← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 237

Sashe 72

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tafi makarantar allo dake yau babu boko. Ƴan kuci_kucin kuma Baban ya tafi dasu gona. Ya wajen su Baba Magaji?" Ɗan murmusawa yayi kafin yace. "Kowa yana lafiya, sannu fa da ɗawainiya Sakina allahu ya bar zumunci" Dariya tayi ta miƙe abinti taci gaba da kaye_kayenta har Bara'u yayo sallama ya shigo. Ganin Gwadabe ne yasa yayi Dariya, sai dai ya girgiza da yanayin daya ganshi a ciki, musamman baƙi da ramar da yayi. Ga wani rawani daya tuntuma a kanshi irin na buzaye. "Baƙin buzu gallah mu ka yi a gidan namu, Gwadabe maraba lale" Zama yayi suka tafa. Sakina ta dure musu ɗumemen dambu yaji rama da man shanu. "Fara cin abinci tukunna mu sha labari" Sai da Gwadabe ya ƙoshi ya sha ruwa kana yace. "Na sameku Lafiya ya ɗawainiya?" "Lafiya lau, ɗawainiya ai yiwa kaine Gwadabe. Ya bayan rabuwa?" Ɗan sauke kai ƙasa yayi yana wasa da yatsun ƙafarshi yace. "Sai alkhairi Bara'u. Ya gona?" Dariya yayi yace. "Gona lafiya lau, sai godiyar Allah. Lafiya irin wannan ramar haka Gwadabe, ciwo kayi mu bamu sani ba ko me?" Bara'u ya faɗa cikin kulawa. Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke kana yace. "Wallahi babu ciwo yau ce kawai Bara'u. Ga ciwon damuwar rabuwa da iyali lokaci guda shima yana damuna ainun. Kuma sana'ar tamu tana da wahalar gaske" Ajjiyar zuchiya Bara'u shima yayi. "Toh Allah ya kawo maka mafita. Ai rashin iyali ga wanda yasan daɗinsu babban tashin hankali ne. Sannan ya haɗema har da yanayin can ƙasar kasan baka sababa. Amman ya batun aurenka da Shafa da Hadiza?" "To Bara'u ni fa gani nake yi in haƙura da Shafa kawai. Bana jin motsin san su sam a raina. Ganin girman waɗanda suka mun kyautarsu kawai nake ji. Ka ganni sai in yi sati biyu ban riƙe nera biyar tawa ba. Da haka ne zan auri mata biyu? Atampa biyu kawai na iya ajjiyewa da sunan kayan akwati fa. Duk da Tamu zai taimaka mun, amman dole inma Hadiza" Shiru Bara'u yayi yana nazarin maganar Gwadabe, domin maganarshi abun dubawace. "To Gwadabe maganarka gaskiya ce domin Allah. Amman dole a nemi maslaha, kasan Tamu ba lallai yaji daɗi ba. Shafa kuma ta gama sa ranta da kai. A gidansu duk ansan da maganar aurenku fa. Ni ina ganin ka daure dai ka auresu du biyun. Sai a tura bikin ita Shafa zuwa nan da ko shekara ne. In yaso ita Hadizan sai ka soma aurenta. Ko yaya kake gani?" Kai Gwadabe ya gyaɗa kafin yace. "To hakanma gaskiya ne. Nima abinda du ya dameni kenan. Kaga kuwa in da za a ɗaga ɗin zuwa lokacin da ka ambata ɗin da abun zaiyi kyau. Muna sa rai abubbuwa zasu warware da izinin Allah. Dan sana'ar tamu in Allah ya dafa ma mutum yana samun arziki. Da ace ina da wasu jari ma a hannuna da abun sana'a zan dinga tafiya dashi ina ɗan siyarwa haka. A samu ɗan na kashewa." Bara'u yace . "Ga shawara kana ganin in kana siyar da magungunan gargajiya ba zaka samu ciniki ba? Da sai ka jaraba ai, ko maganin dattin ciki, da maganin basir, da ɗan na warware gaɓoɓi da sai ka dinga dafawa kana ƙullawa a leda kana tafiya dashi. Kuma fa akwai riba." Shiru Gwadabe yayi yana nazari kafin yace. "Wannan ma shawarace Bara'u. Sai in jarraba, in zan tafi zan tafi da wasu saƙe saƙin in sha Allah" "Sai kaga Yaya Hambali ya gyare gida ko?" Yayi maganar yana dariya" Gwadabe yace. "Gida yayi kyau sosai Bara'u, sai haska gari yake yi." "Hmmm ai Yaya Hambali in faɗa maka harkace ta buɗe mishi. Wani bawan Allah ne ya bashi kwangilar dabino, da jar dawa ko buhu nawa yakai yana siya. Kai duk inda dabino da jar dawa suke Yaya Hambali siye su yake yi ya kaima mutuminnan. Shi yasa bashi da aiki sai zuwa ƙauyuka ƙauyuka neman jar dawa Ance gidanshi na kano ya rushe ya maisheshi bene. Kuma ya sai gonakai shimfiɗa_shimfiɗa a bayan gidan gonar mai gari baka ga girmansu ba, wai yanaso bana yayi noman jar dawa ne." Gwadabe ya taya ɗan uwan nashi murna sosai. Har cikin ranshi yaji farin ciki, yasan ko babu komai Babala zata huta. "Ni na mance sai kazo kaga Auta a gida miji ya sakota uwar miji ta hanata zaman lafiya " Cikin mamaki Gwadabe yace. "Autan aka saka Bara'u?" Baki Bara'u ya saki yace. "Wai baka ganta a gidan ba, ko dai baka tsaya kayi hira da Babala bane?" "Hmmm Bara'u kenan" Nan ya kwashe duk irin cin kashin da Babala da Yaya Hambali su ka yi mishi. Ya ɗaura da cewa. "Zuchiyata dab take da bugawa. Dame zanji Bara'u . Batun mutuwar auren Auta kuma duk Babala ce ta sa aka sakota, ta hanani zama da Iyabo, gashi uwar miji ta hana Auta zaman aure. Lokuta da dama iyayenmu suna kusa kurai" Tsit Bara'u yayi, idanunshi suka rine da kyar yace. "Hakane Gwadabe kayi haƙuri. Ni kaina Yaya Hambali babu irin cin mutuncin da bai yi mini ba akan sai dai in cire Toye daga boko. Dana faɗa mishi gaskiya kuma yace na zageshi. Gwadabe Babala har gidanmu taje ta kai ƙarana" Sun jima sosai suna tattaunawa. Da rana saiga ƴan makaranta. Toye ya girma abinshi, bai mance da mahaifinshi ba. Har iyabo Toye saida ya tambayi Gwadabe. Zuchiyar Gwadabe sai tayi sanyi jin yaron bai mance shi ba. Sai da daddare Gwadabe ya samu damar yin waya da Hadiza da Shafa.Kwanan Gwadabe biyu a Takai, amman zaman duk ya gundureshi sabida irin hantara da munanan furucin Babala a kanshi. Bayan ya huta sai kuma yabi dangi da gaisuwa gida_gida. Kwananshi Takwas yayi sallama dasu. Dashi da Bara'u suka dunguma Habuja wajen Tamu domin su yi mishi bayani akan batun ɗaga biki. Bayan sunci abinci sun huta. Ya ga ƴan biyu ya basu ƴar tsarabar da yayo musu da yaran Tamu, ganin yanda yaranshi su kai kyau da gani ana kulawa dasu, dan kayan jikinsu ma mai tsada ne. Raɗa yaima Bara'u a kunne yace "Maganar ɗaga bikinnan a barta Bara'u. Kunya duk ta lulluɓeni wallahi, jibi hidimar da yaketa yi da yara fa" Kai Bara'u ya gyaɗa halamar hakane. Fitowar Shafa itace ta dakatar da Tamu da magana dan tambayarsu yake yi gulmar me suke yi. Jus ta dire musu tasha ado tayi kyau tana ta ƙamshin turare me daɗi. Kanta a ƙasa ta gaishesu. Bara'u yace. "Ja ira yau mu ake jin kunya Shafa? Lallai kin girma" Murmushi kawai tayi mishi. Gwadabe sai kallonta yake yi yana murmushi. Tamu ne ya miƙe tsaye tare da cewa.." "Kafin su gama Bara'u tawo mu shiga kaga gari. Ai kwana zaku yi dai ko? Dan nasa Shafa ta gyara muku shago an sa katifa ma" Bara'u ya miƙe tsaye yace. "Kwana zamu yi kai bama ɗaya ba, dan wallahi ni kam saina huta. Kai kaji falonnan wani sanyin fanka kuwa?' Tafawa su kayi tare da ficewa. Fitarsu ce yasa hankalin Gwadabe dawowa gareta, itama saita gyara zamanta. Idanu ya ƙura mata ita kuma sai sinne kanta take yi kunya ta isheta. Shi kuma yau ne ya samu damar kallonta tsab. Yarinyace gaskiya, tana da madaidaicin kyau, da matsakaicin tsayi, bata da diri a kallon da yayi mata a tsaye, amman ƙirjinta a cike yake masha Allah. "Gani a gabanki amman kin kasa cewa dani komai. Ke da kika ce kinata mafarkin zuwan wannan ranar. Sai naga kin kasa cewa komai " Sake sunne kanta tayi ƙasa. Yawan kunyarta sai ya zama silar burgeshi, kunya tana yima ɗiya mace kyau, tana zama wani ado na musamman gareta. Murmushi yayi kawai tare da girgiza kai. Shafa tayi mishi ƙarama sosai shi yama rasa taya zasu yi wannan zance. Da dai taga shirun yayi yawa sai yace. "To a ɗago fuskar mana in ɗan kalla" Ɗagowa tayi ta ɗan kalleshi, shima ya kalleta, tayi saurin kawar da kanta tare da cewa. "Barka da isowa, ya ka baro mutanen Takai?" Sai da ya yi Dariya sosai kana yace. "Suna lafiya, ya karatu ya aikin kuma duk anayi ko?" "Anayi Alhamdulillah" "To Allah yayi jagora. Sannu da ɗawainiya da ƴan biyu. Ayashe ta sanar dani irin hidimar da kike yi dasu. Tamu kuma ya bani labarin irin shaƙuwar dake a tsakaninku. Kina son zaki tafi dasu ne in mu ka yi aure?" Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta tace. "E inaso in tafi dasu, sabida zasu yi maraicina, kuma nima zanyi kewarsu da yawa. Gashi ba ƙasa ɗaya ba balle ince zan dinga sawa a kawo mana su hutu. To Amman Yaya Tamu yace babu wanda zai rabashi da su" Dariya Gwadabe yayi. Dariyar yadda take magana muryarta na rawa kamar tana gaban dodo." "Zan mishi magana in lokacin yayi. Dan inason in haɗe kan yarana. Toye dake wajen Bara'u ma zan ɗaukeshi in yaso sai in ba yayarki tayi riƙonshi. Zanfi samun nutsuwa" Da sauri ta ɗago tace. "Wacece Yayata kuma?" Kallonta yayi yana nazarinta, a muryarta yaji kishi. Sai ya basar yace. "Hadiza nake nufi ƴar uwata wacce zan haɗaku" A sanyaye tace. "Ka yanke hukuncin soma aurenta kafin ni kenan? Bayan ni aka soma baka kafin ita" jin furucinta da rawar muryarta sai yasa yaji kunya. Ba shiri yace. "Ko ɗaya Allah shine masanin wacece zata zama fari, in Allah yaso sai kiga rana ɗaya an ɗaura auren. Nace yayarki ne sabida Hadiza ta girmeki sosai. Bazawarace yaranta biyu" Ɗan boyayyen ajjiyar zuchiya ta sauke. A haka hirar taci gaba da gudana. Tsarabarta ya miƙa mata, ya miƙo mata agogon da Hadiza ta bayar a kawo mata. Har a fuskarta taji daɗin kyautar Hadiza sosai. Miƙewa Gwadabe yayi tsaye yace da'ita zashi masallaci an soma kiran sallar la'asar. Haka dai Gwadabe suka kwana biyu a gidan Tamu. Sunga karramawa sosai. Ranar juma'a ya kama hanyar nijer, Bara'u kuma ya kama hanyar Takai.
Chapter 72 · 0% Book details