← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 237

Sashe 10

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙur yai mun da idanunshi wanda suka kaɗa su kai jawur. "Toye Wa Nibi ( zo nan)" Da gudu Toye ya je wajenshi. Murmushi yayi mishi yace. "L'o pade Anty re ( Je ka samu Antynka) Ya turashi zuwa falo. Yana fita Gwadabe ya mai da ƙofar ya rufe. A gabana ya tsugunna. "Ifemi (masoyiyata) me kike shirin yi, ɗakin ki kike son bari, Gwadaben naki kike son gujema? Duk irin juriya da gwagwarmayar da muka sha a baya bai sa mun rabu ba, sai dan akan Laila banzar bazara?. Ifemi ( Masoyiyata) kema kinsan dole zanyi wani abun ko dan samo mana mafita. Na fiki jin zafin tawo da Laila da mu ka yi. Iyabo kar ki yarda shaiɗan ya rinjayi zuchiyarki. Ki tuna Gwadabe ne naki wanda kikai mishi Alƙawarin mutuwace kaɗai zata iya gibtawa a tsakaninki dashi, ki rufa mun asiri ki zauna a ɗakinki" Shiru yayi yana jiran abunda zance. Gwadabe a gaskiya bazan iya zama da Laila a ɗaki ɗaya ba. Bayan tana ɗakin mijinta ma bata dena turo maka da saƙonnin ƙauna ba. To ka sani in ba baka san na san sabida kai Laila ta kaso aurenta ba, to na sani. Dan haka bazan zauna da kishiyata ɗaki ɗaya ta gama gane mun sirrina ba, in aurenta zaka yi basai an turota yimun c.i.d ba." Yanda nake maganar ina haki yafi komai ɗaga ma Gwadabe hankali ƙuri yayi mun da idanu yasan tabbas naje maƙura dan tsakaninmu yi nayi ne, bari na bari. Kafin ya tuno lafazin da zai rarrasheni dashi akayo kiran wayarshi, ya zaro a aljihu. Oga Lurwanu naga an rubuta, shine ogan Gwadabe wanda yake ma karen mota. Da sauri ya ɗaga, murya a sanyaye yace. "Oga Lurwanu yanzu na shigo Kanon, zan tawo yanzu in sha Allah, an gama lodinne?" Daga cikin wayar Oga Lurwanu yace. "Ka hanzarta Gwadabe, an yi rabin lodi, ana gamawa zaku kama hanyar Ikko da izinin Allah. Karen motarka yana nan tare dani tuntuni." "To Oga Lurwanu abinda zan barma iyali fa? Wallahi ɗari ukune a jikina da zanyi kuɗin motar zuwa inda kuke. Kuma a gidan babu komai. Kasan lamarin sai godiya" Oga Lurwanu yace. "Wannan babu wata matsala. Kai dai ka tawo ɗin. Ko yaro ka ba saƙo ya ajjiyema Iyalan. Kai muke buƙata yanzu" A haka su kai sallama da juna. Yana sauke wayar a kunnenshi ya dubeni. Hawaye nake ta faman sharewa. "Iyabo gashi bani da lokaci a halin yanzu. Kina jina da Oga Lurwanu. Abinda zance miki shine ki tausayama masoyinki ki yi zamanki a ɗakin ki, ki toshe kunnuwanki, ki ɗauke idanuwanki daga gani ko jin komai. Dana dawo zan nema mana mafita, amman in sha Allah Laila ba zata zauna tare damu ba. Ki kuma kwantar da hankalinki Laila ba zata taɓa samun gurbi a zuchiyata ba. Ba zata iya ruɗata da komai ba, a gabana ta yi wasan ƙasanta. Ni naki ne ke kaɗai Iyabo. Nasan kishi ke nuƙurƙusar zuchiyarki. Kinga hanya zan hau, taya hankalina zai kwanta in na barki kika koma gida. Sannan ke kan ki in kin koma gidan wani sabon damuwarce kika jefa mu a ciki. In ci albarkacin soyayya haba tauntsun soyayya" Duk wannan kalaman cikin sigar so gami da rarrashi yake yinsu. Gabaki ɗaya sai jikina ya mace mus. Ance tsakanin mata da miji sai Allah. Duk da ina jin bazan iya zama da Laila ba. Amman ya kamata in ma mijina uziri tunda shima umarni aka bashi, kuma bazan so akan faranta mun ya saɓama wacce tai sababin zuwanshi duniyar ba. Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace. Kana da girman daraja a guna. Kaje Allah ya tsare maka hanya. Ya kareka da sharrin ƙarfe da sharrin hanya. Allah yasa sai dai ka ajjiye motar da hannunka ba dai ta ajjiyeka ba. Allah yasa a soma a sa'a, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ne yazo. Ka kular mun da kan ka Gwadabe, dan akwai tarin tulin maganganu marasa daɗin ji a kan ku direbobin manyan motoci, sunan masu sana'ar tuƙin manyan motoci yayi ƙauri, sun san sirrin ajjiye daduro ni bana zarginka amman ina tunatar dakai jin tsoron rabbissama wati wal ardi. Kar ka zama daga cikin irinsu dan Allah, duk da a ko wacce sana'a akwai nagari, akwai na banza." Murmushi yayi ya rungumeni dani da ƙaton cikina yace. "Kamar yadda kika faranta mun raina, Allah ya faranta miki kema. Mala'ikun Allah ku shaida na ɗaga ƙafafuna domin Iyabo matata ta shiga Aljanna" Dariya mu ka saka dukanmu. Ka hanzarta jiranka akeyi dai kar ka shagaltu" "Wallahi kuwa. To ni zan tafi, zan aiko da ɗan kayan abinci da kuɗin da zaki riƙe a hannunki. Ki kula da kanki da abinda yake cikin ki. Da zaran kin soma jin naƙuda ki sanar ma Bose, nima ki yi gaggawar sanarmun, Bara'u sai ya zo ya tsaya. Ballema ina roƙon Allah yasa sai ina nan zaki haihu. Sannan ki kula sosai, Laila ɓarauniyace ta bugawa a jarida, ko ɓera bai kaita iya sata ba, kuma bai fita dabarun iya sace abuba, har hannu take sawa a wandon jeans na maza a kasuwa ta yashesu, gidan biki ko suna kuwa sata take yi tamkar tana bacci dan sauki. In zaki je gidan aiki ki kulle uwar ɗakin ki kar ki sake ki bar mana ƙofa a buɗe. Dan komai ɗauka take yi" Sumbatata yayi a baki, tare da riƙo hannayena muka miƙe tsaye a tare. To in sha Allah zan kiyaye, Allah ya tsare. Mu je in rakaka" Tare muka fito zuwa falo. Laila na tsaye a gaban hoton aurenmu dake manne a falon. Na ci lace da gwaggwaro. Gwadabe ya sha rigar asheke da hular ashoke kai ka rantse beyerabe ne shima. Jin motsinmu ne yasa ta zauna a kujera mafi kusa da'ita. "Fita zaka yi ne Yaya Gwadabe?" Ta furta da zazzaƙar murya ba irin tawa ba, dan muryata tana da ɗan girma gami da kauri. "E tafiya zanyi ma. Ni sai na dawo. Iyabo ki koma ki kwanta ki huta zuwa azahar kya tashi ki yi wanka ki yi salla." Kafin in ce wani abun muka jiyo sallamar Uwani Tabalbalin ƙawata tun ta ƙuruciya, ƙawarda banda madadinta. "A maraba lale Tabalbalin kece a tafe? Ai kuwa kinci sa'a dawowar ƙawar taki kenan daga ƙauye" Cewar Gwadabe daya tari Uwani da fara'a sosai. Cikin dariya tace. "Gwadabe na Iyabo ikon Allah tsuntsun soyayyar daya tashi daga kan Debisi sai ya hau kan Ɗan hausawa. Fita zaka yi ne?" Dariya muka saka dukkanmu, wannan suna yaƙi fita a bakunan waɗanda suka san gwagwarmayar da muka sha kafin aurenmu. "Wallahi tafiya zan yi ma zuwa Ikko. Ya yaran, ina Hafizu Oga ba?" Dariya mu ka yi duka. "Hafizu na baroshi a majalisarsu" A wajen mu kai sallama da Gwadabe ya fita, mu kuma muka koma uwar ɗaki ni da Tabalbalin. "Ashe tafiya kuka yi Iyabo. Kaddai bikin ƙanwar mijinnan naki marar kunyar nan, wacce ta watsa mun miya a zani lokacin sunan Toye kuka je?" Zama na yi a bakin gado. Na yi shiru kawai dan batun zaman Laila na ci mun tuwo a ƙwarya. Zama Uwani Tabalbalin ta yi a kusa dani tace. "Akwai wata matsalar ne Iyabo? Nasan ai ba zata wuce irin wulaƙancin da dangin Gwadabe suke yi miki ba ko. Balle kunje ƙauye an shiga taron biki" Wallahi da shine ma da sauƙi Uwani. Ai kinsan Laila tsohuwar budurwar Gwadabe, ƴar uwarshinnan wacce kwanakin baya muka samu saɓani?" Kai ta gyaɗa tace. "Na ji na ji. Wacce take turo da saƙon batsa tana gidan wani ko, ai kece banza da baki zaune ƴar banza ba. Halan wani abun tayi miki a cikin taro?" Itafa ƙawata. Ana baki kina karɓa Tabalbalin" Bata labarin abinda ya faru nayi kab ina share hawaye. Uwani da ba dan in na koma gidanmu tamkar na tozarta aurena bane, da wallahi kafin Gwadabe ya dawo na bar gidannan." "A'a kar ma ki soma. Dan in ma kika je Iya Debisi sai ta kusan illataki banda kwakwazon da za tai ta yi miki, maƙotanku ma sai sun ji meke faruwa. Amman gaskiya kar ki kuskure ki yarda kici gaba da zama da'ita ɗaki ɗaya maganar gaskiya. Ba zata zo har ɗaki ta iskanta miki miji ba. Amman ko da wasa kar ki sake ki bar ɗakin ki, yo kin bata dama ta kwace miki miji cikin sauƙi kenan ma. Nifa dani Gwadabe yake Aure da tuni na seta kan ƴan uwanshi. Ki kwantar da hankalinki tunda Gwadabe yace zai samo muku mafita kema kinsan bazai barki haka ba. Ya kika baro Sakina da mijintannan nata mai barkwanci Bara'u?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Suna lafiya lau Uwani, ya Hafizu da yaran?" Shiru tayi na ɗan lokaci tace. "Iyabo yau haka muka wayi gari ko lomar da zamu kai bakinmu babu wallahi. Yaran sai turasu gidan Hajiyata nayi nasan ko ba komai ba zasu rasa abinci ba, tunda Hajiya na yin ɗanwaken saidawa. To mu ɗin bamu ci komai ba, ga ni da ciki na wata uku ban baki labari ba, wallahi bansan ina da cikin ba. Ga hayarmu ya ƙare gobe mai gidan zata zo karɓar kuɗinta, ko ficika bamu ajjiyeba, babu wanda muka ba ajjiya. To shine na sha maganin zubar da ciki cikin ya zube yau ɗinnan, Iyabo bazan iyaba, Hafizu bashi da zuchiyar nema. Ni rayuwarma ta isheni Iyabo, Talauci masifane ƴan uwanka ma sai su gujeka su ƙi taimakonka" Kuka ta fashe dashi kawai. Ban hanata rera kukan ba, domin kusan ni na fita sanin zafi da raɗaɗin talauci da wayar gari babu abinda za'a saka a ciki. Tunda Hafizu da yana da rufin asirinshi direban ƙaramar motane yana lodin Kano to Gomber, da Bauchi. Motarshi ce tayi haɗari ta yi rugu_rugu. Har yanzu bai samu wata motar ba. Shi kuma ya ɗaurama kanshi girman kan neman wata sana'ar. Daga haka ya ɓige da zaman kashe wando. Shi yasa rayuwar ta ɗaure musu. Amman ni dama a haka na shigo gidan Gwadabe na sameshi. Dama bashi da cikakkiyar sana'a duk abinda ya fita ya samu yi yake yi kawai. Numfashi na ja kana nace. Kiyi haƙuri Uwani da sauyin rayuwa. Mu yi ta yi musu addu'a babu dare ba rana. Ubangiji rabbissama
Chapter 10 · 0% Book details