← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 237

Sashe 43

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tausayi gami da ƙaunar yaran ta shigeshi ainun. Harma yake ganin ganinsu ne kaɗai ka iya rage mai zafi da turirin rashin Iyabo. Haƙiƙa yayi rashin macen kirki, macen da tafi kowa sonshi da sanin hamimmancinshi. Ji irin wuya da ɗawainiyar da ta dinga yi a sanadiyyar ciwonshi. Amman ji irin sakamakon da su Babala suka yankar mata na tarwatsa duniyarta, tare da farraƙata akan ƴaƴanta da mijinta. Rungume yaran yayi jikinshi babu laka sam, rarrashin Taiwo yayi har sai da tayi shiru. "Toye zo ka kula dasu bari in siyo muku waina kuci" Yana faɗin haka ya fice, babu ko nera biyar a jikinshi, bashin mai wainar ta bashi na wainar hamsin, ya dire musu suka ci, suka sha ruwa. Fita yayi ya shiga kitchen ɗin Iyabo ya kunna risho ya ɗaura musu ruwan wanka. A kitchen ɗin yayi zamanshi tare da tariyo irin rayuwar da su ka yi da Iyabo, da irin nutsuwa da farin cikin da take samar mishi babu dare babu rana. Yana kitchen ɗin Babala ta leƙo da kwanon abinci a hannunta, ganin yanda yayi tagumi ya tusa risho a gaba ne yasa tayi turus a tsaye da kwano a hannunta. Yaran kuma tana jiyo ƙiriniyarsu. "Gwadabe au so kake yi tunani ya halakamun kai. Alhalin ita tana can hankalinta a kwance?. Yanzu me kake yi a ɗakin girki" "Ruwan wanka nake tafasawa zanyi ma yaran wanka Babala" Harara ta watsa mishi tare da cewa. "Ba cewa nayi maka zan tafi dasu ƙauye ba, ka ganni abinci na leƙo in ajjiye maka fa, sai in ɗebesu danyanzu zan juya yau muna da biki a gidan mai gari" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da tasowa jiki ba kuzari, kirjinshi kuwa sai harbawa yake yi, zuchiyarshi na watsa jini jikinshi bisa rashin ƙa'ida. Hakanne ya haifar mishi da jin jiri da mashasshara mai zafin gaske, dan har hucin zafi yake ji a fuskarshi. Bakinshi kuwa tamkar maɗaci aka zuba mai haka yake ji. Inda Babala take tsaya ya isa. "Babala yarannan ni zan riƙesu da hannuna. Inaso zasu yi karatu mai zurfi ba zasu yi rayuwa a Takai ba. Kab yaran gidannan a cikin gidannan su ke rayuwarsu, wasu muna tare dasu, wasu kuma sun yi aure. Dan haka nima zan riƙe yarana" Babala tace. "Da kyau Gwadabe. Dama ni dan in tausaya maka in ɗauke maka nauyine a matsayinka na namiji. Amman tunda har kana ganin reno abune mai sauƙi, gaka ga yaran. In sun ga dama suga ƙarshen biro. Duk karatunsu ai basu isa ganin ƙarshen biro ba. Kuma ka shirya sati me zuwa ka tawo zance wajan Laila ka shiga sahun manemanta, dan manema sun yi mata ca a halim yanzu kowa so yake ya ɗauketa, ni kaga tafiyata" Ta dure mishi kwanon abincin nashi ta fice tana surutai tare da kutuntumawa Iyabo da yarenta zagi. Idanu Gwadabe ya lumshe kawai. Shi yaima yaranshi wanka fes, ya ja hannunsu har zuwa islamiyya kasancewar ranar asabar ce babu boko. A hanyar shi ta dawowane yaci karo da yaya Hambali a mota zai tafi kasuwa sai ya ɗan dakata. "Gwadabe daga ina kake haka? Kaga takalmin ƙafarka ɗaya naka ɗaya na matarka ne fa. An ya Gwadabe asirin da dangin Iyabo su kai maka ya gama sakar ka kuwa, sai kace wanda akace ma Babala ta riga mu gidan Gaskiya" Numfashi dogo Gwadabe yaja, ya kai duba kan ƙafafuwanshi, zahiri takalmin Iyabo ya ƙaƙaba a ƙafarshi duk rabin dunduniyarshi a ƙasa yake, takalmin ma kuma mai ɗan tudu. Ɗayar ƙafar kuma takalminshi taka teba ya saka. Allah yana gani baya cikin hayyacinshi balle har ya fahimci ƙafarshi a matse take, ko yaji yafi tuɗu ta ɓarayi guda. Murmushi kawai yayi. "Kaga yara na miƙa makaranta, bansan wari da wari na saka ba, hankali shine gani, idanu ƙululun kawai ne." Kallonshi Yaya Hambali yayi wata ƴar dariya harda shewa kafin yace. "To sai zuwa yaushe zaka soma zagayawa kasuwar, tunda dai sauƙi ya samu, kuma Iyabo data raɓeka ta raba mu da kai ta zama tarihi a rayuwarka. Kaga ai sai ka zo mu ringa tafiya kasuwa, kwanannan kaima zaka sai motar da kake so ka dinga tuƙawa" Murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo Gwadabe yayi, yace. "Nagode da tayinka Yaya Hambali. Amman bana jin zan amshi wannan tayin naka. In na warware da kyau zan nemi sana'a dede dani in soma. In Allah ya dafa mini sai kaga na yi gida harda mota, yarana sun samu ilimi ingantaccen" Iyakar abinda Gwadabe ya furta kenan Yaya Hambali ya fusata har yana doka sitiyarin motarshi. "Ni kake faɗa ma magana haka gatse_gatse gwadabe? Ka mance sanda nake goyonka muje gona, nake cire kudina in biya maka kuɗin makaranta, in kama hannunka in kai ka makaranta. Kaci kasha naima sutura duk da dukiyata, kuma nake matsayin uwa da uba duka a wajenka? Ko Harisu bai isa faɗa mun maganar banza ba, balle kai wanda a haife na haifeka?" Sai zazzare idanu yake yi yana kumfar baki, Gwadabe dai baice mishi komai ba. Har ya gama hargaginshi. "Hmmm Yaya Hambali kenan. Shagone dai ni Gwadabe bana so bana buƙata. Bana nema a wajenka a wajen Allahn daya baka nake nema, kaima ba dabararka bace ta baka ba ka san da wannan." "To Shikenan na cire hannuna a kan ka tunda dai taimakonka da nake son yi ne baka so. Kaje kayi Abinda kake ganin ya dace da kai ba shikenan ba? Amman in sha Allah dakai da yin kuɗi har abada Gwadabe muddin ina raye baka ba yin arziki da Hambali kake magana, ɗan iska marar kunya fitsararre Allah dai ya kwashe maka albarka" Yana gama faɗan haka fuu ya ja motarshi ya buɗe Gwadabe da ƙura, ya cika mishi idanu fal da kasa. Idanunshi a runtse suke hawayen bakin cikin danginshi na tsiyaya a idanunshi. Shin wai me yasa ƴan uwanshi su ka fi sha'awar ganinshi a cikin halin damuwa da ƙunci ne, anya kuwa Babala itace mahaifiyarshi ta asali kuwa, ko dai shi ɗin ɗan riƙone bai sani ba? Amman da ace ɗan riƙone da dole ƙauye su sani domin a ƙauye kunne ya girmi kaka. A wajen Gwadabe ya ci alwashin bazai taɓa tambayar kowa komai ba, bazai karɓi ko ficika daga hannun kowa ba. Zai fita nema, kamar yadda Yaya Hambali ya fito nema shi shi kaɗai a shekarun baya, kuma Allah ya buɗa mishi. Shima Allah shine gatanshi ba Yaya Hambali ba, zai nuna musu shi namijine mai zuchiya ba mai hangen na wani ba. Idanunshi ya buɗe ya karkaɗe fuskarshi da idanunshi ya ci gaba da tafiya. Haka Gwadabe ya kwana a tsakiyar yaranshi, yanda rana ta kasance mishi haka darenma ya zame mishi. Sai juyi yake yi, yana tunanin irin rayuwar soyayya da kulawar da suka yi da Iyabo. Da irin abubuwan da akaita yi mata, kuma ta shanyesu duk dan ta zauna tare dashi. Amman daga karshen ƙarshe duk kiyayewarta sai da sakin ya afku a kanta. "Iyabo ina roƙa miki Allah ya baki mijin da zai jarabtu da sonki fiye dani, Wanda ya fini komai a rayuwa. Ya Allah ka kai baiwarka Iyabo gidan hutu da jin daɗi, mala'ikun Allah ku shaida ni dai a zamana da Iyabo babu cutarwa, kuma kune shaidar ni dai na ɗaga mata ƙafa dan ta shige aljanna. Allah ka haɗata da abokin rayuwar da zai ɗaga mata tashi ƙafar shima." Sambatu kawai Gwadabe yake ta faman yi kamar zararre. Haka Gwadabe yai ta tunane_ tunane har gari ya waye musu. Kamar jiya bashin wainar ya kuma karɓoma yara su ka ci ya kaisu makaranta Yana shiga gidan ya tadda dangin Iyabo suna tozarci a tsakar gidan. Sun zo dibar ragowar kayanta da yayi ragowa, da suturunta dai da kayan aiki haka. A wannan rana ya yasha zagi da ele a wajen su Iya Beji. Har tukunya Iyaa Kokodeen ta kwaɗa mishi a gadon bayanshi. Da yaga tozarcin ya isheshi sai ya koma ƙofar gida yai zamanshi. Yaya Hambali kuma sai sababi yake yi cewar duk Gwadabe ne sila, daya haɗe musu jini da jikokin oduduwa. Gwadabe na zaune a ƙofar gida ya hango Bara'u tafe. Ƙuri yayi yana kallon tahowar abokin nashi har ya iso gareshi ya zauna daf dashi. Amman fa kafin yace wani abu sai ga su Iyaa Beji sun fito suna zage_ zage Yaya Hambali na biye dasu shima sababin yake yi. Kan kace me unguwa ta ɗinke, mata har ta katanga leƙe suke yi, kunsan mata akwai gulma ko ince son ganin ƙwaƙwaf. basu dena baloƙoƙinsu na gado ba, sai da Yaya Hambali ya cukume Iyaa Beji, a tunaninshi zai daketa. Ai kuwa taron dangi suka haɗu suka yi mishi da ƙyar mazan unguwa suka karɓeshi a hannunsu duk haushin Gwadabe suka saukeshi akan Yaya Hambali. Bara'u da Gwadabe suna zaune suna kallon ikon Allah kawai. Yaya Hambali ya matso kusa dasu Gwadabe a zafafe yace. "Allah wadaran naka ya lalace. Kaji dai kunya Gwadabe ace waɗannan gayyar na aiya gayyar na yadadan sune surukanka. Mu kanmu ka cutar damu daka dage sai da muka haɗa iri da yarbawa. Duk irin matan dake cikin hausa Fulani ka rasa wacce zaka so sai Iyabo. Jibi yadda mata suka dakeni har suka fashe mun baki dan iskanci kuna zaune" Bushasshen yawu Gwadabe ya haɗiye muƙut. Bara'u ne yace. "Yaya Hambali ayi haƙuri. Komai ai ya riga ya daya ƙare. Allah dai ya ƙara rufa mana asiri" "Gafara can. Bara'u ai ko kisa Gwadabe yayi ba zaka iya ganin laifinshi ba. Aikin ɓur in ji tusa" Ya buga kafarshi ta dama a ƙasa, kana ya shige cikin gida. Bara'u ya sauke ajjiyar zuchiya yace. "Kayi haƙuri Gwadabe na roƙe ka da girman Allah. Ka ɗauka wannan ƙaddarace daga cikin sinnar rayuwa. Iyabo kai mata adda'a gaba Allah ya bata miji na haƙiƙa. Ni kuma da nazo da zummar in tafi da yaran duka can wajena Sakina ta haɗe da nata ta riƙe. To ina cikin mota sai Tamu yai kiran wayata Allah da ikonshi na kwashe zance tas na sanar mishi, to sai yace shi zai riƙe ƴan biyun a hannunshi zai sa su a makaranta. In kanaso zaka iya barinsu a hannunshi. In kuma kayi aure zaka iya zuwa ka ɗebi yaranka ka
Chapter 43 · 0% Book details