Sashe 234
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Wallahi ni Uwani kaina a kulle yake. Kinsan Allah ji nake dama mutuwa nayi tun farko"
Hajja Mama wacce duk hirarmu tana zaune tana jinmu tace.
"Assha iyabo. Bawa bai isa ya tsallake ƙaddararshi ba, karma ki soma faɗin haka. Dole za'a samu manyan malamai, ko kotun musulunci sune suke da ilimin warware wannan ƙullin. Duk abinda ya faru ki rungumi ƙaddararki. Ki gode ma Allah ma, a jikin Usman gidaje biyu manya kika siya a garin Lagos banda kwala_gwalai da kika tara. Bugu da ƙari kin koma makaranta ke malamar kiwon lafiya ce. Ga yaranki sun samu karatu me kyau. Ki gode ma Allah a duk yadda rayuwa tazo miki "
Sukaita rarrashina dani dasu, da Usman ɗina babu wanda ya runtsa a wannan daren. Ruwan hannuna sai asuba ya ƙare na zare na miƙe da taimakon Uwani na ɗauro alwala nayi Sallah ina zaune a kan dadduma na buga tagumi zuchiyata sai harbawa take yi tunanin Usman cakuɗe da tunanin Hamma yana shirin haukata ƙwaƙwalwata.
Sallamar su Hassan da Abbansu ne yasa na runtse idanuna zuchiyata kamar zata faso ƙirjina ta faɗo.
"Umma ina kwana Yaya jikin naki?"
Cewar yaran da suka haÉ—a bakinsu duk suka zube a gabana
Lafiya lau jiki dai to ku yi ta mun adda'a Allah zai kawo mafita kunji ko yaran ummu?"
Da wani irin rauni na faÉ—a to Husaini sun riga sun girma tuni suka fahimci akwai matsala , sai dai basu ga fuskar tambayata ba.
A sanyaye muka gaisa da Usman kaina a ƙasa. Muryarshi a dashe ya amsa mun suka gaisa dasu uwani da Hajja Mama ma
"Uwani muyi magana dake a falo mana"
Ya faɗa yana fita. Miƙewa Uwani tayi suka fito falo
A falon Uwani ta tarar da yar Usman É—in a zaune tana cike da damuwa Anty Sumayya. Gaisawa suka yi da Uwani.
"Dan Allah a taƙaice ki bamu labarin iyabo Uwani. Tunda tun kuna yara kuke tare. Inason sanin wacece ita da musabbabin shigarta wannan matsalar da ƙaddara ta cillota garemu"
Cewar Anty Sumayya kenan. Uwani nan ta warware musu zare da abawa ta basu labarin duk wata rayuwa ta Iyabo. Kai Usman yake ta kaÉ—awa ya kasa cewa uffan sai tsananin so cakuÉ—e da tausayin rayuwar matarshi. Anty Sumayya ce tace.
"Na tausaya mata matuƙa. Uwar mijinta na farko bata da imani. Na jinjinama aurenta na biyu da irin yadda soyayya ta jata. Ta kuma yi kuskure da a saninta ta auri Hamma alhalin tasan wacece Hama. Amman ƙaddarallah. Yanzu Hajiya uwani tunda Hajiya Iyabo bata da ishasshiyar lafiya ki bamu lambar Hamma, da lambar Debisi mu kirasu sai su zo su samemu. Akwai wani alƙali dake alƙalanci a kotun musulunci zamu gayyaceshi yazo ya warware mana wannan ƙullin.
Usman kayi haƙuri dan Allah ka daɗa nasan kayi.
Ita ƙaddara ta rigayi fata. Ka duba da duk irin soyayyar da Iyabo tayi ma Hamma ko zaman shekara ɗaya cib basui ba. Kai kuwa sai da ka shekara goma sha bakwai da'ita ta haifa maka yara har uku duk kuruciyarta kai ka kwashe ta. Nasan irin son da kake yima Iyabo da irin tasirinta a rayuwarka ka dangana ka karɓi duk abinda Shari'a tazo dashi"
Uwani ta É—aga waya ta kira Hamma.
"Hajiya Uwani barka da safiya ya Kano da yaran?
"Malam Hamma kowa yana lafiya. Dama na kiraka ne muyi magana da kai. Gani a Gombe kuma cikin amincewar Allah mun haɗu da Iyabo yanzu haka muna tare a gida ɗaya tare da yaranka ma. Kazo ka sameni a Gombe dan Allah in da hali kazo da wani babba domin akwai wani babban ƙulli"
"Allahu Akbar. Allahu Akbar Allahu Akbar ya Allah nagode maka Allah na gode maka ashe zan sake ganin iyabo. Mustafa inane gabas zanyi sujudul sukur" Yake tambayar na kusa dashi.
Hamma duk ya birkice ya saki kukan murna yanata jero addu'o'in godiya ga Allah.
"Uwani nagode gobe zamu tawo yanzu zan kama hanyar Adamawa"
Nan Uwani tana share hawaye ta zare wayar a kunnenta ta kira Debisi nan shima suka ruÉ—e da murna duk aka tsaya akan gobe suma zasu tawo.
Usman yayi shiru sai Allah yake ambato a zuchiyarshi kawai. Yaranne suka zo suka fice daga gidan. Dr kuma ta shigo sake duba jikin Iyabo.
Uwani ta miƙe tabi bayan Dr, Alhaji Usman da Anty Sumayya suka fita
Nan duk wanda ya dace su zauna dasu dangin iyayensu manya sun zauna sun tattauna an fasa matsalar dai. Cikin ƙanƙanin lokaci aka san halin da ake ciki.
Ga Usman a zaune Suna karbar gaisuwar makoki amman hankalinshi baya tare dashi. Ƴan biyu dake zaune a jere dashi kawai yake ji a halin yanzu Iyabo kam ya riga da yasan ta kuɓuce mishi in ba wani ikon Allahn ba. Amman yana ji a ranshi da iyabo zai ƙare rayuwarshi, irin sonda take nuna mishi yafi son da tayi ma Hamma a baya a labarin da Tabalbalin ta bashi. Idanunshi yake lumshewa lokaci zuwa lokaci.