Sashe 17
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ishasshe a kai mata. Amman ko da aka kai sai dawo dashi Uwani tayi Babala tace bata cin abincin Yarbawa, da akayi tuwon dare ma na kuma sa Uwani ta kai mata, amman bata karɓa ba. Har magriba babu Gwadabe ba dalilinshi sai wajajen taran dare muna zaune dani da Sakina da Uwani suka shigo shi da Bara'u da ƴar baƙar ledarsu a hannu. Idanu ya zuba mun tare da lumshe su. Na fahimci akwai gajiya da tarin damuwa dake damun Gwadabe. Ko wanne halin zai shiga in na barshi oho, nasan Gwadabe yana sona so mai tsanini, duk da na fishi zurfi a soyayyar da nake yi mishi, jin Gwadabe nake tamkar shine mahaɗin numfashin da nake yi dan in rayu. Amman dole in fita daga rayuwarshi shima ya samu ya nutsa. "Ayi mun afuwa uwar biyu. Abubbuwanne su ka haɗu suka caɓe mun. Mun fita da Bara'u fafutukar yanda za'a samu na abincin suna da abun haƙiƙa a fita kunyar ƴan uwa." Murmushi nayi mishi nace. Babu komai, sannunku da dawowa ina wuninku?" A tare suka amsa duk aka gaggaisa baki ɗaya. Sakina ta tafi kawo musu tuwo. "Tamu ya kirani da magriba madam ɗinshi tana son tayi miki barka, yace ma ana gobe suna zata zo. Bari in kira ku gaisa" Kiran layin Tamu yayi bayan ya ɗaga wayar sai ya miƙo mun muka gaisa tare da yi mun barka. Daga ƙarshe ya haɗa ni da Ayashe itama tayi mun barka tare da faɗin. "Kayan fitar sunan ƴan biyu dana Maman ƴan biyu yana wuyana in sha Allah. Ana gobe suna zan tawo in zo ayi komai dani." Dariya nayi nace. Muna godiya Ayashe Allah dai ya bar so da ƙauna, mun gode ƙwarai" Mu kai sallama na miƙa ma Gwadabe, nan Tamu yake sanar mishi ya ɗauki nauyin rago ɗaya. Mun yi farin ciki matuƙa gaya. Sun jima a falo muna hirarmu gwanin ban sha'awa daga ƙarshe su kai mana sallama, suna fita muma muka tafi kwanciya. Haka dai ranaku sukaita tafiya, duk da kauce ma rikici da dangina suke yi sai da akayi rikici a tsakanin Anty Mulka da Yaya Haula. Wai an jiƙa tsakar gida da ruwan wanki, shine fa Yaya Haula tai ta zage_zage tun su Anty Mulka basu tanka ba har suka tanka. Akaita gwabza rikici har sai da manyan unguwa suka shigo akaita basu baki tukunna. Ni dai ranar naci kuka sosai sabida Babala har ɗaki ta shigo ta ƙaremun tanadi tas. Har ta gama babu wanda ya tanka mata, sai da tayi mai isarta ta fita. Ana gobe suna da yamma sai ga su Gwadabe da raguna tiƙa _tiƙa guda biyu sun ɗaure, da kayan cefanen suna niƙi_niƙi. Daf magriba Ayashe ta ƙaraso da yaranta biyu. Gaskiya ta gwangwajeni da ƴan biyu sosai. Shadda ta ɗinka mun taji aiki sosai, harda mayafi da takalm. Taiwo kuma bulawus mai tsada ta siyo mata irin mai takalmi da abun kai na yara, Kahinde kuma riga da wandon jins ta kawo mishi. Godiya na dinga yi mata. A ranar Bose, da Kauliya, da Anty Mulka a nan suka kwana. Washe gari asubar fari aka shiga aikin abinci. Da asubar Burodami Debisi ya kawo mana nama cikin leda mai zane, Burodami kokodeen kuma ya turo masu rumfa suka kafa runfuna biyu da kujeru. Yasa yara suka shigo da koka kola kireti huɗu. Ƴan uwa masu daɗi, ƴan uwa abun wuya wannan ya kawo nashi wannan ya kawo nashi sai kaga ashiri ya rufu ruf, a gaskiya ba yabon kaiba muna da hadin kai sosai. A ƙofar gida suka kafa murhun girki, masu Amala nayi, masu yin jallof nayi, ga nama jingin anata yankawa ana soyawa, wasu suna gyaran kayan miya. Tun asussuba ni da ƴan biyu muka yi wanka, ina ɗaki a zaune Bose tanai mun kwalliya ta kece raini. Ba yabon kai ba mu yarbawa mun iya kwalliya da sanin darajar kaya masu tsada. Domin mazan yarenmu basu san siyama mace ƙaramin zani ba, ko ashobi zamu fitar muna zaɓar mai tsada mu fitar. Domin matan yarbawa har adashe akeyi na musamman domin kece raini, ko wacce mace tana son asan mijinta na kulawa da'ita. Ko ni duk talaucinmu tun cikina na wata ɗaya nake zubin dashi a shagon Iyaa Beji me shagon atampa da lace ta bakin layinmu. Da kaɗan_kaɗan na tara kuɗin les ɗaya, sai naci gaba da tarawa, in ƴan uwana sun kawo mun ziyara sun ban kuɗi a ciki zan zari wani abu in zuba dashi, da haka na sake tara kuɗin leshi na karɓi lace biyu iri ɗaya na bayar da ɗinkin nawa a wajen Yemi, na gwadabe da Toye na bayar a shagon ɗinkin maza. Lace ɗinne a jikina tun sassafe nasa aka miƙama Gwadabe nashi shi da Toye dan tare suke kwana a ɗakin zaure. Sarƙa Bose ta saka mun a wuyana. "Wannan karon mai gidanki yayi ƙoƙari ba kamar lokacin haihuwar Toye ba. wannan lace ɗin da sarƙar babu laifi ba sui arha da yawa ba, ba sui tsada can can ba. Ga raguna manya_manya" Harara na doka mata, ta kwashe da Dariya ta doki kafaɗata. Dole nima na murmusa, dan Bose a lokacin da nake cikin matsi a gida sakamakon soyayya da Gwadabe, a wajenta kawai nake samun sauki. Yaya Haula ce ta shigo ɗakin da sallama tana wani gatsine, ta sha kwalliyarta da wata shadda mai maiƙo tayi kyau sosai, dan Baban Nazifi yana ƙoƙarin sosai a kan iyalanshi, bama su kaɗai ba harda iyalan ƙannenshi. Turus tayi data ganni na fito shar dani kamar ba ni ba, ba wata kwalliya bace a fuskar tawa ba, hoda ce sai jan baki, sai kwalli da Bose ta ziraramun, ko ja gira banyi ba sakamakon akwai gashi sosai a girata. Ɗan kunne da sarƙar da Ayashe ta tawo mun da'ita ta ba da gudunmawa sosai wajen ƙawata kwalliyar tawa, sannan dinkin buba ɗinkine dake fito da kyawun ko wacce irin mace, musamman masu jiki duma_duma irinmu, kwalliya da ado na fito da masu ƙiba ainun. "Iyabo gashi kayan yarinya na ɓangaren dangin miji." Ta dangwararmun da leda mai zane_zane. Kafin in yo godiya ta ƙara watso mun mugun kallo tace. "Na ga anata aiki babu wacce ta buƙaci ganinmu a wajen. Amman ki sani duk tsiya dangin uba sun fi power fiye da dangin uwa. Amman ke kinfi son duk abunki ƴan uwanki su tsaya a wajen, dan ku aikinku kenan ƙabilanci, tunda kika haihu ake yare a gidannan dan masifa." Murmushi nayi dan har ga Allah bana son cusa ma zuchiyata baƙin ciki a irin wannan rana mai albarka. Ai bansan basu neme ku ba Yaya Haula tunda ni bana wajen." Jijjiga kai tayi tace "Ai ba zaki sani ba tunda dai Gwadabe shi ya baki ƙofar raina danginshi. Babala tana gidannan a kasa zuwa a kiramu mu kama aiki a matsayinmu na dangin miji, ai shikenan hausawa na cewa sai bango ya tsage ƙadangare ke samun mafaka." Tana gama faɗar haka ta fice fuu kamar kububuwa. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke na jawo ledar data dire mun. Riga ce ƴar ɗari uku uku guda biyu ta mace da na namiji, sai sabulu sanda biyu da omo mudu ɗaya shikenan abinda ke ciki. Bose ta riƙe baki tace. "Wannan kayan shine kayan dangin miji ke da kika haifa musu ƴan biyu? Lallai Anty Iyabo dangin mijinki basa ƙaunarki.. Ya isheni Bose ki barni in ji da abinda ke damuna dan Allah." Ina faɗar haka na miƙe zuwa uwar ɗaki, na tarar da Ayashe tana shirya Taiwo da Kahinde sun fito sun yi kyau sosai. Dubana tayi tana dariya tace. "Kai masha Allah mai jego kin fito shar dake kamar ba ke ba." Dariya mu ka yi dukkanmu. Simbi ce ta shigo niƙi_niƙi da buhu ta dire a gabana, Sai ga Taufiq shi da Lekan suma sun shigo da ghana most go. Yaran Burodami kokodeen ne Taufiq, Lekan kuma yaron Iyaa Kokodeen ne, Simbi shekararta goma sha takwas haka, wannan shekarar ta game sakandare ɗinta. Taufiq kuma yarone shekararshi sha biyu, yana jss 2. Lekan kuwa saurayine Buhun sobeniya ne na robobi, da kofuna, mafificin roba, moɗa da sauran kayayyakin roba mai manne da sikitar dake ɗauke da sunan Taiwo da Kahinde. Wanda ya ɗauki nauyin yi naga an rubuta Burodami Debisi Adebayo. Ghana most go ɗin kuma shaƙe take dam da kayan jinjiraye da atampopi , omo, sabulu da su nabkin. Hawayene ya gangaro a kumatuna mahaifiyata na tuno tana can ƙungurmin daji, babu waata hanyar da za'a iya sanar mata na haihu balle itama tazo ayi komai a gabanta. Duk da bani da maraicin uwa sam balle uba, Iyaa Debisi itace makwafin uwa a gareni, Burodami Debisi kuma shi ya zame mun makwafin uba. Shi yaita ɗawainiya da rayuwata har tasowata yanzu ma da nake gidan mijina bai fasa turo mun abun alkhairi ba, kuma yana kawo mun ziyara lokaci zuwa lokaci, duk da matarshi na tsananin tsantsar kishin kulawar da mijinta yake bani, sabida alaƙar data tafa gibtawa a tsakaninmu na soyayyar da Allah bai nufi shine uban ƴaƴana ba. Kafin ƙarfe takwas na safe tuni an gama girki tsab an zuzzuba a kuloli, An yanka raguna harma an gyara kayan ciki, kayan cikin dabba ɗaya nace a miƙa ma su Babala su soya da kansu kar suce an musu coge. Abinci ma ni da kaina na tsaya saida aka basu duk abinda ya dace, har sobeniyarsu nasa an cire musu Anty Mulka da Uwani suka kai musu har ɗakin Yaya Haula. Takwas da rabi Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya iso, ƙofar gida, zuwa lokacin ƴan uwa maza da mata duk suna waje a cikin rumfa a zazzaune. Gwadabe ne ya ratso cikin mata yana saye da leshi da hular ashoke, Kahinde ya riƙe Ni kuma ina riƙe da Taiwo, Ayashe da Sakina ne suka mara mana baya har zuwa ƙogar gida inda Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya soma wa'azi. A gabanshi muka gurfana, ya soma ragargazo ma ƴan biyu adda'a tare da roƙa musu alkhairan duniya dana lahira, tare da samun nasara gami da rayuwa mai tsayi, mai albarka. Duk wannan cikin yaren yarbanci yake yi, yanayi da waƙa dukkanmu muna amsawa da. Ameen" Muma cikin salon rerawa kamar masu waƙa. Yaran muka