← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 237

Sashe 181

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bara'u ma sai kallonki yake yi yaga duk kin lalace kin koma baƙauya fitik, jibi wata atamfa ruwan kwara_kwara a jikinki" Banso inyi dariya ba amman ni da Uwani muka tuntsure da dariya. Sallamar Yafendo Jabu, da Dadane ya katse mana hirarmu. Maraba Yafendona, Dada sannu da zuwa" Tabarma na shinfiɗa musu a gefe suka zauna muka gaggaisa, Uwani ta miƙo musu yaran. Sai ga Yafendo dasu Toye da Baɗɗo sun shigo. "Kunzo ganin mazajen naku kun kasa haƙuri sai gobe. Dada inyalli jam?" Dada ta yi ma Yafendo murmushi aka gaggaisa, suka ga su Toye tare da shi musu albarka. "Jabu wannan biyun naki macen naga sai ƙananun kuka take ɗanyi dai, tana ambaton Mama." Da yarbanci na kirata abun mamaki sai gata tazo na ɗaurata a cinyata nace. Menene kike kuka Taiwo?" Sai take ce mini ita gida zata tafi wajen Babanta. Nan dai Yafendo tai mata dabarar ta bari sai gobe sai a kaisu. Su Dada dai su kai mana sallama suka fita. Ƴan biyu sai sheƙa baccinsu suke yi, ruwan nonona inaji yana zuwa. "Iyabo ni ɗinnan fa a cikin damuwa nake sosai. Ni da ba dan wannan cikin ba, da kuma ina tunanin wahalar da yarana zasu sha a hannun matar ubansu ba. Ke da auren zan ajjiye wallahi in huta, na gaji matsaltsalu iri da kala. Ko kinsan yanzu ni da Hafizu sai gani sai hange baya iya yin mu'amalar Aure dani abun baya yiwuwa. Tun yana so, harya haƙura. To daga baya ma aka dena lissafin wani rabon kwana, sai sanda yaga dama yake shigomun. Dama kuma na daɗe da korarshi a aiki, amman ya samu wani Alhaji ya sai mishi victira yana lodin ƙauyuka. To akan matarshi ya tare, ni dai da yarana sai dai fa in ciyar damu. Ɗan sauƙin dana samu ma kasuwancin Allah ya dafa mun mun haɗe shagunan ma duka biyu na zuba kaya sosai, na ɗauki su Ummi aiki tunda su zuchiyarsu ta mutu" Ajjiyar zuchiya na sauke nayi ƙuri ina kallon uwani harta dire maganarta. Rayuwarnnan bata tafiya face da tarin tulin matsaloli sune abokan tafiyar rayuwar. Ke ina ke ina wani barin gidan aure kina da gidanki, kina da sana'arki? "A'a ni ƙuncine bazanta ƙunshewa ba Iyabo. Ke kinsan bani da daɗi. Rannan anyi haihuwa a salam layinmu. To mai haihuwar ƙawartace, ni kuma yarinyar kostomatace dan nina haɗa mata kayan haihuwa. Kinsan yarinyarnan saina shiga na taddata tana ba ƙawayenta labarin ai tayi asiri ta kashe na Hafizu gaba a gidana bashi da fus. Kaza_wa_kaza dai ni kuma sai gani. Zagewa nayi na kirɓata wallahi, a daren kwana muka yi ni da Hafizu muna rikici. Ke nifa bazan mutu Lokacin mutuwar tawa batai ba." A lokacin dai sai haƙura da hirar muka yi, muka kwanta. Washe gari da safe muka ɗaura. Ina zaune fitowata daga wanka ban daɗe ba kenan. Yafendo Jabu ta gama ma yara wanka ta muƙo mun su, na zura musu nono suka hau sha. Baɗɗo ta shigo da tuwo a kwano yaji yajin daddawa da manshanu sharɓan. Baɗɗo an kaima Bara'u abun karin da Uwani tayi mishi?" "Ai gashi nan ma a tsakar gida fitowarshi daga wajen yafendo kenan. Yace in kiraki ke da Adda Uwani shi zai koma" Yafendona tace. "Jeki maza. Baddo ke kuma ki fitar da ruwan wankan da kayan yaran ki wanke. Ni sai in zauna da yaran" Ajjiyesu nayi duk sunyi baccima, na saka takalmi da mayafi muka fito. Bara'u wai harka fito sai tafiya?" Taiwo na maƙale dashi gam. "Wallahi ai naso asussuba ma in koma gaskiya. Iyabo Allah ya raya, ni zan koma sai nan da sati huɗu zan dawo ɗaukarsu. Ga Taiwo ta ɗaneni so take ta bini fa" Kuɗi ya zaro nera dubu huɗu ya miƙo mun. Uwanice tasa hannu ta karɓa. Muka haɗa idanu da Hama wacce ta kafa ta tsare tana kallonmu "A siyi sabulu ayi wanki. Ni zan koma. Allah bashi in mai gidan ya dawo a gaisheshi" Godiya mai tarin yawa nayi mishi, na bashi manshanu soyayya da nono kindirmo cikin jarka, harda zakara nasa Baɗɗo ta kama aka ɗaure mishi. Nace ya kaima sakina. Godiya yayi ya fice, da ƙyar ya ɓanɓare Taiwo a jikinshi. Yarinyarnan tafi awa tana kukan banza harda birgima. Ina jiyo Hama na zage_zage a tsakar gida. Yafendona ce tai ta rarrashinta fa da ƙyar tayi shiru. Can maƙota suka shiga tururuwar zuwa, tare da dangi na kusa gida ya cika tab da ƴan barka. Kunsan ƴan biyu akwai farin jinine. Haka aka dinga zuwa ganin ƴan biyu. Kab zuriyar su Dada babu wanda yake da ƴan biyu sai nice na kafa wannan tarihin. Irin baƙin cikin da Hama ta dinga nunawa abun ba'a cewa komai. A cikin ruwan wankan jariran tasan yadda tayi ta jefa allurai biyu, Yafendona tana sa Hassan allurar ta caki duwawunshi wajen ya fashe sai jini. Dani da duk masoyana hankalin kowa ya tashi. Nifa tsabaragen ruɗewa fisge yaron daga hannun Yafendona nayi na shiga karanto mishi duk adda'ar da tazo bakina. Matan gida suka cika a ƙofar ɗakin kukan yaro har maƙota wallahi. Ana zubar da ruwan wanka saiga allura guda biyu. A masai Baɗɗo ta jefa alluran. Anata mana Allah ya kyauta, amman fa alkinkimar ko a tsakar gidanma bata. Sai sabon ruwan wanka Uwani ta ɗaura tayi zamanta har ruwan yayi zafi ta juyo ta kaawo ma Yafendona. Kafin magriba ba sai jikin yaro ya saki ba, ga zazzaɓi ya rabkeshi. "Iyabo ina zuwa. Bari kiga in koya ma matarnan hankali" Da sauri najawo Tabalbalin nace. Kul cikine da'ita kar a yi ta Hajiyayye da Yaya Uwa ( NA FAƊO DAGA BENE.. NA ZARCE RIJIYA) Batta a niya bi a niya. Na tofesu da adda'a babu komai. Yaran da ko duniyar ba'aso suka zo ba. Da Allah dai na haɗata har suka fito duniyar. Yanzunma na haɗata da Allah. Ammam in wani abun ya samu ɗana, ko kuma ya mutu baki ɗaya. Zanyi abinda ni da Hama sai dai mu yi mutuwar kasko" Dawowa Uwani tayi ta zauna. Ni dai ina riƙe da ɗa ko nono yaƙi kamawa. Abu fa kamar wasa bamu runtsaba a gidannan sai jefin asuba dana tuno bari in mishi karatun Qur'ani a kunne. na soma karanta mishi wallahi sai yaro ya sauke ajjiyar zuchiya, a_a ba sai bacci ba. Sannan ne hankalinmu ya kwanta. Ni dai dana soma baccin wahala saida na kai hantsi. A hakanma Cubu ce ta tasheni sunzo da yaran Baffa Musa. Yafendona tace. "Ai gara ki daure kije kiyi wanka. Me jego bata zama da yinwa a jikinta. Wankan na daure naje nayo, abincinma tutturawa nayi babu dai daɗi. Har dai zuwa rana yaran suna lafiya ƙalau babu wata matsala. Baɗɗo da Cubu ne suka goya biyu aka kaima Dada su ta gansu dan ba zata iya zuwa ganinsu ba a kunya irinta fulani. Dawowarsune Baɗɗo take faɗamun wai taga mahaifinsu a wajen Dada yana rarrashinta ta koma. Kafin in bata amsa sai ga sallamar gungun ƙawayen Hama sun shigo, harda ita da tun a tsakar gida da muka haɗu ban sake ganinta ba sai yanzu. Uwani ta miƙa musu yaran suka amsa. Wata zabiya a cikinsu tace. "Ba shakka yara sak ubansu, Amarya daga zuwa taci gida" Ta faɗa tana dariya kamar ba magana ta cusa mana ba. Uwani ta kalleta tace. "Taci gida, taci miji ba. Saima kunga ta sake haifo wasu ƴan biyun ko ƴan uku du maza tukunna. Marasa mutunci fitsararru zaku zo har ɗaki kuna watsar mana da magana." Ƙwace yaran daga hannunsu tayi tace. "Ku tashi ku fice mana da gani tatattun marasa tsoron Allah. Ke kuma Hama na dawo kanki da ba dan kina da ciki ba da saina miki ɗan banzan duka kafin in koma garinmu, Jabu ƙyaleki take yi kinsan karonmu ai babu daɗi" Hama ta taɓe bakinta ta miƙe tsaye da ciki. Ƙawayenta suka tashi tsaye suma. "Jabu kina ji ƙawarki na cin zarafin mutane kin kasa dakatar da'ita? Nifa ban gane me kuke nufi ba kuna dai son ƙalamun sharrine ni bani na saka allura a ruwan wankan yara ba. Kamar yadda kuma Jabu ta haifi maza ai nima abinda ke cikina kenan. Hamma kuma nawane kowa ya sani. Uwani ki bar ganin a baya kinci galaba a kaina ki rikeshi ya zame miki makani. A yanzu nafi ƙarfinki. Hafsatu mu fitar mata a ɗaki" Ni dai da uwar harara kawai nabi bayanta naja dogon tsaki nace. Jahilar mace wacce bata san kanta ba" Harta fita suka juyo a tare ita da ƙawayenta. "Ni kike kira da jahila? Oho dai da jahilcin nawa muka haɗa miji, mijin da yai miki gata harda uwarki da ƙannenki tunda shike ciyar dasu abun kunya" Da sauri na miƙe tsaye na nufi Hama ni da Baɗɗo. "Yayi kyau Hama sannunku da naimam fitina, ke dai kin kasa kwantar da kanki ku zauna lafiya ke da abokiyar zamanki, yanzu abun ya kai har Addan tawa kike zagi. Dan Hamma ya ciyar da'ita shine abun gori shi da yar mahaifiyarshi. Kul kika sake yinƙurin zagin Jabu a gidannan dan in ranki yayi dubu sai ya ɓaci wallahi." Yafendo ta ƙare mata tanadi tas, dalilin da yasa na koma ciki kenan. Ammam na ƙudure a raina na daina ragama Hama kwata_kwata a gidannan, in dai ta cakaleni zan mayar mata kamar yadda mudubi yake maida hoton fuska. A cikin zaman bakwai ɗinnan ba fa ƙaramin rikici aka dingayi da Hama ba tata ɓurza babu wacce ba'aiba. Komai masifa ta takurama su Taiwo sosai ni fa sai gidan Cubu aka kai yaran dan tsabaragen fitinar Hama. Ana jibi suna Uwani da Baɗɗo suka shiga kasuwa ranar kasuwa suka siyomun wasu kujeru marasa hannu dogaye biyu da wan_wan biyu, sai gadon katako waya goma sha biyu, da katifarshi. Uwani ta sai mun labule da ɗan abubuwan da baza'a rasa ba. Harda atampa kala biyu, sarƙa da ɗan kunne da takalmi daman uwani ta tawo mun dasu, da tulin kayan jarirai masu kyau. Dan ranar dasu Baɗɗo suka wanke kayan saida ya cika igiyoyin gidan kab. Ba Hama kaɗai ba fa har daga maƙota zuwa kallon kayan akeyi, dan basu taɓa ganin kayan jarirai masu yawan haka ba a cewarsu. Hama kuwa yi tayi
Chapter 181 · 0% Book details