← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 229 OF 237

Sashe 229

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni dai tunda na kwanta bani na farka ba sai asuba.
Bayan nayi salla na yi wanka ni da yaran sai na fito taya Luba girkin safe. Da misalin goman safe muna zaune a falo Luba na bani labari Hajiya ta kira Luba a waya akan suna hanyar dawowa dan haka ayi girkin dare dasu. Hakanne yasa nace ma Luba nice zanyi girkin daren. Wajajen azahar sai ga Usman ya shigo sai naga hannunshi duk datti ya nufi masaukina. Barin biyu nayi a wajen Luba nabi bayanshi. Ina shiga yana fitowa daga banɗaki. Idanu muka zuba ma juna. Yana tsaye yaƙi motsawa nima kuma na kasa ƙarasawa gareshi. Hannunshi ya miƙo mun dole ƙanwar naƙi na bi hannun. Ina ƙarasowa ya fisgoni duk girmana ya ɗaura kaina a ƙirjinshi. Idanuna na lumshe kawai inajin yana wasa da inda yafi ɗaukar hankalinshi. Banyi yinƙurin hanashi ba sai taimaka mishi ma da nayi. Abu fa tun daga tsaye sai gamu a zube a ƙasa. Ku dai kunsan komai.
Sallamar Luba ce tasa ya zare bakinshi a nawa yana sauke ajjiyar zuchiya. In tashi tsaye ya hanani tashi. In amsa sallamar ni kuma harshena yayi mun nauyi. Da taji shiru dole ta juya ina jiyo kukan biyu.
"Kin susutani haka doguwar riga take zama miki a baya? To daga yau kar in kuma ganinki da zani, doguwar riga kawai nake so, so samu irin waɗannan masu santsin. Ki shirya yau zaki tare dan jiya na ƙwaru"
Ni wallahi matanka tsoro suke bani"
Saida ya shafi wuyana yana wasa da sarƙar dake wuyan yace.
"Ki sha kuruminki ai na dawo dake gidana dake jikin wannan, yanzu haka jera miki kayanki akeyi ma"
Idanu na zaro, inason tambayar dalili ya hanani wannan damar.
"Ki bani abinci inci zan koma inga aikin. Su Alhaji Baba suna hanya fa yau zasu dawo.
Abinci naje na kawo mishi yaci ya ƙoshi ya koma can gidan tare da sake jaddadamun yau da ƙirjinshi zanyi matashin kai. Ni kuma har ga Allah nafi son yaje ga matanshi ni maci amarcin namu a can.
Ai kuwa da daddare sai ga su Alhaji Baba. Nan na gabatar musu da abinci suna ci harda Usman suna hira, ni dai nayi shiru .Da dai Alhaji Baba yaga dare yayi sai ya dubi Usman yace.
"Ya kamata ka ɗauki haramar tafiya kaga dare na yi. Ƴata kema ya kamata kije ki kwanta gobe zaki tashi da shirye_shiryen tafiya"
Ai zuruf na miƙe nayi musu sai da safe, Usman kuma sai kashe mun ido yake yi nayi kamar ban gani ba.
Sun jima ina jiyo muryarsu kafin daga bisani ya fice ya tafi can wajen matanshi.
Washegari na tashi da shirye_shiryen tafiya. Zuwa taran safe Anty Sumayya tazo muka fita, sai a mota take faɗamun da ƴar mai aikinta zamu tafi zata dinga yi mun renon ƴan biyu kuma ta ɗebe mun kewa in Usman zai yi aikin kwana. Ai kuwa naji daɗi sosai. Shagon dogayen riguna Anty Sumayya ta kaini ta dinga zaɓamun masu kyau kalar ƴan gayu. Daga nan muka shiga shagon rigunan bacci nanma ta siya mun masu bayyana sura ni dai duk kunya ta kamani.
Anty Sumayya inaso in sai kaji inaso in yi dambun namane"
"To Shikenan akwai mai kajin su Hajiya sai a sa ya kawo"
Ai kuwa muna dawowa na samu mai kaji ya kawo guda shida. Ni da Luba muka yi aikin dambun mune har taran dare bamu gama ba. Da daddare sai ga Mus'ab ƙanin Usman da wata ƴar yarinya da bata wuce shekaru sha uku ba da jakar kayanta. Luba ta kirani muka gaisa da Mus'ab yace.
"Anty Sumayya ce tace in kawo miki Halima ta kwana sabida gobe sassafe zaku wuce"
Allah sarki to nagode sosai ka gaida iyalan"
"Zasu ji. Ohh su Halima an zama Æ´an India iye iye"
Ya shiga tsokanarta ita kuma ta shiga murna.
A wannan daren na kai kusan biyun dare ina haÉ—a kaya. Inayi muna waya da Usman da duk ya dameni da zantukan sake layi. Ni dai sai dariya kawai nake yi mishi.
Washegari sassafe Mus'ab yazo shi da Usman shi zai kaimu Airport. Alhaji Baba ya jima yana mun nasiha haka Hajiya ma. Nan nayi sallama da Luba muka kama hanyar Airport. Muna zuwa muka soma bin layin shiga Bus ɗin da zata ƙarasa damu wajen jirgi. Usman na rungume da Hassan ga akwatin kaya. Ni kuma ina riƙe da kayayyaki Halima na goye da usaini.
Gaga gaga sai ga jirginmu a Abuja. Hotel ya kama mana a Abuja dan sai dare jirginmu ya ɗaga zuwa India da misalin ƙarfe takwas na dare. Allahu Akbar Allah shi ke da iko akan komai.
Tafiyar awa goma sha uku da minti goma a sama.
Karfe taran safe jirginmu ya sauka a filin jirgin Rajiv gandhi international airport.
Ni dai sai zazzare idanuna nake yi, ina biye da Usman har zuwa fitowarma daga cikin Airport niƙi_niƙi da kaya ga biyu ga Halima. Mota mai ƙafa uku muka shiga wanda a wannan lokacin ban taɓa ganinta ba har ga Allah. A filin jirgin ƙasa motarnan mai ƙafa uku ta sauke mu muka shiga, a wani dogon benci da masu jiran tashin jirgi suke zaune Usman ya zaunar damu.
"Ku zauna ina zuwa, zan kawo muku abinci kuci, sai in siyo mana tikiti jirginma da halama ya kusan cika"
Ni dai sai zazzare idanu nake yi ina kallo indiyawa maza da mata da yadda suke magana suna motsi da kayukansu. Wasu suna zaune suna cin abinci, duk masu cin abinci abun mamaki da hannu suke ci. Muma Usman ya kawo mana wata shinkafa da kaza, da wasu miyoyi dil_É—il daban daban kusan kala shida kuma a ganye aka zuba abinci sai aka É—aura a tire.
Ruwa ya zuba mun na wanke bakina da hannayena na soma cin abincin shi yana riƙe da biyu. Halima ma sai zuba loma take yi ta shawo yunwa duk da mun cicci abinci a jirgi amman dangin fulawane kuma ƴan kaɗan kaɗan ne a cikin kwalin. Sai da na ƙoshi na ba biyu suka ci Usman dai yace shi bazai ci ba.
Sai da mu ka yi sallar azahar aka soma sanarwa a shiga jirgi. Duk muka shiga muka zazzauna jirgin akwai girma sosai tarago_tarago. Tafiya mabuɗin ilimi muna tafe Usman yana yi mun bayanin garuruwan da muke ta wuwwucewa, abubuwan gwanin sha'awa sai gamu a garin Rajasthan garine mai matuƙar girma da yawan jama'a yana daga cikin manyan birene a India a ƙarƙashin Rajasthan akwai birane masu yawa. Daga nan muka hau wata doguwar bus zuwa Udaipur city.
A wannan gari Usman yake zaune. Bamu muka shiga gida ba sai dare, iyakar galabaita nayi sosai abinka da ba'a sababa. Da ƙyar na daure na tashi na yima biyu wanka suka sha nono sai bacci suma sun galabaita sosai. Usman na fitowa daga wanka nima na shiga na watsa ruwa na gargass jikina sosai. A zaune a kan teburi na fito na sameshi yana cin cake da dambun nama da tea. Murmushi ya sakarmun yanata ƙaremun kallo ganina ɗaure da tawul. Ni kuma duk sai naji na takura rigar baccina na dauƙa na koma bayan gida na saka, na shafe jikina da Humrar matan aure.
Na fito na sameshi sai dariya yake yi mun ni kuwa na basar na je na ja kujera na zauna na soma shan tean da ya haÉ—a mun.
"Iyakar abinda zaka ci kenan ko in shiga kitchen in dafa maka wani abun?"
Idanu ya lumshe yace.
"Ya'isheni yau ba daren cika ciki bane yau ni dake ne a wannan daren. Na kai Æ´an biyu can É—akin Halima in muka gama abinda zamu yi sai in dawo dasu, gobe zamu shiga kasuwa mu siyo musu gadon yara"
Gaga_gaga a wannan daren abubbuwa da dama sun faru na farin ciki masu tsaiwa a zuchia.
Allahu Akbar bawa bai isa tsallake ƙaddara ba, face adda'a dake rage karfin ƙaddara koma ta canjata baki ɗaya. A hakanma nayi imanin adda'ata ita tasa Allah ya taimakeni.
Usman ya zame mun uwa ya zame mun uba. Ya haÉ—ani da yara ya rungumemu. Gaga_gaga rayuwa taci gaba da shurawa cikin farin ciki. Cikin watanni dani da Æ´an biyu duk muka canja jin daÉ—i da hutu ya soma sauka sossi a jikinmu.
Rayuwar tayi daÉ—i ci gaba ya sameni na komawa makaranta.

Bayan wasu shekaru:.

MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

ramlex266: Ina mata da suka amsa sunan su ba Muna mata ba....

Ina macen da take so ta zamo tauraruwa a gidan mijinta,itace uwargida itace amarya...
ramlex266: Uwargida ko Amarya shin minene matsalar ki a wajen miji?

Rashin dandano ko ni'ima?
Bushewar farji qayau kamar busashen ciyawa?
Rashin samun gamsuwa a wajen maigida ko rashin sha'awar ce ga baki d'aya?
Budewar farji kamar kofar wambai ko qarni/wari ke damunki
ramlex266: Kina so ki zama tauraura kuma sarauniya a wajen oga a rasa gane sirrin naki? Ki zamo yar gaban goshi sai yanda kika ce wato kin mayar da oga mijin kafin ta ce? Ba boka ba malam gyaran shimfida kawai Hajiya to ki nemi hjy ramlex domin qarin bayani
ramlex266: 07069722234 ko 08064421211

Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi😆 Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanyar tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata😍
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801
Chapter 229 · 0% Book details