ni fa amman shawarace. In kuma kana gudun matsala yi ƙuri'a duk abinda suka ɗauka sai ka ɗauki dangane. A babin maslaha kenan wannan. Amman zanso ace Shafa ta ɗauka ko dan albarkacin kawaici da Iyabo da take goyama a bayanta" "Wallahi nima haka. Bara'u ina ma Shafa so mai kyau mai haɗe da mutuntawa da darajawa, ita gani take nafi son Hadiza, a zuchiyata kuma ba haka bane. Wallahi in ranta ya ɓaci sai inji har shakkarta nake ji, kuma fa bawai zata yi mun magana bane. Itace makwafin Iyabo wajen haƙuri. Yarinyarnan Iyabo da take goyo ina jin sonta sosai dannewa kawai nake yi." Bara'u ya kwashe da dariya suka tafa. "Wallahi Gwadabe kai mugun ɗan iska ne. Mata na gidan aurenta ka kasa haƙura da'ita gaka da mata ɗanɗasa_ɗanɗasa itama Shafa naga sai fashewa take yi dan na fahimci kanason ƙatuwar mace mai jiki zaz tsoka. Dariya suka saka harda tafawa. A gidan iyayen Bara'u suka samu suka shiga suka yo wanka sannan suka shiga ɗakin zaure suka sake kaya gidan suna cike da mutane maƙil. Bara'u ne ya kirawo Sakina mai jego tasha kyau. "Ki karama Gwadabe matanshi su sameshi a ɗakin zaure. In abinci yayi a tawo mana dashi." "To amman Bara'u kayan cikin tunkiyarnan yayi kaɗan an soyashi baka ganshi ba, nace ko za'a ƙaro mana naman kasuwane?" "Ni ina naga wani kuɗin Sakina. Kajinnan guda huɗu dake cikin keji kisa a yanka sai ku haɗa ai dai shikenan ko?" "I shikenan zansa Alawiyya ta ƙaro mun biyu ana Ummanmu su zama shida sai a haɗa. Bari in turo maka su. Dama Hadiza taƙi sakewa sai takure kanta takeyi. Ni naga duk ta lalace ta dena gayen ma ta ɗaurama kanta kishi mai tsanani." Harararta Bara'u yayi yace. "Nima ai auren zan sake in sha Allah. Tunda Gwadabe yayi biyu nima kinsan sai nayi" Dariya tayi harda guɗa. "Allah dai ya kawota lafiya. Kaine dai sai mu rabaka biyu ko wacce taja nata. Ni wallahi sai in barma amarya kai kacokan in rungume ƴaƴana." Nan ta wuce Bara'u tayi cikin taron mata. Bara'u na ba Gwadabe labarin diramar da suka yi da Sakina sai dariya suke ƙyaƙyatawa sai ga Shafa ta shigo da tran abinci niƙi_niƙi ta dure, ta sake fita sai gata da ruwa. Iyabo ta miƙa ma Gwadabe yayi maza ya amshe abunshi ya rungumeta. Bara'u daya ɗebi abincinshi sai ya bashi waje. Shafa ta zuba ma Gwadabe abinci ta saka cokali ta ɗebo ta kai bakinshi kenan Hadiza ta shigo riƙe da ɗiyarta. Tana ganin haka ta sake murtuke fuska. Shafa ta sake ciko cokali ta ba Gwadabe. Hadiza ta kai iya wuya dan ko nunawa ba sui sun gane tana ɗakin ba sai wani taɓa shi Shafa take yi, itace harda goge mishi baki. "Ko dai inje ne in kuka gama taɓarar ni sai in dawo." Gwadabe cikin cusa haushi ya kalleta yana zare idanu yace. "Ya ilahi baki ga abinci nake ci ba, ko so kike saina ƙware? Sannan da kika shigo wa kika kula ma? Hadiza ta dubeshi tana mamakin akan Shafa ne yake yi mata haka. Kai kawai ta girgiza ita kuwa Shafa sai ciko cokali take tana bashi ga wata dariyar iskanci da suke ta yi. A fusace ta miƙe har ta sa ƙafarta ɗaya a waje Gwadabe yace. "Kul kika sake kika fita na faɗa miki kenan. Shin ke a komai sai kin nuna rashin haƙurinki ne mtws?" Kamar dai ba zata dawo ba sai dai ta dawo ta zauna. Hannunshi ya dunƙule ya miƙama Hadiza yace. "Zaɓi ɗaya hagu ko dama?" Hannun ta ƙarema kallo ta rasa wanda zata ɗauka. Sai kawai tace. "Shafa ta soma ɗauka" Gwadabe ya miƙa ma Shafa hannun sai tace ta zaɓi dama. Hadiza tace "Na ɗauki hagun" Ware hannayen yayi ya nuna ma ko wacce abinda ta ɗauka. "Ke me kika ciyo Shafa?" Tana dariya tace. "Tafiya naci, wayyo Allah daɗi mijina" Murmushi yayi yaji daɗi sosai da abinda Shafa taci har ga Allah da ita yake son tafiya. Hadiza kuma ƙwafa tayi tana hawaye tace. "Wallahi, wallahi bazan yadda ba. In Qur'ani zaku haɗiye kuna aman ayoyi bazan yadda ba bakinku ɗaya ba. In dai adalcine dani ya dace ace an tafi babu wani ƙuri'a." Murmusawa Gwadabe yayi yana kallonta da mamaki yace. "Hadiza kenan. Ai ko a gidanku malam da ƙuri'a aka san shi. Kuma bai taɓa sauya wadda taci ba. Na lura ke dai bakya son ganin ana zaune lafiya. Ba dan ina jin tsoronki ba zan yi ƙuri'a a takadda ku sake zaɓa duk wacce taci itace kawai." "E na yadda da hakan. Amman wannan kam ban yadda dashi ba ina." Gwadabe ya girgiza kanshi kawai ya nufi wajen akwatin ƙarfen dake ɗakin ya yagi takaddu ya yi rubutu ya dunƙule ya kawo musu. Hadiza sai girgiza take yi tana ciccika tana babbatsewa. "Ke ki soma ɗauka" Cikin fishi ta warci ta gaban Shafa." "Allah ya kyauta" Cewar Shafa. Ai sai Hadiza ta daki ƙirjinta tab tace. "Ya kyauta abunda yafi haka ƴar abu ta kazan...." Gwadabe yasa hannu ya tsinka ma Hadiza mari lafiyayye. Ya dubi Shafa yace. "Yi haƙuri My love, baki ji dai ciwo ba ko?" Murmusawa Shafa kawai tayi. Hadiza kuwa tuni ta shiga taitayinta tana dafe da kuncinta tana ma Gwadabe kallon mamaki. Shi ko sai hura hanci yake yi. "Shafa ɗauki naki. Ko wacce ta faɗi abunda taci" Shafa tasa hannu zata ɗauka kenan Hadiza ta ajjiye wanda ta ɗauka ta warce wanda Shafan zata ɗauka. Gwadabe ya taɓe bakinshi kawai. Shafa tace. "Tafiya na ɗauka" Ai sai Hadiza ta fashe da kuka ta miƙe da ƴarta a hannunta. "Shikenan ka nuna mun matsayina a wajenka. Ka fifita Shafa a kaina. Da ita kake so lallai kayi tafiya. To ni dai sai dai ka sauwaƙe mun wallahi Allah na gama aurenka tunda har ka iya dukana a gaban wannan yarinyar. Ga atampar da mitsiyaciyar matarka ta bamu banso" Ta kwaɗo mai atampar a fuskarshi tab. Idanu ya lumshe yana ambaton Allah dan wallahi ji yake yi kamar yaita dukan Hadiza a ɗakinnan haka yake ji. Shafa ce tayi saurin riƙe hannunta hankalinta a tashe. "Sakemun hannuna dan kutumar.... Ta mulmulo zagi ƙato ta cunkusama Shafa. Cikin wata iriyar tsawa Gwadabe yace. "Ki sake ta ta tafi nace miki kafin in illatata a ɗakinnan dan wallahi zan iya nakasata" Tsawar ta gigitasu dukkansu da sauri Bara'u ya shigo ya tadda su a birkice. Bangazarshi Hadiza tayi ta fice. Sai gata da akwati tazo wucewa Sakina sai magana take yi mata taƙi saurarenta. Haka Bara'u ya bi Hadiza waje shima da sauri. "Ungo yarinyarnan ki shiga gida. Sannan ki soma shirye_shirye umara zamu tafi" Shafa ta buɗe baki zata yi magana Gwadabe ya mata wani kallo. Muƙut ta haɗiye maganarta ta karɓi yarinyarta ta koma ciki. Sakina tace. "Gwadabe a riƙa haƙuri kasan sha'anin mata sai haƙuri. Duk da dai Hadiza kam tana da matsala. Tun dai da aka ambaci Iyabo, tare da gabatar da tsaraba shikenan na kasa gane mata. Ko aikin girki taƙi yi, sai tunane_tunane take yi. Ayi haƙuri amman ko dan gudun lalacewar zumunci. "Babu komai Sakina nagode. Kuci gaba da taronku bari in je in samu Bara'u ' Yasa kai ya fice kiciɓus sukai da Bara'u a ƙofar fita. Hannunshi ya jawo suka nemi ƙarƙashin bishiya suka zauna a kututture. "Tabb yau ni naga kishin mata. Yarinyarnan yi tayi kamar fa zata zageni. Dan idanunta gaskiya sun gama rufewa. Tayi tafiyarta abunta taƙi fur ni kuma ba matata ko ƙanwata ba balle in jawosu da ƙarfin tuwo ba. "Rabu da'ita Bara'u. Gara data tafi dan in ina ganinta zan iya aikata abinda zaku yi mamaki. Kasan menene tun kafin Hadiza ta sani cikin uku zan yima tubkar hanci ai banji a jikina zan iya ci gaba da rayuwa da'ita ba. Gobe sassafe zamu juya muma. "Kai abun ya matuƙar bani mamaki yanzu abinda zamu yi muje masallaci muyi sallah sai mu ci gaba da tattaunawa " A masallacin jikin gidan Zulƙi sukai Sallah Zulƙin ma ya fito tare dashi akayi sallar. A cikin masallacin harda Da'u sai kallon Gwadabe yake yi. Gwadabe ma yana ta kallonshi yadda kuka san bai gane Da'u ba. Sai dai a ƙasan ranshi tausayin Da'u ne danƙare a ranshi ganin yadda ya rame ya fita hayyacinshi. Shi ko Gwadabe yana cikin shiga ta alfarma kallo daya zaka yi mishi ka gane yana cikin kwanciyar hankali. Jikin Da'u a mace ya fita daga Masallacin ya juma a jingine a ƙarƙashin bishiya yanata tunanik ko ya koma su gaisa da Gwadabe ne ya faɗa mishi Babala bata da lafiya? Wata zuchiyarce ta gargaɗeshi da yin hakan yana gudun kar Babala tayi fishi dashi, dama yanzu hakan ma a cikin fishi dasu take tana faɗa musu sun gaza a kan lafiyarta. Tunda dai Yaya Hambali ya ƙwace dukiyarshi daga garesu Babala ta juya musu baya suma matansu da yaransu suka kasance abun kyara kamar Iyabo a da. Gwadabe dai suna zaune har Zulƙi ya salllami jama'a ya dawo wajensu Gwadabe. "Yaya ake ciki ne, wanne hukunci ka yanke Gwadabe munyi waya da maigidana yace in kawo ka" Idanu Gwadabe ya lumshe yace. "Na amince Zulƙi. Amman sai dai haɗuwar ta zama yau in Yana da lokaci matsalace na iyali ya taso gobe nake son in juya" Zulƙi yace wannan babu wani matsala. Bari zuwa bayan magriba ai sai muje mu ganshi ko Bara'u. A tsaida magana ka cike form na jam'iyya shikenan ka zama member. Sai dai fa kaga lokacin ya kusan gabatowa an riga an kaɗa gangar siyasa ba zaka samu lokacin kan ka ba, kaine meeting a Abuja, kaine meeting a cikin Kano haka za'aitayi. Sannan zamu samu malamai da zasu dinga mana adda'a akan lamarin". "Duk babu wata damuwa. Allah dai
Chapter 210 · 0% Book details