Sashe 26
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
roƙon da nake yi miki kiyi taka tsantsan kuma ki iya takunki, kisa ma Laila ido sosai, kinsan na faɗa miki ƙasurgumar ɓarauniyace." Kuka na fashe dashi. Kana nufin a haka zanci gaba da zama tare da kai anai mun kallon ɓarauniya, harma duk abinda aka nema aka rasa sai na biya? Gwadabe haƙurina ya ƙare ni na...." "Kul kika bari mala'ilun Allah su yi fishi dake, Allah yayi fishi dake. Iyabo wallahi dukkan wannan abun so akeyi a samu a ukun da da kanmu zamu ji mun haƙura da junanmu, abinda suke so kenan. Nayi duk iya iyawata in kare ki, abun yafi ƙarfinane bazan tsaya ina jayayya da Yaya Hambali ba, domin uba ne, a kafaɗunshi muka girma, Balle kuma Babala da goggo Iyatu. Kiyi haƙuri ni zan dinga biyansu duk abinda suka ce an sace musu." Ya batun korarmu kuma da Baban Nazifi yayi, ba gara mu bar gidan ba, tunda in bana gidan ba mai cewa nayi sata?" Kanshi ya dafe kafin a tausashe yace. "Babala tace ko bayan rants bata yafe ma duk wanda ya bar gidannan ba. Ashe Yaya Hambali da Yaya Harisu sun sai gidajen su Malam Audi, da gidansu Baturiya, wata mai kamawa ma za'a soma aikin fashe katangun a haɗe gidajen. Kinsan bikin Nazifi da Laraba ya ƙarato, nima fa duk yau nake jin labari. Nazifi zai zauna a cikin gidannan da matarshi. Itama Laraban a cikin gidannan zata zauna. Ai kinsan Ilum ɗakin Goggo mai Yaɗiya ko? To shi zata aura, Yaya Hambali zai ɗaukeshi aiki a kasuwa. Ni dai Iyabo abinda nake so dake shine kar ki sake fita tsakar gidannan sai in fita daga gidan zaki yi, ko ban ɗaki zaki shiga. Su girki, wanke_wanke wanki duk kiyi a ɗakinki, kiyi haƙuri damo.." MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI