← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 237

Sashe 163

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ko Hassanan Hari ta ɗan dinga taimaka miki, tunda Jatau ya ba Dada ita ba'a barki ke kaɗai ba. Baɗɗo zata dinga zuwa dubaki akai_akai Allah ya ƙara sauƙi " Mu kai ficewarmu ba tare dana amsa a sauka lafiyan da Kishiyar Cubu take mana ba. Muna tafe da Uwani munata tattauna matsalolin da mata suke fuskanta a gidan aure, sai dai muce Allah ya kawo mana ɗauki. Da Sallama muka shiga gidan mai jego matan gidan ba kowa ko wacce ta tafi tallar Nono, sai wata tsohowa da inaga mai kula da mai jegonce. "Maraba, ku shiga tana ciki me jegon" Uwani ta ajjiye ƙunshin kayan hannunta muka shiga muka samu mai jego a zaune tana ba jaririyarta Nono. "Ah malama sannu da zuwa. Kinga kuwa yanzunnan Hama ta shigo taimun barka ta fita" Zama mu ka yi a tabarma ta miƙo mana jaririyar. Jikina a mugun mace nace. Allah sarki ta shigo kenan sannu mai jego" "E yau ta dawo maƙota ma nata zuwa mata barka, ƴan tsurku ma suna yi maganganu sai yawo suke. Baiwar Allah ina wuni?" Ta dubi Uwani da fara'a ta gaisheta. Ita kanta uwani jikinta a mace ta amsa. "Lafiya lau ya jiki Allah ya raya abinda aka samu" Ni dai gurum nayi ina mamaki Yaya Hamma yasan matarshi zata dawo shine bai sanar dani ba. Hmm maza ho halinsu sai su. Jaririyar na miƙa ma Uwani ina tambayar me jegon Gobe ne sunan ko?" "E gobe ne Malama. Naji anata labarin magungunan da kika kawo da kayan kwalliya nima dan Allah inaso malama tunda nima ɗalibarki ce." Murmushin dole nayi nace. To babu damuwa, gobe zan shigo da safe taya aikin abincin suna zan tawo miki dashi. Akwai ɗan kunne da sarƙa fella_fella in kina so" MRS BUKHARI B4B
Chapter 163 · 0% Book details