← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 237

Sashe 9

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwadabe
Yana fitowa ya dubi inda Iyabo ta zauna, zamanta kawai ya duba yasan tana cikin damuwa mai yawan gaske. Amman da zata tona taga irin damuwar da yake ciki zata san damuwarshi ta dame damuwar da take ciki ta shanye. Ya jima akan Iyabo yana son su haɗa idanu domin karantar yanayinta amman fur taƙi yarda ta ɗago. Dama muddin Iyabo na cikin ɓacin rai bata yarda ta ɗago kanta, sannan bata iya furta kalma. Isowar su Bara'u ce ta dawo dashi hayyacinshi. Gefe guda abokin nashi ya jashi.
"Wadannan fantimotan ba na Laila bane Gwadabe. Kano zaku tafi da'ita ko me? Kasan zamanta gida ɗaya da matarka ba zai haifar da ɗa mai ido ba ko? Iyabo fa tasan irin soyayyar da Laila take yi ma, a lokacin da take ƙarƙashin inuwar auren waninka ma, ta kasa barin zuchiyar Iyabo ta nutsa, balle yanzu da nayi imanin farautar zuchiyarka zata je yi. Gwadabe ya kamata su Babala da Goggo Iyatu su ƙyale Iyabo ta nutsu, ta sha ruwa a gidanka. Yarinyace mai hankali da biyayya, gata da tausayinka, son da take yi ma mai tsananine. Shin ko dan so da ƙaunar da take yi ma ba hujja bane da zai sa Babala ta haƙura ta barku kuyi rayuwar Aminci ba?" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke yace.
"Ni bansan da wanne idan ma zan kalli Iyabo ba. Kar kaso kaji irin cin fuskar da Babala ta gama yi mata yanzu. Ba wanna ba Bara'u kasan ni Babala ta ba riƙon Laila a ɗakina zata zauna? Bayan hakan har tana ƙarawa da faɗin in mun daidaita kammu su hakan suke so. Ina cikin tsaka mai wuyar fita, ina jin nauyin Iyabo sosai, tana haƙuri da yawa da dangina." Bara'u ya dafe ƙirji tamkar wata mace yace.
"Gwadabe kace Babala ce da kanta ta baka riƙon Laila, alhalin tasan ɗakinka ciki da falone kuma ƙananu, a haka take so ku zauna da Lailan duk abinda kuke yi tana jiyowa? Zaman ma bazai yi kyau bane Gwadabe kuma in akace an yi hakan to tabbas an zalinci Iyabo kuma an shiga hakkinta. Tana da damar yi maka bore ko tawaye. Kuma itama Babala dole ayi mata biyayya a matsayinta na uwa. Amman Gwadabe kar in tsayar daku kuje. Ni kuma zan shiga in samu Babala mu tattauna wala Allah zata fahimcemu. In yaso Laila ta zauna a wajen Haula tunda ita babbace kuma tana da ɗakin ƴan matan yaranta. Duk da hakan zaman ba kyau zai yi ba, amman in muka samu hakanma dama_dama. Dan Allah ka ba iyabo haƙuri ni wallahi kunyarta nake ji ma" Kai Gwadabe ya ƙyaɗa yace.
"Kar ka wahalshar da kan ka da yawun bakin ka Bara'u. Ni nasan ko sama da ƙasa haɗewa zata yi, Babala ba zata saurareka ba balle ta fahimceka. Ko kasan yanzu haya zan dinga ba Yaya Hambali har nera dubu ashirin a shekara, ina nake da irin wannan kuɗin Bara'u?" Jijjiga kai Bara'u yayi yace.
"Maganar tana da tsayi, da girma Gwadabe. Ungo Bakonnan shinkaface, da masara, sai kuka da daddawa, da gyaɗa da Sakina ta saka muku, ku kama hanya. Zanzo da zaran ka dawo daga legas, sai mu tattauna. Ta yi haƙuri ita Iyabo kafin mu tsayar da mafita. Muje suna jiranmu"

Iyabo:.
Ni dai ina zaune kamar mutum mutumi . Ita kuma Sakina sai gargaÉ—i take yi mun akan duk rintsi kar in kuskura in bar Laila taci nasara a kaina, kana kar in kuskura tasan logona na zafin kishi dan zata wahalani dashi. Jinta kawai nake yi, dan banga abinda zaisa in zauna inuwa É—aya da Laila mu gauraya numfashi a É—aki tare ba. Duk wannan abinda akeyi Laila na tsaye a gefe da Samarin cikin gidansu Gwadabe tana hira, duk da nayi imanin hankalinta na garemu. Su Bara'u ne suka nufo mu.
"Tsuntsun soyayya to shikenan Allah ya tsare hanya. Aita haƙuri duk abinda yai farko ƙarshenshi yana tafe ko mu jima, ko mu daɗe. Allah ya yi miki albarka bisa bin mijinki da kike yi mun gode, in Allah ya saukeki lafiya Sakina zata zo da wuri ayi komai da'ita. Kuma a miƙa mun saƙon gaisuwa zuwa ga Iya Debisi, da Debisin"
Ameen nagode sosai." Iyakar abunda nace kenan dan muryata shaƙewa tayi." Mashin Sakina ta tarar mun na hau, ta ɗaura mun fantimotina a gaba, ta miƙo mun ledar hannunta.
"Amshi Atampa ce, kya ɗinka ki ƙara a kayan cin suna" Kafin in mata godiya har ta shige gidansu Gwadabe. Gwadabe ya hau mashin shi da Toye, da jakar kayanshi. Itama Laila ta hau nata aka ɗaɗɗaura mata kayanta muka wuce.
Ina zaune akan acaɓa tunani duk ya addabeni, na rasa inda zan tsoma kaina. In na bar gidan Gwadabe na tafi gidanmu, bani da tabbacin Iya Debisi zata amsheni, kuma ko bata amsheni ba, sai ta yi mun kwakwazo da tonon sililin da kab ƴan gida sai sun sam halin da nake ciki. Ƙauyan da mahaifiyata take Aure kuma sau ɗaya na taɓa zuwa, shima a lokacin ina da shekara goma sha biyu ne. In wuƙa za'a ɗaura mun bisa wuya ko sunan ƙauyan bazan iya tunowa ba. Kuma har ga Allah bazan iya zama da Laila a ɗakina ba. Ajjiyar zuchiya na sauke wanda yayi dai_dai da isowarmu inda zamu hau mota.
"Cikin gari ne, Alhaji, Hajiya kuzo ga mota" Cewar ma'aikatan tashar, suka yo kanmu suna rige_rigen sauke mana kayanmu zuwa wata cinyayyar Bus wacce ta ga duniya. Ni dai ina biye da mijina. Waje ya sama mun na zauna, Laila kuma ta zauna a jerin kujerun farko. Sai ajjiyar zuchiya nake faman yi. Ina hango Gwadabe ta taga yana biyan kuÉ—in motarmu, bayan ya biya ya shigo cikin motar.
"Ga waje na samama kamar zaifi cikin sanyi ko?" Cewar Laila, tana yi tana kashe muryarta kamar tsohuwar karuwa. Tsaki ya ja bai ce mata uffan ba ya wuto inda nake a baya, yana riƙe da Toye. Zama yayi a kusa dani baice mun komai ba, amman naji jikinshi yayi zafi kau halamun zazzaɓi. Idanu na lumshe hawaye suka zubo mun suka diga a tsintsiyar hannunshi, kasancewar a mugun matse muke a motar. Ɗagowa yayi ya kalleni, ni ko kaina na kallon waje.
"Iyabo so kike ki ƙarasa sukurkutamun lissafi kenan, ni da zan kwana a hanya ina tuƙi. Shin in ban samu sassauci a wajenki ba ina zan shiga in ji daɗi? Dubi yanda kike asarar hawayenki ke da baki da ishasshiyar lafiya" Da raɗa_raɗa yai mun maganganun. Zuchiyata ta tsinke, sai naji sababbin hawaye suna gudu a kumatuna. Allah ya gani bazan iya zama da Laila ba zaman da bansan irin sharrin da aka tanadar mishi ba tunda abun shiryayyene. Hawayena na share dan in sama ma Gwadabe ƴar nutsuwa. Amman sai na kulle idona kawai kamar mai bacci. Har motarmu ta fice a tasha, ta ɗauki hanya ban buɗe idandunana ba, banda niyyar buɗewa. Amman idanuna biyu zuchiyata na faman yi mun turiri. Ina jiyo muryar Toye yanai ma Gwadabe yarbanci, yana bashi amsa da yarbancin. Duk da ba iyawa yayi sosai ba, amman yana ƙoƙari wajen koyo, dan lokaci mu ka saka na musamman a tsakankanin magriba ruwa isha, ina koya mai yana maimaitawa in ya haddace sai ya rubuta. Wasu kalmomin da ƙyar yake iya furtasu. Muna nishaɗi sosai dan dariya muke yi sosai har tsakar gida ba za'a rasa jiyomu ba. A tsakanina da Gwadabe rayuwa muke yi mai aminci, muna ƙoƙarin bama junanmu farin ciki, da bama juna cikakken lokacin juna. Wannan irin zaman ke ƙaramun so da tausayin Gwadabe a ko wanne daƙiƙa. Shima hakan ke ƙara mishi sona. Bama iya ɓoye ma juna dukkan wani sirri. Haka naita tunane_tunanen daddaɗan zaman da muke gudanarwa da Gwadabe na. Zamanne danginshi basa so, sabida na fito a ƙabilar da ba tasu ba." Nasha wuya da wannan tsohuwar Bus sosai. Kafin mu sauka jikina yayi likib. Muna sauka muka samu abun hawa ya kawo mu har ƙofar gidanmu. Ni dai ana isowa na sauka abuna, ɗan mabuɗin ƙofar na ciro a jakata na buɗe gidan. Dukkanmu ko wacce ita da mijinta suna da safaya ki da mijinta. Ɗakina na buɗe na shaga, ban zauna a falo ba na shige uwar ɗaki na rufo ƙofar garam. Zama nayi a bakin gado, kamar am tsikareni na miƙe. Cikin ƙarfin hali na buɗe akwatina na soma loda kaya, ina jin Gwadabe yana kiciniya da fantimotan Laila .
Da gudu Toye ya shigo yana dariya, rungumeni tsam yayi. Tunda muka tafi Takai sai yanzu da muka dawo gida yaron ya sake. Dariya nayi mishi nace dashi.
Keeni ( Menene)? Na tambayeshi da yare.
"Kiyasi (Ba komai) Ya faÉ—a cike da nishaÉ—i. Muna cikin haka Gwadabe ya shigo da sallama.
Hirar sama data ƙasa na haɗe.

Ku meye shawarar da zaku ba Iyabo. Shin ta zauna da Laila a É—aki É—aya. Ko kuma tayi tafiyarta su Babala burinsu ya cika, shin inta koma gidan kuna ganin zaman zai mata daÉ—i. Sannan inta zauna tare da Laila me zai faru?
Ina saurarenku

MRS BUKHARI

https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm

NAMA YA DAHU...
ROMO ÆŠANYE

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

Lamba ta huÉ—u (4)

*(SANARWA DUKKAN WAƊANDA SU SAYI WANNAN LITTAFIN TAMKAR SUN TAIMAKAMA MARAYUNE DA IZININ ALLAH. DOMIN KUƊIN KAI TSAYE ZAI TAFI ASUSUNMU NA GIDAUNIYATA MAI SUNA AMILA FOUNDATION NE. GIDAUNIYAR TAFI ƘARFI WAJEN TALLAFAMA MARAYU, DA TAIMAKON MARASA LAFIYA, SAI KUMA TALLAFAMA ZAWARAWA DA JARI MUSAMMAN WAƊANDA MIJI YA MUTU YA BARI DA ƳAƳA. SIYAN WANNAN LITTAFIN TAMKAR TALLAFAMA MARAYU DA IYAYEN MARAYUNNE. KUZO MUYI TARAYYA AKAN AIKIN ALKHAIRI)*

*( KAR KU MANCE INA SAIDA TURARUKAN WUTA DA HUMRORI, DA DUK DANGIN ƘAMSHI MASU INGANCI NA MATAN KANURI. KANURI MUNE ƘAMSHI MEDUGURI GIDAN ƘAMSHI)*
Chapter 9 · 0% Book details