← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 237

Sashe 106

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ɗaya yana kaina ko ƙibtawa bayayi. A tsaye yake yayi tsaiwa irinta fulani, irin tsaiwar da suke yi da ƙafa ɗaya, ɗayar ƙafar sai su ɗaurata akan ɗayar. Fararen kaifafan idanunshi sai yawo suke yi a jikina.." "Jabu yaushe kika dawo, ya kika baro jama'ar makka?" Cewar mahaifiyar Yaya Hamma. Shekaran jiya jirginmu ya sauka a Legos, jiya muka shiga Kano Yafendo. "Allah sarki sai kika dawo kika tarar da Adda Daso cikin jinya. Shekararta guda munata fama. Hamma shi yaita jigilar nemo mata magunguna ƙauye_ƙauye bai taɓa gajiyawa ba. Babu abinda zamu ce dashi sai dai muce Allah ya bar zumunci. Cewar Yafendona. Sai naji zuchiyata ta sake nitsewa a so da ƙaunar Yaya Hamma. Wanda zaima mahaifiyarka wannan hidimar ai dole kaji ka soshi. Murmushi nayi nace. Allah sarki. Yaya Hamma Allah ya saka maka da Alkhairi. Allah ya bar mana zumuncinmu. Boɗɗo kema ciwon kika yi ne naga duk kin fice a haiyacinki?" Na tambayeta cikin kulawa. "A'a Adda yanayin canjin rayuwane kawai, da kuma ciwon Dada,. Yaya Amaduyal wannan itace yarmu Adda Jabu" Tana faɗar haka Amaduyal ya rusuna kanshi a ƙasa yai mun sannu da zuwa, sai murnar ganina yake yi. Nima naji daɗi sosai dana sake kasancewa tare da dangina.Yaya Hamma duk wannan maganar da akeyi baiyi ko tari ba, sai ido kawai da yaketa binmu dashi. Likitan daya shiga duba Dada ne ya fito. "Mutum biyu daga cikin Yaran Daso su biyoni a baya" Yafendo sai ta nuna ni, ni da Yaya Hamma muka bishi zuwa ofishinshi, ya bamu wajen zama. "Tun yaushe baiwar Allah'nnan take cikin wannan halin kuka barta a gida saida ciwo ya cinye jikinta sannan zaku kawo mana ita? Tazo ta mutu a hsnnunmu ku ɗaura alhakin kisan a kanmu" Yaya Hamma ne yace. "Dakta ciwon zata kai shekara ɗaya da rabi haka tana yi. Amman a tsaitsaye da yin tsananinshi baifi watanni shidda ba. Sai an ɗagata sai an kwantar da'ita. Munyi magunguna gargajiya da yawa ba haka muka zauna ba" Wannan Dakta ya zare tabarau ɗinshi daga idanunshi. Ni kaina jin tsayin lokacin da Dada ta ɗauka tana jinya ya ɗagamun hankali, tausayinta ya sake ɗarsuwa a zuchiyata ai saina fashe da kuka ina salati a hankali. "Jabu kiyi shiru, kuyi haƙuri in sha Allah Dada zata tashi. Ƙarshen wahalarta a gidan Baffa yazo tunda ya rabu da'ita. Dani dake zamu iya riƙe Dada mu bata farin ciki. Dakta a faɗa mana abinda yake damunta." "To abinda yake damunta suna da yawa. Na farko shine hawan jini, dan jininta ya hau sosai, babban abinda yake damunta cutar Rawaya ce, sabida tsananta da yayi ya haifar mata da ƙurajen a hanjinta, ma'ana yaci hanjinta sosai da sosai. Dole tana buƙatar ai mata aiki ciwo kun bari yaci jikinta ainun. Akwai buƙatar ai mata ƙarin ruwa, babu ruwa babu jini sosai a jikinta. Kunyi sake da yawa, Mama na da tsawon rai ne shi yasa har Allah yasa ta kawo yanzu da ranta." Ni dai hawaye kawai nake zubarwa na tsantsar tausayin Dadana. Allah sarki baiwar Allah damo sarkin haƙuri kenan. Yaya Hamma yace. "To Dakta wanzu me ake buƙata daga ɓangarenmu?" "Akwai buƙatar kuɗi, sannan akwai buƙatar ku bata jini a ƙara mata. Da zaran mun gama duk gwaje_gwajen daya dace in sha Allah zamu sanar daku lokacin da za'ayi mata aikin. Bazai wuce jibi ba Ku dai ku tanaɗi kuɗi." Kai Yaya Hamma ya dafe da hannunshi. "To Shikenan, a bata jinina a saka mata Dakta" Dariya Dakta yayi yace. "Za'ku je lap dai a tabbatar da ingancin jinin, in yayi daidai da nata sai a ɗiba. Amman sai dai kuje ku biyu ko uku, dan leda shidda muke buƙata na jini." Tare muka fito, Yaya Hamma ya kirayi su Amaduyal suka wuce lap domin a aunasu. Ni kuma a sanyaye naima su Yafendo bayanin halin da Dada take ciki. Yafendo ina ganin ko zaku tafi gida, ni da Boɗɗo saimu dinga kwana da'ita. Asibitin akwai sanyi zai iya damunku, kuma gida Babu kowa." Kafin suce wani abun saiga Baffa Musa da Yafendo A'i hankulansu duk a tashe. "A'i am kina fama da kanki ai da kin turo Jumare yazo ke ki huta a gida. Ga dare harya rufa" Cewar Yafendo Kaɓoji. Hawaye Yafendo A'i ta share da mayafinta. "Zuchiyata ba zata samu nitsuwa ba. Yadda labarin yazo mun. Su Cubu na gidan Yaya Musa Mai Nagge ya korosu suma bayan tafiyarku. Hakan bai mishi ba ya samu Yaya Musa yake faɗa mishi wai Jabu zata gani duk abinda ya faru da'ita shine. Sannan ga yara mu mu riƙe tunda mun nuna mun fishi iko. Abun dai babu daɗi sam" Baffa Musa yace. "Ku ajjiye wannan maganar a gefe. Ke Jabu yaya jikin ita Dason?" Yafendona tace. "To jikin nata sai adda'a Yaya" Ta labarta musu abinda Dakta yace. Baffa Musa sai ya buɗe baki yana maganar su ba za'aima Dada aikiba mutuwa akeyi a asibiti, su kaza su kaza. Kuma su Yafendo suka goyu bayanshi akan hakan tare da yanke hukuncin zasu mayar da Dada gida ayi mata na Hausa. Ai saina fashe da kuka na zube ƙasa. Baffa am dan Allah kuyi mana rai Dada tana buƙatar jini da ruwa. Tana buƙatar kulawar asibiti tunda ance babu irin na hausan da ba'ayiba. Ku bari mu jarraba na asibitin" Ganina a ƙasa yasa Boɗɗo itama ta tsugunna muka ci gaba da basu haƙuri. Kundai san halin iyayen namu Fulani da taurin kai, da kuma ƙauyanci. Baffa Musa sam yaƙi yarda gashi shine mai faɗe aji a dangi kasancewarshi babba. Ni dai na koma saman kujera sai kuka nake yi Yafendo A'i tana rarrashina. A haka su Yuguda suka zo suka samemu. "Daga ina kuke Yuguda?" Buɗar bakinshi yace. "Wata likitace wai zata kwashi jinina ni na taɓa jin yadda akayi haka Baffa? Yaya Hamma yana kwance tana zuƙe mai jini wai za'a sama Dada, Amaduyal ma Yaya Hamma yace dole sai ta zuƙi nashi. Ni gaskiya bazan iyaba." Banga laifin Yuguda ba, rashin ilimi da rashin wayewa ke damunsu. "Jabu kinga duk abinda zuwa asibitinnan ya jawo ko? Mu fa a kan zuriyarmu babu wanda waɗannan mayun suka taɓa mana. Bama zuwa asibiti mu. Yuguda mu je ka kaini ɗakin shan jinin maza." Da sauri na riƙe babbar rigar Baffa. Dan Allah Baffa ka tsaya kaji. In ba'a sama Dada jininnan ba mutuwa zata yi" Sai yayi dariya yace. "Yarinya muna da maganin ƙarin jini namu na gargajiya da muke sha tun iyaye da kakanni. Daso ba za'a ƙara mata jinin maita ba." Muna cikin wannan badaƙalar wannan Dakta dake lura da Dada yazo zai wuce yaji abinda muke tattaunawa dake mutumin kirki ne kuma shima bafulataninne sai ya gaiyacemu ofishinshi. "Baffa Musa kamar yadda naji yara na kiranka ko, nasan ba lalle ka ganeni ba. Ubale ne ƙanin Ilyasu gare_gare." Da jin haka Baffa yace. "Ilyasu gare_gare abokinmu da yake ɗaya daga cikin mutanen da turawa suka ɗiba zuwa ƙasar waje dan suyi boko" Dakta yayi dariya. "Shifa Baffa Musa. To ni ƙaramin ƙaninsune wannan wanda kuke kora in zaku dandali. Wannan wanda bayan kaci shaɗin aure yake rakaka zance" Ajjiyar zuchiya na sauke jin abinda Dakta yake ce da Baffa Musa. Nasan ko babu komai zai iya shawo hankalinshi ya bar Dada a asibiti a nema mata lafiya. "Hahaha Ubale baka da mantuwa gaskiya. Yanzu shi Ilyasu gare_gare yana inane?" "Yana ingila da iyalanshi acan yake aiki shekara ashirin da biyar kenan." Baffa yace. "Allah sarki. Kai ka tura yara wai aje a tsotse jininsu Ubale? Marar lafiyar fa Daso ce ƙanwata kafa santa. Kaga ga A'i, ga Kaɓoji, ga Jabu. Waɗannan biyun yaran Dason ne, wannan kuma yaron kaɓojine." Nan Dakta ya dinga yima Baffa Musa bayani cikin hikima da dabaru irinna masu gogewa. Da ƙyar da suɗin goshi Baffa Musa ya amince yace a bar Dada a asibitin. Ajjiyar zuchiya na sauke mai ƙarfi. "To Alhamdulillah Baffa Musa, in sha Allah ba za kuyi dana sanin zuwa asibiti da'ita ba. Amman ku zaku koma gida mutum biyu sai su zauna da'ita a cikin ɗakin. So samu da namiji ɗaya ko za'a buƙaci wani abun." Baffa yace. "To Shikenan Jabu da Boɗɗo tunda sune masu jini a jika sai su zauna. Hamma ya zauna dasu ɗan baɗo dan na lura kamar ƴar gida za'ayi da Jabu" Sauke kaina nayi da sauri ina ɗan murmushi. Da haka muka fito a ƙofar ward ɗin su Dada muka ga su Hamma suna zaune a benci. Tare duk muka ɗunguma ciki, Dada na kwance ana mata ƙarin ruwa. Fuskarta tayi fayau. A gurguje suka dubata su kai mana sallama. Yafendo a tawo mana da bargo da taburma gobe in za'a kawo mana abincin safe. Akwatin kayana yana wajen Hari ki karɓa. Dafa kafaɗata tayi tace. "Allah yayi muku albarka, Allah ya baku ladan jinya. Gobe Daso zata tawo muku dashi, ita zata yo abinci daga gidanta ta kawo muku. Boɗɗo ki kunto goyon yarinyarnan asibitinnan da akwai sanyi kuji da kanku. Ita yarinyar tasha nonon shanu tunda akwai masu shayarwa." Boɗɗo ta sunto ƴarta Baban ƴar ya amshe abinshi. Yaya Hamma yace. "Jabu ku kula da Dada bari in kaisu Baffa tasha. Daga nan zan tawo muku da abinci" A dawo lafiya mu ka yi mishi. A lokacin ƙarfe kusan takwas na dare. Banyi la'asarba ga magriba da isha, ni sai yanzu na tuna. Boɗɗo bari inje in nemi wajan alwala, ke ki zauna inna dawo sai kije kema kiyi." Fita nayi da tambaya da kwatance na je wajen yin alwala da kama ruwa. A wata katuwar rumfa na hango mata suna sallah nima na shige cikinsu na rama sallolin da ake bina. Na jima sosai ina kai kukana ga Allah, tare da neman tsari a wajen Allah game da furucin Baffa a kaina na dukkan abinda ya sameni shine. Gaisawa nayi da matan dake cikin rumfar. Wata bafulatana tace. "Ai ɗakinmu ɗaya gadonmu na kusa da naku. Marar lafiyar mahaifiyarku ce?" Na dubi matar a girme kamar ba zata girme mun ba. Nace da'ita. Allah sarki, mahaifiyarmu ce" "Allah ya bata lafiya. Nima mahaifiyata nake jinya mun kai tsawon wata uku a asibitinnan muna jinyarta. Kinsan yanayin jikin tsufa, ya haɗu da ciwo" Kai na gyaɗa
Chapter 106 · 0% Book details