← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 237

Sashe 196

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

sake yin kyau fiye da lokacin sunan Cubu da ta ganni, na kuma ƙiba. Damuwa to ɗaya ce a yanzu a raina rashin dawowar Yaya Hamma. Yaran na sunto a bayana idanunsu biyu na miƙa ma Yafendona ɗaya, na miƙa ma Yafendo ɗaya. Na gaishesu da ladabi. Daso ta harareni naga har yatsa sai da ta ciza. Ni dai na kada baki na gaisheta ta amsa a daƙile dai. Ni ko ko a jikina. "Kin samu su Toyosi lafiya, ya kika baro uwani?" "Lafiya lau Dada. Iyaa tace a gaisheku, su Iyaa Beji duk suna gaisheku. Uwani kuma ta samu ɗiyarta mace Fatima" "Allah ya yara, ina amsawa" Taja bakinta ta tsuke. Yafendo tace. "Hama ma ta haihu yau kwana shida kenan gobe suna. Abinda ake tattaunawa kenan ma kika shigo kika sakemu. Sai ki shirya goben aje sunan dake in Allah ya kaimu. Amman sai dai kuyi fitar sassafe ƙauyen da ɗan tafiya" Allah ya raya. Me muka samu Daso?" Na tambayeta dan itace sa'ata. Su inna tambayesu kamar nayi rashin kunyane. A taɓe tace. "Mace ta samu" To Allah ya rayata da imani. Bari inje in ɗan huta in rama sallolin da ake bina. Gaga_gaga washegari muka tashi da kacaniyar shirin zuwa suna. Ni dai har ga Allah banso ayi tafiyar dani ba gudun wulaƙanci, ga dangin Hama duk zasu ganni ƙila aita zunɗena. Kaya masu kyau sababbi fil na sama ƴan biyu. Nima na ɗakko sabuwar atampata na saka na ɗauko ɗankunne da sarƙana na saka, na saka takalmi da jaga, zobe, awarwaro duk na saka na fito shar, dama kunsan nace muku nayi kitsona, na yi ƙunshi. Sai suka sake haskani. Na goya Hassan, Safiya ta goyamun Usaini. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Chapter 196 · 0% Book details