← Book details Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 237

Sashe 22

Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kudaɗe na soke a giyo. Mu je ki rakani in yo cefane kinji in ɗaura abincin rana, dan Gwadabe suna asibiti da Babala, bansan ko gado za'a kuma basu ba, ko zasu dawo gidaba, ya kamata in gama abinci da wuri" Fita a gidan mu ka yi muna tafe sai tauna matsalolin dake ci mana tuwo a ƙwarya muke ta ta faman yi. A wajen wata beyerabiya mai kayan miya da niƙa na sai tumatiri da albasa da attaruhu, rabi na gyara a wajen na wanke ta niƙa mun, dama mun fito da robar fenti, rabi na ƙunso abina na sayi ɗanyan kifi shawa da su maggi a wajenta, Uwani ma na sai mata haɗin kayan miya na ɗari da hamshin, maggin hamsin, man hamshin, sai kifi ɗanye na hamsin, sai murna da godiya take yi mun. Muna dawowa gida na shiga aikin abinci, ni ina jajjage Uwani na yi mun tsintar shinkafa. Matan gida sai shewa suke yi, ko wacce tana girkinta a ƙofar ɗakinta, Yaya Haula kuwa kajine cikin tukunya take ta aikin musu jar suya gidan ya karaɗe da ƙamshi, Suwaiba kuma kifi take soyawa sukumbiya ɓula_bula, ga jajjage kayan miya tana yi, ga alayyawo ta baje akan tabarma. Kullum su kam a cikin cin daɗi suke kullum baren ma Yaya Haula tunda mijinta kusan shine mai kuɗin familyn baki ɗaya ma. Tukunya na ɗaura na zuba mai na jefa ɓararriyar tafarnuwa guda, man yana yin zafi na zuba jajjagena, na wanke kifina tas na tsaane a kwando, ai sai matan gidan baki ɗaya kallo ya dawo gareni kawai dan hakan sabon abune a tukunyarmu gaskiya, barmu dai da yin fara da mai, ko tuƙa amala da miyar ewodu ko mai babu. Yaya Haula tace. "Lallai bana abun arziki muma ya biyo ta layin gidanmu har mun samu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta" Sai suka saki shewa dukkansu, ni kuwa ko in kula na gama tsayar da sanwar girkina nasa ma uwani hannu muka ci gaba da tsinta. Sai bayan azahar girkina ya sauka na juye tumaturina a tukunya na mayar kan gawayi. Waya na ɗauka na kira Burodami Debisi nace inason nama na dubu biyu dan Allah ya turo yaro dashi. Bayan mun gama cin abinci sai ko ga yaro da nama cikin ƙaramar baƙar leda dam harda kayan miya cikin leda mai zane, yace kuma in bar kuɗin naman. Allah sarki ɗan uwa mai daɗi kiranshi nayi na dinga yi mishi godiya, ina ajjiye wayar sai ga kiran Gwadabe ashe sun dawo Yana ɗakin Umman Nazifi. Abinci na tafi musu dashi, na gaishe da Babala da jiki, na ɗan jima a ɗakin kafin na fito." MRS BUKHARI
Chapter 22 · 0% Book details