Sashe 185
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
duka kaÉ—an na rage. Washe gari sassafe ta yi mana sallama ta kama hanya, kafin dai ta tafi ta faÉ—amun watannin daya rage haihuwarta sabida kintata zanyi in tawo tunda bamu da network. Haka rayuwa taita tafiya su Taiwo sukaita bani wahala in wannan ya warke ciwo sai wannan ya kama, canjin ruwa da zaman Æ™auye duk saiya sa suka rame ga Æ™uraje caÉ“a_caÉ“a ya fito a jikinsu babu masaka tsinke. Ranar da suka cika wata guda a ranar Bara'u ya tawo ya kwana a gidan Dada washe gari suka wuce. Na haÉ—ama yaran goma sha tara na arziki. Taiwo Atampa biyu na bata. Na kulle atampa biyu daban na matan Gwadabe. Toye da Kahinde nasa Uwani ta sai musu kaya kala bibbiyu Æ´an kanti duk da dai irin na Æ´an Æ™auyene amman dai na siya musu. Na siya ms Iyabo kaya itama. Dada ta haÉ—a musu tsarabar Æ™auye, hakama Yafendo, da su BaÉ—É—o. Aka dai haÉ—a musu tsaraba rigijib harda zabi huÉ—u aka haÉ—asu dashi wai suyi kiwo. KuÉ—i masu yawa Bara'u ya miÆ™o mun da kaya cikin babbar Æ™atuwar leda yace wai inji Gwadabe yace a bani kuma yanayi mun barka. Allah sarki Gwadabe. Dan Allah Bara'u kace nagode Allah ya saka mishi da Alkhairi " "Babu komai ai tsuntsun soyayya. Naso mu tawo da Sakina ma amman tayi nauyine sosai haihuwa ko yau ko gobe. Amman wata rana kwatsam zaki gammu." Allah sarki Sakina Allah ya raba lafiya. Nima indai na shigo kano nanda wata É—aya in sha Allah zan shigo Takai É—in da izinin Allah." Da haka mu kai sallama ya tusa yaran a gaba suka tafi. Mu kuma rayuwa taci gaba da garawa damu. Shayarwa tasa nayi kyau na ciccika sosai. Hankalina ya kwanta sosai a tafiyar Hama gida har ga Allah ni dai saida nayi fatan inama karta dawo. Gabaki É—aya gidan da matan gidan duk sun sake. Ƴan biyu kuwa suna ganin gata a wajen Yafendo da Æ™annen Yaya Hamma. Haka dai naci gaba da shayar dasu cikin tsabta da lafiya. Abun mamki nayi Æ™iba sosai baku ganni ba, sabida Æ´an biyu suna da tsotso sai nima cin abincina ya ninka, dani dasu duk mukai É“ul_É“ul damu." Yau tun safe na tashi da shirin zuwa dubo Dada. Da wuri naima yara wanka nayi mana wankin kayanmu na shanya, na goya Æ´an biyu na fito. Æarayin Yafendo na nufa nai mata sallama inaso in je dubo Dada daga can zan leÆ™a Cubu dan ance bata ji daÉ—i ba." "Sai kun dawo Æ™ila anjima nima in leÆ™o gidan in duba Adda dan jiya ciwon kai ya sata a gaba" Ni banma sani ba sai yanzu da nake ji. Ayya ai kuwa zan tafi mata da Æ™wayar bature ta haÉ—iya. Sai mun dawo Yafendo" Fitowa nayi duk inda na wuce sai na tsaya an gaisa sun ga Æ´an biyu kafin in wuce. Ga rana sosai a garin zafi akeyi sosai safiyace amman har rana tayi zafi. Sai naji idona wannan marar ganin ya soma ciwo har yana zubar da ruwa. Da sallama na shiga gidan Dada ina haki abunka da masu kitse. A tsakar gida na samu Dada a kwance Yusufu na mata fifita Kari kuma tunda ban ganta a tsakar gidanba nasan bata nan an tafi talla. "Jabu kune da safe haka? Saifa da nace da BaÉ—É—o ba sai sun faÉ—a miki ba shine saida ta faÉ—a" Zama nayi a kan tabarmar, na sunto Æ´an biyu da suketa kukan zafi. Yusufu ya karÉ“i É—aya Dada ta tashi zaune itama ta miÆ™o hannu in sa mata daya. A_a Dada kiyi fama da kanki Usaini nauyine dashi ga tumbuÉ—i" Murmushi tayi tace. "Kema lokacin da nake koyonki ai kin fishi girma da nauyi. Cika bayana dam kike yi. Duk inda na wuce sai an kalleni, har ciwon Æ™irji saida ya kamani a goyonki. MiÆ™o shi" Murmusawa nayi. Ni dai Allah ya jarabceni da tausayin Dada. Sanyin muryarta kaÉ—ai ka iya cika idona da ruwan Æ™walla. Usaini na miÆ™a mata na tashi na É—ebo ruwa a randa na É“alla mata fanadol biyu. Na bata ta sha ta kwanta. Na samu Yusufu ya riÆ™e mun yaran nayi mata kwalima, na wanke mata tufafinta tas na share tsakar gidan. Bani na bar gidan ba saida na yi mata miyar tumatur na aika Yusufu ya siyo mun nama da shinkafa. Sai wajajen biyun rana na nufi gidan Cubu. Da sallamata na shiga cikin gidan abun mamaki kishiyoyinta da girmansu wasu da yaransu a gidan miji ma amman suka saka Cubu a gaba uwargidan ta zauna a Æ™aton cikinta sai ihu take yi. Ragowar kishiyoyin suna ranÆ™washinta. Subhanallaah me zan gani kasheta zaku yi ko me?" A firgice suka juyo suka zuba mun idanu. Hawaye suka gangaro a kumatuna. Cubu numfashinta sai kokuwa suke yi ita dashi" Mrs Bukhari