Sashe 126
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
mai fenti me kala duk farar ƙasace a shafe a nasu bukkar, azara ai ke kika siya da kuɗinki Iyabo. Ke dai zuwa goben dai ki kwantar hankalinki Amarya a gidan Hamma." Dariya muka saka dukkanmu nace. Baki da dama Uwani Uwargida a gidan Hafizu, Hafizu ikon Allah" Wata uwar harara ta watso mun. Na sake fashewa da dariya. Baɗɗo tace. "Bari in kawo muku fura da nono Adda" Ta fita sai gata da Fura da nono cikin ƙwarya, tayi mana sallama ta fita dan a lokacin goman dare zai iya yi. Muna daga gado muna hira da Uwani muna shan fura. "Iyabo nifa harna hango miki alkhairan kasuwanci. Wallahi in Allah ya dafa miki me kuɗi zaki zama, kita sare_sarenki. Nima kafin in tafi zan sari man shanu. A hannun Baɗɗo tunda yanzu lokacin arharshi ne." Mun daɗe sosai muna tattaunawa kafin bacci yayi awon gaba damu. Washe gari aka kuma tashi da hatsaniyar biki. Uwani tun wurwuri suka shiga gari ita da Baɗɗo. Daga ni sai Anti Ramata a ɗakin, sai wajajen takwas na safe matar ƙanin Hamma ta kawo mana shayi ruwan bunu da ƙaton biredi sai ƙosai cikin kula. Ni banci biredin ba ma, ƙosai biyu naci sai ruwan bunun dana sha. Cubu ce ta leƙo ɗakin tace. "Adda na kai miki ruwan wanka ki je ki watsa" Dama tuntuni wankan nake son yi inje mu gaisa da Yafendo, da ragowar matan gidan. Hijabi na saka na fita hannuna riƙe da kwandon soso da sabulu. Ruwan wankan yana cikin sabon bokitin ƙarfe in leƙa ruwan sai naga wani garin magani yana yawo a cikin ruwan. Baki na buɗe ina mamaki, ba shiri na kelayar da ruwan na fito da bokitin a hannuna. Da hannu na yafito Cubu dake gindin murhu. Tana ƙarasowa na damƙa mata bokitin. Ungo ki zubo mun wani ruwan zafin. Kafin ki zubo ki ɗaurayo bokitin sosai. Wancan zamewa nayi ya zube" Karɓa tayi ta zubo mun wà ni ruwan nayo wanka zuchiya cike tab da fargaba. Ina fitowa na kintsa cikin riga da siket na atampa, na yi kwalliya sama sama na yafa mayafina wanda na bishi da turaren feshi. Ina fitowa tsakar gidan ido ai sai ya dawo kaina. Anan zan dakata sai Allah ya kainmu gobe.