← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 237

Sashe 12

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kayayyaki da take ta warewa na maza da mata. "Yauwa Iyabo ashe kin dawo. Kar ki so kiga yanda wanki ya taru mana, kinsan yara da ɓata kaya" Dariya nayi cikin girmamawa da ɗan risinama wanda kake mutuntawa wanda ya zama ɗabi'a mai kyau ga ƙabilar yarbawa nace. Ina kwana Alaja ya yaran?" "Lafiya lau, an yi biki lafiya dai ko? Yau da Toye akazo bai je makaranta bane?" Wallahi kuwa bai je ba sai dai zuwa ƙarshen wata. Wannan kayan har da su a wankin Alaja?" Na tambaya ina kiciniyar kwashesu tace. "A'a kayane muka fitar na kwalima, za'a tura ƙauye a buhu zaki zura mun su. In akwai wanda kike so sai ki ɗiba" Baki na washe nace. Ahhh irin na yarbawa" Alaja nima inaso, bari in tsakura tunda mabuƙatan muna da yawa. Amman duk sanda akayi a dinga cira mun. Alaja tace. "To ki kwashe duka wannan na matan ki bar na mazan, ai ban gama kwaso kayan ba ma" Ba shiri na tsugunna ina ta faɗin. Ahh_Ahhh_Ahh Alaja na mazan ma inaso in da hali, zan bama mai gidana shima yana da ƙarancin suturu' Shiru tayi tana kallona, mamaki na bata ko tausayina taji sai Allah, sai da ta sauke ajjiyar zuchiya tace. "To ki haɗa duka ki kwashe, zan fito da wanda na ware a ɗakina sai ki zuba mun a buhu. Akwai takalman maza ƙafa biyu a dokin ƙofa ki haɗa dasu in zai ma me gidan naki, ni zam shiga ciki." Ahhh Olorun bukun fun o ebi re ( Allah ya albarkaceki, ya albarkaci iyalinki) Na faɗa da yaren yoruba. Na fassara mata da hausa dana tuna bata jin yaren. Da "Ameen_Ameen" ta amsa ta yi shigewarta ciki. Bayan na tattare kayan na shiga aikin share_share ka'in da na'in. Ina yi ina wanki a injin. Bayan na ƙalƙale ko ina kuma sai na shiga ɗakin yaranta, sai da na goge kayayyakin dana wanke tas kafin na miƙe lokacin anata kiraye_kirayen sallar azahar. Na jera na yaran a sib ɗinsu, na Alaja kuma na kai mata ɗakinta na saka mata a sib. Na gyare mata ɗakin tas. Kafin nayi salla kuma. In idar da sallah sai na tsinci kaina da rashin aha'awar komawa gida. Sai na tsiri gugar kayan da Hajiya ta bamu, tunda a wanke suke, sai ƙamshin turare mai daɗi suke yi. Dana gama wajajen biyu da rabi dai dole na fito daga ɗakin yaran ina riƙe da buhun kaya da Toye. Robar da take zuba mun abinci ta miƙo mun, da wata farar roba babba mai murfi tace. "Miyar ganye ce a cikin robar nan, ta ɗan jima a firji ne bazan iya amfani da'ita ba bansan ko kina so ba?" Karɓar ledar nayi nace. Inaso Alaja. Aidupe ( Nagode) Nayi mata sallama muka kama hanyar komawa gida. Ga buhu a kaina, ga leda a hannun hagu, ga Toye ina riƙe dashi, ga uban ciki mai tsini a gaba, ina tafe da ƙyar duk jikina ciwo yake yi mun. Da sallama na shiga gidan, tsakar gidan tsit kamar ba gidan hayaniya da shewa ba. Turus na tsaya a daidai tagar ɗakina bakina a sake, furucin Laila na ƙarshe a waya ne ya daki kunnena. "Ai in sha Allah na shigo kenan sai dai ta fita ta bar mun ɗakin, Gwadabe nawane halak malak" Sai ta saki Dariya. Murya a daƙile nace. Salamu Alaikum. Nasa ƙafa na shiga, tayi saurin kashe wayar da take yi. Na ƙare mata kallo da kyau. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Chapter 12 · 0% Book details