← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 237

Sashe 51

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gwadabe:.
Takai.
Tun a ƙofar gida ya hango motar Yaya Hambali a gefe guda, kuma ya ga Nazifi na zance da Nana ƙanwar Layla.
"To Gwadabe ni da Toye zamu wuce gida, in kun gama ganawa da Baba Magaji dasu Babala ka sameni a gida" Cewar Bara'u kenan.
"To Shikenan sai nazo. Ka isar da saƙon godiyata ga Sakina" Yana faɗar haka ya shige cikin gidan. Da Nazifi da Nana babu wanda ya kalli Gwadabe balle su gaisheshi. Zumunci ya riga da ya taɓu, ana rikice_rikice a gaban yara suna ji suna gani, sai su taso da raini da rashin ganin girman wanda aka watsar a gaban idanunsu. Wanda ake mutuntawa kuma a gabansu, sai su taso da ganin girmanshi ainun.
(Wannan kuskuren namu ne iyaye. Mu guji yin abinda bai dace ba a gaban yaranmu. Shi fa zumunci da haÉ—in kan haula babu abinda ya kai shi daÉ—i)
Gwadabe yana tafe yana girgiza kai, ciwo yake ji a zuchiyarshi sosai ta yanda zumuncin gidansu ya lalace. A falon Babala ya tarar da kowa da kowa. Babala da nata tawagar haka ma ƙannenta su Goggo Iyatu Baba Magaji yana tsakiya.
"Gwadabe kaine tafe da yamma haka?" Cewar Baba magaji.
"Nine Baba Magaji. Mun same ku lafiya?" Gwadabe ya bi kowa da gaisuwa Babala da Goggo Iyatu fur su ka ƙi amsawa. Baba Magaji yace.
"Zauna nan." Ya nuna mishi kusa da Yaya Hambali. Yana zama Yaya Hambali ya matsa, har yana share sangalalun hannunshi inda jikin Gwadabe ya gogeshi. Da mamaki Gwadabe ya dubeshi, shi kuwa ya zuba mishi Uwar harara.
"Marar kunya ji yanda kake ƙare mishi kallo sai kace sa'anka" Cewar Yaya Halima da bata fiye son a zauna lafiya ba dama" Baba Magaji ya yi mata daƙuwa tare da cewa.
"Ungo naki Yau ga mutuniyar banza. Shi Hambali baki ga share hannunshi yake yi in da jikin Gwadabe ya goga ba? Sai kace wani karfa. To magana dai ta ƙare kai Gwadabe meye hujjarka na nuna zafin ƙiyayyarka ga ƴar uwarka Laila? Dan naji labarin komai" Gwadabe ya ɗago kanshi yace.
"Ba ƙin Laila nake yi ba, face ƙin munanan halayanta abun ƙi. Na farko Laila babu wanda bai san ɓarauniya bace. Ko yanzu a taronnan in ba'ai da gaske ba sai ta raba wani da abunshi. Sannan da aure a kanta bata dena bibiyata tana turo mun da saƙonnin ƙauna ba. Wannan manyan dalilan yasa bazan taɓa iya auren Laila ba" Kafin ya rufe baki Goggo Iyatu da Laila suka fashe da kuka wi_wi. Ganin haka yasa Babala soma shessheƙar kuka itama. Baba Magaji yayi tsam yana bin kowa da ido ɗaya bayan ɗaya yana karantar yanayinsu. Yaya Hambali cikin zafin ranshi yace.
"Uwar ƴaƴan naka ma naga ɓarauniyace. Wacce iriyar sata ce bata tabka mana a cikin gidaba? Ai kai kasan komai tunda kai ke biyan kuɗin duk abinda ta sata. Ita ka zauna da'ita sai Laila jininka ce ba zaka iya aura ba?" Gwadabe yace.
"Wallahi ko tsinke Iyabo bata taɓa sata ba. Duk wannan kitumurmurar Laila ne. Ita ke satowa ta jefa ma Iyabo a ɗaki. Ni kuma ina biya ne dan ba son ganin ana tashin hankali nake yi ba"
"Babu shakka Gwadabe "
"Duk ya isheku haka ku saurara mun. Iyatu ku yi mun shiru ya isa haka nan" Sai da É—akin yayi shiru kana yace.
" Duk wannan kumfar bakin da kuke yi ba daidai bane sam. Layla dai kowa yasan mai dogon hannuce, tunda har maraɗi wajena Iyatu ta kawota ai mata magani. A lokacin hekarunta baifi goma ba. Sata kuwa da ta dinga yi a ƙauyannan abun yayi muni. Ina bayan Gwadabe na ƙin amincewa da auren Laila. Tunda kunce satarta shafar aljanune sai ku dage ku nema mata magani. Kuma da ace ni nasan irin tsangwamar iyalin Gwadabe da kuka yi da tuni nayi ma tubkar hanci tuni. Ko yanzu ma dan saki ukune a tsakani da ko kun ƙi ko ku so sai ta dawo tunda itama musulmace ahalul kitabi ma aurensu akeyi ballantana ita musulma gaba da baya."
Falon yayi shiru sai hawa da saukar numfarfashi kawai. Baba Magaji yace.
"Yaran dasu ta tafi ne Gwadabe?"
"A'a Baba Magaji bata tafi da su ba. Shi Toye yana hannun Bara'u Sakina zata ci gaba da kulawa dashi, za'a sa shi a makaranta. Su kuma ƴan biyun na kaisu wajen Tamu a can Abuja shi ya buƙaci hakan" Baba Magaji ya jijjiga kai yace.
"To Allah ya saka musu da alheri. Faɗuwa tazo dede da zama ni zan tafi da Gwadabe maradi yaje ga su Auwala can suna aikin haƙar zinariya, yaje shima ya jaraba wata ƙila arzikinshi yana can. Akwai ƙannenka mata ma a cikin gida, in kuka daidaita da ɗaya daga cikinsu kaga sai ayi tuwona maina ku yi zamanku a can. In ma aikin haƙar zinariyar bai maka ba akwai aiyuka da zasu dace da kai" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke kuma yaji daɗin hukuncin da Baba Magaji ya zartar, shi kanshi yana da buƙatar yin nesa da danginshi ya fita neman na kanshi. Kuma yaji aikin haƙar zinariyar ya kwanta mishi a rai. Ya je can maraɗi ya samu sababbin ƴan uwa da zasu so junansu.
Babala ba haka taso taron ya watse ba, amman bata da ikon cewa komai. Haka tana ji tana gani washe gari Gwadabe da Baba Magaji suka wuce maraÉ—i a bisa jagorancin Bara'u zuwa tashar mota.
Wannan shine dalilin barin Gwadabe Kano, ya koma maraÉ—i hannun wan mahaifin Babala"

JIHAR MARAÆŠI DAKE CIKIN JUMHURIYAR NIJER
Cikin unguwar Ali É—an tsoho.
Chapter 51 · 0% Book details