← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 237

Sashe 56

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iyabo Motarmu na dira a tsaha idanuna su kai tozali da kyakkyawar fuskar Yaya Hamma. Yana jingine a jikin wata Bus ya ƙurama motarmu idanu bai ƙibtaba, bai kawar da kanshi daidai da na sakan guda ba, har sai da yaga na fito a cikin motar. Da sauri ya nufoni fuskarshi ɗauke da yalwataccen murmushi, murnarshi ta kasa ɓuya. Yasa hannu ya karɓi ledar kayana. "Jabu tunda na shigo tasharnan zuchiyata bata dena dokawa ba har sai da na ga sakkowarki a cikin motarnan. Wata zuchiyarma ce mun take yi baza ki dawo garemu ba kwata_kwata" Ɗan murmusawa nayi kawai nace. Yaya Hamma kenan, na gode da kulawa, amman kafin ma in tafi na sanar maka zan dawo." A jere muka fito daga cikin tashar, a bakin titi muka samu motar Girai muka shiga, wata kwaraɓaɓɓiyar Bus mara gudu muka samu. Bayan tafiyarmu ta ɗan yi nisa sai nace dashi. Ni ko ya jikin Dada Yaya Hamma?" Wannan tambaya tawa farad ɗaya saita sauya fuskarshi, daga farin ciki izuwa ɗaurewar fuska, harma da alhini. Lamarin daya dagula jinin jikina kenan, ruɗewar da nayi da yawa ne yasa yace dani. "Ki kwantar da hankalinki Jabu. Bawa baya iya tsara ma kanshi yadda zai rayu. Nayi imani da hakan na faruwa Al'umma babu mai zubar da hawaye. Bayan tafiyarki abubbuwa manya sun faffaru marasa daɗin labari. Amman bazan baki labarin komai a cikin motar haya ba. Kiyi haƙuri in mun je gida zaki ji komai" Bai daina rarrashina ba har muka iso Girai. Ni dai ko da muka shiga akori kura bana iya ko magana sai fargaba da nake cikinta. Jikina sai bani yake yi Dada ta haɗiyi zuchiya ta mutu ne ƙila bayan tafiyata, ko kuma maƙetacin mijinta ya kasheta. Da waɗannan tunane_tunanen muka shiga cikin Jaɓɓi lamba. Sai gamuwa da mata masu tallar nono muke yi Yaya Hamma gidan su Dada zaka kaini, zan tsaya a ƙofar gida sai kai ka shiga" Ƙuramun idanu yayi, sai naji idanun nashi sun yi mun kaifi ba shiri nayi ƙasa da nawa idon, tare da sauraren amsar da zai bani. "Dada bata gidanta, tana gidan Baffa Musa, ki bini kawai in kai ki" Ai jin haka yasa na kuma tsurewa har hawaye sai da ya zubo a idona. Tafiya muke babu mai cewa da ɗan uwansa ci kanka har muka isa gidan Baffa Musa, tafiyar ƙafa ce mai mugun nisan gaske. A ƙofar shiga gidan naci karo da Burodami Debisi shi da Jatau. Sai nayi turus ina dubanshi cike da maɗaukakin mamaki. Shi kuma cikin sanyi yake kallona irin kallon da naso in samu irinshi daga gareshi a shekarun da suka shuɗe, shekarun da wutar sonshi ta kusan ƙone mun rayuwata. Sai a yanzu da bana buƙatar kowa a cikin rayuwata ne, zai dinga jifana da irin wannan kallon? Ko zan iya ba maza wata damar, babu Burodami Debisi a cikinsu, zaifi mutumci ya riƙe matsayinshi na wa gareni "Iyabu Ekabo ( Sannu da Zuwa) Burodami Debisi yaushe a gari?" Na tambayeshi da yaren hausa, babu yabo babu fallasa a fuskata. Jatau yace. "Ai tun ranar da kika yi tafiya shima ranar yazo. Tare muke ta zuwa kiwon shanu" Da mamaki na dubeshi, kuma na yaba ƙoƙarinshi daya iya har kwana biyu a ƙauyenmu. "Mu je ciki Jabu, ki ga halin da Dada take ciki, naga kamar kin sha'afa" Cewar Yaya Hamma da muryarshi a kausashe har ɗan rawa take. Wucewa nayi cikin gidan, Yaya Hamma na biye dani a baya, su Burodami Debisi na biye dashi har zuwa cikin bukkar Goggo matar Baffa Musa. A kwance na tarar da Dada kanta naɗe da bandeji, sai kuma hannun damanta dana ga an ƙulle da tsumma, ga kara an jera mata kamar mai karaya. Sai numfarfashi take fitarwa, Boɗɗo na gefenta a zaune, su Yusufu, da Cubu duk suna kewaye da'ita, harda yaran Baffa Musa waɗanda suke gidan miji, Yafendonmu Jabu, da Yafendo kaɓoji mahaifiyar su Yaya Hamma, da Yafendo A'i suna wajen duka. Kuka kawai na fashe dashi domin na rasa ma abinda zance, bansan wa zan tambaya ya bani amsa ba, kowa a cikin damuwa yake. Boɗɗo ce ta dawo kusa daf dani ta riƙe hannayena biyu. Meke faruwa da Dada Boɗɗo, naga hannunta kamar karayace ma?" Baffa Musa ne yace. "Abinda ya faru kusan sanadiyyarki ne Jabu. Wannan ƙiyayyar da mijin Daso yake yi miki abune daɗaɗɗe sosai. Kuskuren da ita Daso tayi shine data yarda da sharaɗinshi kafin ya aureta. A lokacin da mahaifinmu Allah ya jiƙan rai ya matsa ma da Daso kan a cikin gwarazan samarin da suke neman aurenta za'a saka shaɗi, a lokacin shaɗi gwarazan mazan fulani suke yi su auri mace, dole sai namiji ya nuna jarumtarshi. Aka saka ranar shaɗi, Allah cikin ikonshi sai mai nagge yai nasarar cinye wannan gasa ta neman auren Daso. Gashi matashi mai dukiya, dan Allah ya albarkaceshi da tarin shanu a lokacin. Amman mutumne shi mai zuchiya da kafiya akan ra'ayinshi ko mai muninshi. Duk da wannan kusan ɗabi'ace dake gudana a jinin ko wanne bafulatani, amman na mai nagge yayi yawa. Bayan anyi aure kafin ta tare sai yake sanar mata shi mutumne mai tsananin kishi shi baya son ya saka ɗiyarta ƴar margayi a idanunshi sam, ta yi mai alƙawarin zata kiyaye mishi hakan, amman bazai hanata zuwa ganinki ba, bai kuma yarda yaranshi suyi zumunci dake ba. Ita kuma Daso cikin rashin sanin girman furucinshi sai ta amince mishi da duk abinda ya gindaya. Duk da dai ba'a musu dashi. Jabu daga ranar da yar mahaifnki Toyosi ta ɗakkoki ta kawoki garinnan dan kiga dangin mahaifiyarki, bayan tafiyarku sai da igiyar auren Daso ya kutsure, ta fuskanci tashin hankali, da faɗa sosai harda duka ma a wajen mai Nagge kafin ya korota gida. To shekaran jiya kinje mishi gida, a gabanku ke da Daso ya fashe mata kai. Bayan ya rakaku da gudu sai ya rufeta da duka. Ana cikin wannan hali ranar ko tallar Nono ta kasa zuwa. Sai ga Debisi shima da yamma lis. Zuwanshi ne yai silar da kika ga Daso a kwance tana jinya. Hamma gashi shi yaita kai kawo akan nema mata lafiyarta. Debisi kuma da Jatau suka kaita asibitin Girai aka duba lafiyarta. Wai hawan jinine ma da'ita a yanda su suka ce. Kinji abunda ya faru, amman kuyi hakuri wata rana fa sai labari, masu ba da labarin ma wata rana basu. Haka zamu shuɗe kamar yadda magabatanmu suka shuɗe. Kuka mai taɓa zuchiya na fashe dashi kawai. Wannan zalunci da mai yayi kama, yama za'ayo a raba uwa da ɗiyarta ɗiyar ma ta fari marainiya bugu da ƙari. Tsit ɗakinnan yayi bakwa jin komai sai sautin kukanmu ni da ƙannena da suka kewayeni suna rarrashina. "Jabu ki dena wannan kukan. Ki yafe mini kinji? Yarintace tasa bansan girman sharaɗin da mai nagge ya gindayamun ba, ba dan bana sonki bane na amince mishi ba. A cikin yarana kab nafi jinki fiye da kowa, kasancewarki marainiyar yarinyar da bata taso a gaban mahaifanta ba. Bugu da ƙari soyayyar Toye kanki ta koma kacokam." Hannunta nayi carab na kama, idanu ta lumshe wasu hawayen nadama suka gangaro mata. Mayafina nasa na goge mata. Baffa Musa ne yace. "Daso baki da lafiya bai kamata ki yawaita magana ba. Hutu kike buƙata. Na faɗa ma Jabu wannan labarinne domun tasan abinda ke gudana, ba dan in tashi hankalinki ba. Kai kuma Debisi duk sanda zaka zo wajen Jabu, ka sameta a gidan Yafendonta, ka sanarma Toyosi itama. Jabu ku tashi ku koma can gidan Yafendonku, ki samu ki huta" Ba haka naso ba, so nayi su barni in yi ma Dada jinya. Amman Baffa Musa yaƙi fur sai cewa yayi ma dinga zuwa dubata, matanshi zasu kula da'ita. Muna tafe a hanya amman tunani ya cika kaina, damuwa tayi ma zuchiyata yawa, ina neman wanda zan kwanta a kafaɗarshi in ci kuka ko zan samu salama. Gwadabe ne ya faɗo mun, tunashi kawai da nayi wallahi sai na tsinci kaina ina murmushi kawai. Tare duka muka shiga gida. Ni da su Daso wacce tunda na dawo naga ta fita sha'anina. bukkarmu muka shiga, na nemi waje na zauna jigum. Yaya Hamma ne ya shigo hannunshi riƙe da kayana. Yana shigowa sai naji Daso ta sau siririn tsakin da ba kowa ne zai ji ba. "Ga kayanki Jabu. Ku kuma ku bamu waje zan yi Magana da Jabu" Su Cubu duk suka miƙe suka fita, banda Daso wacce kwanciya take shirin yi. Sai da ya yareta kuma da faɗa naga yana magana. Kuka kawai naga Daso ta fashe dashi ta fice fuu. Ni dai ba ta fishin Daso ma nake ba, ta kaina nake yi. Zama yayi a ƙasa yana fuskantata. Idanu ya zubamun yaƙi cewa dani komai, yaƙi kuma ya dena kallona. Ni kuma duk sai na tsargu. Jatau ne ya leƙo. "Jabu ki zo Debisi yana son zaku yi Magana, yana gindin bishiya, ki je da tabarma, ga fura Hari ta dama sai ki tafi mishi dashi" To" kawai na iya cewa, ya saki asabarin yayi tafiyarshi. Yaya Hamma kuma naga yayi ƙasa da kanshi kawai yana wasa da layar dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi" Yaya Hamma bari in je in dawo, tunda naga kamar baka son yin maganar da kace zamu yi" Ɗagowar da zaiyi sai naga idanunshi sun rine, jijiyoyin fuskarshi sun yi burɗun_burɗun. Gabana ya yanke ya faɗi ganin yanda cikin ƙanƙanin lokaci na ganshi a cikin wani irin yanayi. Cikin kaurin murya mai cike da karaya yace. "Shikenan gobe zan dawo, nima zanje gida in kwanta jiri nake ji" Haka kurum sai banji daɗin ganin shi a sabon kamanni ba. Kafin in gama tubkewa ya fice bankai ga warwarewa ba. Jikina a mace na fito tsakar gidan. Tabarma da damammiya fura Hari ta miƙo mun nasa hannu na karɓa. Har na kai ƙofar fita na juyo na kalli Boɗɗo nace. Boɗɗo ku jirani in je in dawo. Inaso zamu je gidanki akwai muhimmiyar maganar da nake son mu tauna" Ina faɗan haka sai naga Daso ta zare idanunta, firgici ya bayyana karara a fuskarta" Ficewa nayi waje. A tsaye a gindin bishiya na hango Debisi yana kallon garken shanun da suke wucewa. Kurama juna idanu muka
Chapter 56 · 0% Book details