Sashe 58
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Ni kuma a wannan lokacin sakin kawai nake buƙata ba shanayen banza ba. Sai da mu kai sallar isha a gidan. A ɗakin Yafendo muka haɗu mu ka ci abinci anata hira, maza kuma suna waje suna shan iska. "Cubu je ki kira Hamma a waje ya raka su Daso guda, kuma sai ku kama hanya tunda ga Yusufu sai yai muku jagora" fitar Cubu ke da wuya sai gata Yaya Hamma na biye da'ita. "Dada gani" Ya faɗa da murya mai kauri. Yarinyarshi dake hannun uwarshi sai ɗaga mishi hannayenta take yi halamar ya dauketa Hama ta miƙa mishi yarinyar ya ratayeta a kafaɗarshi. "Su Daso zaka raka gida tunda dare yayi ." Ɗan murmushi yayi kawai kafin yace. "To Dada su sameni a waje sai mu je. " A tsaye ya ɗan yi ma ƴar tashi wasa ya miƙa ta hannun uwarta ya fita. Muma mu kai ma Yafendo sallama muka fito, suma su Yusufu suka nufi hanyar komawa gida. Shiru_shiru mukaita tafiyar. Duk cikin mu ukun kowa da abinda ke azalzalar zuchiyarshi. Abun mamaki har muka isa gida ba wanda yayi ko tari. A ƙofar gidan muka haɗu da Jatau da Burodami Debisi sun kafa sun tsare suna jiranmu. "" Ƴar halak ta ƙi ambato ka ganta ma. Jabu mun fi mintu talatin muna jiranki anan wajen" Hannu Yaya Hamma ya miƙa musu suka gaggaisa, sai naga ya kuma haɗe ranshi. Ni da Daso dai muna tsaye, Allah cikin ikonshi sai ga Manga shima ya tawo taɗi shi da abokinshi. Yaya Hamma ne yai ma Daso jan ido ta je wajensu. "Jabu ki je ki saurareshi, ni zan jiraki a wancan wajen itaciyar, inason mu yi magana ne" Yaya Hamma ya faɗa a sanyaye. To Yaya Hamma" Iyakar abinda na faɗa kenan. Burodami Debisi yaima Hamma godiya, ni dai na bi bayanshi dai muka matsa gefe haka. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE