Sashe 82
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
GWADABE
MARAÆŠI
Da daddare sosai Gwadabe ya shiga gida. Dan Hadiza ma ta ƙaraci jiranshi, da sunturin zuwa ɓarayinsu harta haƙura ta kwanta.
"Kaine da daddare haka Gwadabe, ai daka raba tafiyar biyu." Cewar Auwala dake karɓama Gwadabe jakarshi. Sai da ya zauna daɓas a ƙasa yace.
"Kai dai bari. Allah ya iso damu lafiya. Da fatan na sameku lafiya?" A tare suka waiwaya inda Mammada ke bacci yanata gwarti. Dariya suka saki su biyun.
"Wannan matarshi ta shiga uku da wannan gwarti nashi" Cewar Auwala yana dariya. Gwadabe yace.
"Kai kuma taka matar ta shiga uku da shegen cin abinci ba" Harararshi Auwala yayi.
"Au to taka matar dame ta shiga uku, ko kai goma kake ba tara ba?" Dariya ya saka yace.
"Ga gajarta ga tumbi" Dariya suka saka. Gwadabe dai ya miƙe ya samu ya watsa ruwa yazo ya rama sallolinshi.
"Ga abinci Hadiza ta ajjiye maka. Tazo shashennan yayi sau talatin, gorin matan malam ne yasa ta haƙura, sai ta kawo abincin na ajjiye maka. Ammanfa tare zamu ci ato" Kai Gwadabe ya girgiza kawai. Ya jawo tiran silvern da kwanakin silven ke kai. Kwano na farko dafa dukan shinkafar manja ce da bushasshen kifi. Ɗayan ƙaramin kwanon kuma farfesun kazar Hausa ne, sai zoɓo cikin kofi me murfi na silver. Tunda ya buɗe abincin yaji yana wani irin ƙamshin spices na musamman. Da ya saka a bakinshi ji yayi tunda yake bai taɓa cin abinci mai daɗi da ƙamshin wannan ba. Yaci abincinnan da yawa, ragowar Auwala ya janye kwanon dan dole.
"Auwala Hadiza ce tayi wannan girkin amman?" Saida ya yagi naman kaza kana yace.
"Itace. Hadiza ba baya ba wajen iya dahuwa, damma bakaci miyar tuwonta ba. Lokacin da take gidan tsohon mijinta ina yawan kai mata ziyara kasanni da son sanwa" Kai Gwadabe ya gyaÉ—a yace.
"Amman mijinta ya tabka babbar asara daya saketa."
"Inji wa? Ko kai Hadiza tayi ma irin abinda tayi a gidan mijinta sakine zai tabbata a garete. Kai bata da daɗi fa wajen kishi. Kishinta na hauka ne. Kai dai kabi a hankali. Kuma Allah ne ya jarabceta shi yasa ma ta faɗo hannunka a lokacin da kai kuma tuni ka amshi soyayyar wata. Wallahi ba ƙaramin so Hadiza take yi maka ba da har ta amince da kishiya tun kafin aure ma" Gwadabe yayi shiru yana jinjina lamarin, tare da auna maganganun Auwala a ma'aunin hankali. Tsoronshi Allah tsoronshi tashin hankalin da zaije ya taɓa zumuncinsu. Kuma gashi ya kasance namiji mai son walwala da dauwakammen farin ciki a gidanshi.
Amman yaci alwashin yin bakin ƙoƙarinshi na ganin bai kunna kishin Hadiza ba a cikin zamantakwar tasu. Yanata tunanin irin zaman da zaiyi dasu su biyun. Da waɗannan tunanin gari ya waye haske ya maye gurbin duhu. Nan samarin gidan suka soma layin yin wanka domin fita nema. Masu goge baki nayi, masu goge takalmi nayi. Gwadabe yana zaune a dakali yana jiran fitowar su Auwala. Sai ga Hadiza ta ratso hannunta rike da babban tire. Ƙurama takunta kallo Gwadabe yayi. A tsanake take yin komanta babu bankaure balle hayaniya. Saida ta kusan zuwa inda yake sai ya miƙe ya karɓeta Sadiƙu ya ja tsaki yace.
"Aikin banza harara a duhu" Da Hadiza da Gwadabe duk suka waigo suka dubi Sadiƙu dake shirin ficewa a shashen.
"Allah ya shirya. Barka da isowa Dijena" Murmushi tayi kawai ta dubeshi tace.
"Ya hanya, ya ka baro kowa da kowa?" Fitowar Auwala ce ta katse amsar da Gwadabe yaso yaba Hadiza. Tiran kayan karin ya karɓe.
"Ina kwana Yaya?" Hadiza ta faÉ—a tana haÉ—iye dariyarta.
"Hadiza lafiya. Gwadabe zo da hanzari mu karya mu fice aikine damu sosai"
"To Dijena kije, in muka dawo saimu samu mu tattauna, in kuma baki tsarabarki. Amman naji daÉ—in yin tozali dake, kuma na yaba da abincin da kika girka mun" Farin ciki fal zuchiyar Hadiza tace.
"To godiya nake yi. Nima yanzu wajen aiki zan tafi, in ka dawo ma tattauna ƙila bakasan ina fita aiki ba. Sai kun dawo Allah ya tsare" Juyawa tayi ta kama hanya. Gwadabe kuma ya shiga ciki, suka gama karyawa tsab, aka fita nema. Basu suka dawo ba sai bayan isha yau sunyi dare. Suna dawowa Mammada yayi wanka ya tafi zance. Auwala kuma ya shiga cikin gida ya karɓo musu abincinsu. Bayan sun gama ci, Gwadabe yayi wanka sai ya tura yaro yai mishi kiran Hadiza. Bata fi minti goma ba sai gata. Yana hangota ya miƙe tsaye.
"Yau dai muje waje mu É—an zazzaga muna tafe muna zanca Uwar gida sarautar mata" Gwadabe shi ya soma fita Hadiza tabi bayanshi, sai da suka fita waje ne suka jera.
"Soma bani labari. Da safe kince zaki tafi aiki. Dama kina zuwa aikine bansani ba?" Murmushi tayi
"Na fahimci abun ya tsaya maka. Dan in ba haka ba ba hirar daya kamata mu soma ba kenan. Amman tunda ita ka zaɓa Shikenan zaka ji. Dama tun ina gidan tsohon mijina ni madam ce ( malamar makaranta) Ina koyar da yara ƴan primary school, fannin arabiya, nike ɗaukarsu Qur'ani da wasu littattafai biyu. to bayan aurena ya mutu ne, sai malam yaje da kanshi ya nemi alfarmar a bani hutu in kammala iddata. To ranar monday na ci gaba da koyarwa. Kaji abinda kake son ji" Kai ya jinjina yace.
"Ashe tare da Madam nake ban sani ba? Kinga in mu kai Aure zaki dinga koyar dani karatu in sha Allah. Yayi kyau ni bazan hanaki aikinki ba, dan Shafa ma tana aiki a Najeriya, kuma wanta ya roƙeni akan in akayi auren zata nemi aiki anan inta samu to." Lokaci ɗaya annurin dake kan fuskar Hadiza ya gushe. Shiru ya biyo baya, sai tafiya suke yi a hankali. Hardai shi Gwadabe ya kawar da shirun ta hanyar jefo mata tambaya"
"Yaushe su Malam zasu dawo ne?" A taƙaice ta bashi amsar.
"Babu wanda yasan ranar dawowar tasu" Shiru ya ƙara biyo baya, wani ɗan dakali Gwadabe ya gani sai ya dubi Hadiza yace.
"Zauna ki huta sarauniyar mata, takawarki Lafiya. Kinsan bana son ki wahala" Dole dai sai da ya dawo mata da farin cikinta, ta hanyar furta mata kalamai. Zama tayi tana dariya.
"To Hadiza nima inaso zuwa gobe in soma sana'ar dafa magunguna na gargajiya. Wanda ya shafi na basir, maganin rana, da shawara, zan dinga ajjiyewa a wajen aikinmu. Sai ki taya ni da adda'a, in Allah ya taimakemu sai kika sana'ar ta karɓeni" Sun jima suna taɓa hira, daga bisani kuma suka koma gida, shi yayi shashensu, itama tayi nasu shashen.
Kwana Gwadabe huÉ—u da dawowa, Baba Fhatsima suka dawo suma da daddare. A washe gari Malam ya tattare kan iyalinshi harda na gidan auren. Bayan Baba Fhatsima ta rarrabawa kowa tsabarshi, Malam ya soma magana.
"Maƙasudin wannan taron dai shine zaman lafiya da haɗin kai. Ni da kaina na roƙeku da ku daure ku haɗe kawunanku, ko dan haɗin kan ƴaƴanku. A ko da yaushe a cikin fargaba da damuwar rashin haɗin kan iyalaina nake kwana in tashi, lamarin da ya kusan haifarmun da ciwon zicciya. To a wannan karon duk macen data nuna taurin kai, ko ta hana yaran ɗakinta yin biyayya a kan dokikina to magana domin Allah zan sallameta. A yanzu in ganku kayukanku a haɗe shine babban abinda ke gabana." Take aka shiga ƙusƙus a falon. Malam yayi shiru yana kallonsu kafin ya ci gaba da cewa.
"Doka ta farko shine, dole ko wanne yaro a cikin gidannan da safe yabi ɗakunan matana kab ya gaishesu wajibine wannan, duk wanda ya saɓa zai gamu da abinda baiyi zato ba balle tsammani. Kuma tun yanzu inaso yarana in cakuɗesu a ɗaki ba kamar yanzu da suke a wawware ba. Ina nufin Mammada zai koma Ɗakin su Sadiƙu, shi Sadiƙu ya koma gadon Mammada, Sabitu kuma ya koma cikin su Zailani, shi zailani ya koma ɗakin su Safiyanu. Haka dai nakeso ya canja, domin su soma sabawa da juna tun kafin su yi aure. Sannan a yarana kab, da matan nawa duk me son wani abu daga gareni ga Tasi'u na ɗaura mishi duk nauyin. Wanda yasa girman kai sai ya haƙura. Shine magajina, Babban wa uba, dole a bashi matsayinshi" Baba asshi ce ta miƙe tare da cewa.
"Malam inada..."
"Dakata Asshi. Wannan ba malam ɗin da kika sani a shekara talatin baya bane. Ki zauna ban ba kowa izinin magana ba, asalima bana buƙatar maganar kowa. Duk matar da taji ba zata iya bin dokikin gidana ba, ƙofata a buɗe take" Jin irin yadda Malam yake faɗa sai kowa ya shiga taitayinshi. Malam ya dinga tsaro yanda yakeso ayi. Abinda ya kamata ace tun sanda yara suna ƙanana ya kamata ayi, shi malam sai yanzu akeyi. Kuma wannan ya farune a bisa yanda Malam ya kasa zama tsayayye a gidanshi. Ya sake ko wacce mace inta shiga da irin abinda take shigowa dashi. Shi kuma ya kasa taka burki a gidan nashi. A haka gidan ya cika da yara, a lokacin da yaran suke ƙanƙana babu irin rikicin da ba'ayi a gidan. Uwargidan Malam ce kaɗai mace mai haƙuri da kawaici. Itake ke iya kawar da kanta in matan malam nayi ma yaranta hukunci, kuma mafi akasarin hukuncin na son zuchiyane. Babu irin hawala da makircin da Baba Fhatsima bata gani ba a wajen Baba Asshi ba. Dan har takai ta kawo malam ko ƙofar ɗakinta baya iya kallo in ba ranar kwananta bane. Ta baza mulki tayi abinda takeso. Sai da malam ya sake auro mace ne Baba Fhatsima ta samu sassauci a gidan, domin kishi an kasafta gida biyu a lokacin. Malam kuma duk matar daya auro saita kasance itace ta gaban goshi a wajenshi, harma baya iya ɓoyewa, hatta cefanan ranar girkinta dabanne kawai. Ire_iren waɗannan halayyar ta maza ta rushe haɗin kai da zaman lafiyar haula da dama.
MRS BUKHARI