← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 237

Sashe 13

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm

NAMA YA DAHU..
ROMO ÆŠANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.

Lamba ta biyar (5)

Saye take cikin shuɗiyar atampa, ta ci kwalliya da jan baki da hoda, fararen idandunanta rambaɗe da kwallin daya sake fito da hasken fatarta. Sai wani ƙamshi take yi ita da falon. Haƙiƙa na tsorata da Laila da muguwar nifaƙar dake tafe da'ita. Amman in ta san wata ai bata san wata ba. Wanda ya riƙe Allah shi ke da gagarumar riba, nasara tana biye dashi. Dan duk nisan jifa dole ya dawo ƙasa. Kallon dana cikata dashi shi ya jefata cikin taraddadin daya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Murmushin dole na sakar mata na yi shigewata ɗaki, na zauna daɓas a kan gado ina sauke numfashi kawai. Tagumi na zuba ina tunani. Na jiyo murya a falo kamar ta Burodami Debisi. Da hanzari na leƙo ai kuwa shi ɗinne a tafe da abubbuwan arziki. A guje Toye yaje ya ɗafeshi, shi kuma yayi maza ya rungumeshi tsam a jikinshi. Ɗagowa yayi ya ƙuramun idanunshi, nima shi nake kallo.
Burodami barka da zuwa"
Na faɗa tare da ƙoƙarin kawar da kallon da yake yi mun. Hijabi na zura , ban fito ba sai da na zuba mishi abincin dana dawo dashi daga aiki. Jallof ɗin taliyace ta ji bushasshen kifi, na zuba ruwa a kofin roba, na ɗaura a tiran roba, sai na fito. A gabanshi na dire tiran, na sake komawa na zubo ma Laila da Toye abincin bai yi ragowa ba, ga raina ya biya ina fatan Burodami Debisi ya ci ya rage in samu in lasa. Miƙoma Laila abincinta nayi, Toye ma na zaunar dashi a leda ya soma cin nashi.
Ekabo Burodami ( sannu da zuwa Yaya) Ya gida, wa ni Iyawo re bawo ni ebi re? ( Ya Iyaninka) Murmushi yayi mun yace.
Awon ti wani ol atanran. Bawo ni o se wa ( suna lafiya, ya kike?)
Ohh mowa daa_daa ( lafiya Ƙalau) Ga abinci kaci karya huce. Abincin ya kalla nima ya kalleni, saurin kawar da kaina na yi gefe guda. Murmushi yayi tare da girgiza kanshi.
"Ba zama nazo yi ba. Kuma in naci abinci anan, in na koma gida Emisi ba zata ji daɗi ba in nace mata na ƙoshi, dan na barota tana ta faman dakan sakwara" Wani yawu ne na jarabar kwaɗayin masu juna biyu ya tsinko mun jin an ambaci sakwara, muƙut na haɗiyeshi kawai, dan bani da yanda na'iya.
"Ga TV da dvd, da kafet na kawo miki, na sauya ma Emisi kayan ɗakine shine na raba muku tsofaffin. Yanzu haka daga gidan Simbin Maman Kokodeen nake na kai mata labulaye da kujeru" Har ƙasa na tsugunna ina ragargazo mishi godiya, dan nayi farin ciki sosai, a cikin gidan ni kaɗaice bani da kayan kallo. Wataran matan gidan suna haɗuwa a ɗakin mutum ɗaya su harhaɗa kuɗi a yo renting ɗin kaset sai dai in jiyo sauti, muna dai da rediyo da muke sauraren labarai, harma wataran in saka kasetin waƙar yarena, dan Allah yayi ma yarbawa baiwar iya waƙa da son rerata, dan ko karatu zamu yi da waƙe muke yinshi, gamu da son sha'ani a taru taci asha ayi ashobi. Dubu biyu ya zaro ya ajjiyemun mu kai sallama ya fice. Kinkimar komai nayi na shigar ɗaki, na dawo na ɗauki abincin nayi shigewata, Laila na zaune bakan a zaune tayi tsit da halama saƙa take yi da mugun zare a ranta. Da daddare Gwadabe ya kirani mu ka ɗan taɓa hira ba mai yawa ba dai haka, yai mun albishirin ƙila jibi ko gata ya dawo da izinin Allah. Fatan alkhairi nayi mishi, tare da samun alkhairai.
Washe gari ma kamar jiya ina gama komai na tafi wajen aiki abina. Ina dawowa tun daga bakin zaure na fahimci masu waje sun dawo mai tabarma dole ya naÉ—e, dan muryoyinsu har waje nake jiyosu ana mayar da yanda akayi da yanda za'ayi. Da sallama na shigo amman babu wanda yaji balle su lura da shigowar tawa. Karab a kunnena na jiyo Laila tana faÉ—in.
"Ai ku baku ga irin kallon soyayyar da take ma farkan nata ba. Wai ni zasu ninke baibai. Ya kawo TV da dvd harma da kafet ƙato, ga kuɗi fa. Bai tashi zuwa ba sai da ta ga ba idanun Gwadabe" Yaya Haula tace.
"In banda abinki Laila yarbawa ai sun saba iskanci wannan ba wani abu bane. Su da suke zaman wa jo ko, yarinya tana gaban iyayenta saita koma ɗakin saurayi, wai da sunan gwajin mahaifa, sai ya ɗirka mata ciki zata dawo gidan iyayenta. Kiga anata murna abu yayi kyau zata auru. In kuwa juyace shikenan an shata musulla. To su da suke haka har dan tsohon kwarton Iyabo ya biyota ɗakin aurenta wani abunne?" Ƙirjina take naji yana fat_fat_fat take numfashina na soma jin yana karkatsewa. Ban yi aune ba na jiyo muryar Gude tana cewa.
"A can gidansu ma fa ɗakinsu ɗaya akace, tare suke gwamutsuwa su yi baccinsu, kinsan yarbawa dai sai a hankali basu cika hankali ba. Ni dai na rasa uban abunda Gwadabe ya gani a jikin beyerabiya wacce ƴar uwarshi Bahaushiya bata dashi. Ita ba kyauba, sai gandar baki da kayan ɗuwaiwaka ɓaka_ɓaka iyakar abinda matansu ke dashi kenan fa" Dariya suka saka dukkansu. Da Suwaiba muka haɗa idanu ina tsaye kasaƙe ina jin irin sharrikan da ake bina dashi.
"Ahh kin dawo ne Iyaa Toye shine ba ko sallama?" Ta kula ni ne domin ta ankarar da abokan gulmar tata tai musu isharar wanzuwata. Ai kuwa sai su kai kamar ruwa ya cinyesu kawai.
Hmmm e nadawo, ai nayi sallamar hira ce tayi daɗi shiyasa baku ji ni ba. Sannunku da hanya." Ina kaiwa nan na yi wucewata zuwa ɗakina. A saman kujera na zauna ƙirjina na soya mun. Da ƙyar na iya sa abinci a bakina, salla ma a daddafe nayi, kawai sai na ji na zama marar lafiya gaske. Sai tubka da warwara nake yi a zuchiyata hakanne ya hana ni sukuni da numfashi me kyau.
Tun dawowar su Yaya Haula daga Takai, al'amuran gidan suka sake jagwalgwale mun. Sabon gulma da tsigudidi aka buÉ—e sabo. Laila kuwa irin ado da kwalliyar da take yi yana firgitani sosai. A tsakar gida suke wuni gulma da shewa, a gabana suke yi ma Laila adda'ar samun damar warce zuchiyar Gwadabe, tana amsa musu da Ameen.
Ranar da Gwadabe ya faɗamun zasu shigo Kano da safe ina zaune ina wanki a ƙofar ɗakuna, ina ɗan waƙe_waƙenmu na yarbawa. Baban Nazifi ya fito daga banɗaki, dake banɗakin gidan a kusa da ɗakinmu lungun yake. Har ya wuce sai ya dawo da buta riƙe a hannunshi.
"Wadannan randunan naki, da gayyar tarkacen robobinki, da wannan kwantenar da kike girki a ciki sun tsushe hanyar wucewa ban É—aki. Sabida haka ki tattare komai a wajen ki sam inda zaki ajjiye, irin wannan tarkace suke lalata gida. Yana gama faÉ—ar hakan ya wuce yana mita. Sukairaju wanda fitowarshi daga É—aki kenan yace.
"Yaya Hambali magana kake yi ne?" Ya tambayeshi. Cikin É—aga murya dan in ji yace.
"Da wannan masu kwalo_kwalon nake yi, kasan yarbawa da ƙazanta gasu ta tarin shirgi, ca nayi ta kwashe randunanta sun tare hanya." Harisu dake ɗaki sai ya amsa da cewa.
"Yaya Hambali ai nima fa na jima ina son ince tarkacen lungun su Gwadabe yayi yawa, in zaka je banɗaki sai ka ta ture bokatai kafin ka wuce" Kaina na sauke ƙasa kawai. Gabaki ɗaya akan wannan maganar sai da kowa ya tofa albarkacin bakinshi. Ni dai da zafin zuchiya na gama wankina na nufi bakin rijiya zan ɗebi ruwa. Laraba ƙanwar Nazifi ƴar Yaya Haula kenan, tana bakin rijiyar tana ɗiban ruwa.
Laraba ɗan zuba mun ruwa guga biyu nayi ɗauraya bayana ya riƙe" Ai ina rufe Baki Suwaiba ta iso inda muke da bokatanta da bahunanta itama zata ɗebi ruwa. Da safe duk matan gidan muke ciccika kayayyakin aikinmu, da randunanmu da ruwa. Buɗar bakinta tace.
"Harda su kaza acin danƙo. Akanme yarinya uwarta ta sata aiki, zaki dakatar mata da aikin da aka sata kice ta zuba miki? Laraba in kin gama bani gugar" Ina tsaye Laraba ta gama jan ruwanta ta tsab sai ta miƙo ma Suwaiba guga. Ni ko nasa hannu na warce gugar a hannun Laraba. Na zura a rijiya. Suwaiba ta nemi kamani da kokawa a bakin rijiya, ai kuwa na dubeta nace.
In ki kai wasa zan miki hajijiya in jefaki cikin rijiyarnan Allah, ki shiga taitayinki ba fa tsoro nake ji ba, ina dai son mu zauna lafiya ne. Da sauri Suwaiba ta matsa dan ni ɗin ƙatuwace tubarkalla masha Allah, kun dai san matan yarenmu akwai ƙiba babu laifi, gani da mazaunai a sama ɓaka_ɓaka masha Allah. Nan matan gida su kai mun ca a kaina, kowa na tofa albarkacin bakinshi, Gude har tana zunguremun kaina. Mazajen gidan a lokacin sun fita nema. Ni dai har na gama kab aikina na tsakar gidan, basu dena kwashena iyayena da dangina albarka ba. Ina shinfiɗa kafet ina hawaye harna gama shinfiɗawa, na saka tv da dvdn a inda ya dace, ɗakin sai ya sake sosai. Randunana na kwasosu na saka ɗaya a bayan ƙofar falo, ɗayar a uwar ɗaki, bokatan na ɗaurasu akan randar falo, bahunan kuma na ɗaura a saman randar uwar ɗaki, na fita na share wajen tas na shigo ciki. Duk fa wannan aikin ina jin ciwon mara da nake kyautata zaton haihuwace. Ina ninkin kaya na ji ciwon na ƙaruwa mun, ina jiyo ɓuruntun Laila a falo. Waya na ɗaga na kira Uwani Tabalbalin ,da Bose na sanar musu ina naƙuda, Bose kuma ta kira gida ta sanar, a cikin ƙasa da awa guda sai gasu dukkansu afujajan. Gashi ko reza bamu ajjiye da sunan haihuwarba, ta abinda zamu sa a bakin salati muke yi.
Zaman dirshan nayi a ƙasan leda, sai zufa nake yi, ina ɗan nishi sama_sama su nai mun sannu. Ana cikin haka sai ga Yaya Mulka matar Burodami kokodeen, babban ɗa a gidanmu ta iso.
"Yaya jikin nata Bose? "
"Gashi nan dai tana ta fama, ko dai zamu kaita asibiti ne? Ƴan biyu ne fa a cikin ina tsoro" Ni da naketsakanin rayuwa ko mutuwa na shiga ɗaga musu hannu, ina musu nuni da su barni bazan je asibiti ba. Amman da ciwon yai tsanani gashi harna soma galabaita, babu shiri suka ɗaukeni, Burodami kokodeen ya zo da mota ƙofar gida. Matan gidanmu sai gani su kai an rirruƙoni mun fita. Sai faɗi suke
"Au naƙudarce mu da muke cikin gida bamu sani ba, sai danginki kika kira? Yarbawa munafurci a jininku yake. Wannan ai iskanci da rashin daraja dangin mijine"
Bansan wacece ta yi maganar ba, amman babu wacce ta tanka mata.
Uwani maza je ki rufo mun uwar ɗakina. Na ƙarashe faɗe ina nishi.
Chapter 13 · 0% Book details