Sashe 228
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Usman
"Allah ya kyauta mata halinsu ai sai su. Bari in shiga in watsa ruwa"
"Yaya Amaryar fa to?"
Har Usman ya juya ya juyo yace.
"Tana can gida taƙi biyoni."
Dariya suka yi duka. Ɗakinshi ya wuce yana nan tsab komai a goge a gyare, an sake labule, an sake zanin gado, banɗakin ma daya shiga s gyare yake a wanke yanata ƙamshin sabulun wankin tayil.
Yana wanka yana tunanin Iyabo har ya fito tunaninta bai barshi ba.
Zama yayi ya goge jikinshi ya ɗan shafa cocobutter dinshi yabi jikinshi da turaren boss. Rigar bacci mai dogon wando ya saka lokacin ƙarfe taran dare yayi. Kanshi ya girgiza kawai ya fito babu kowa a falon wuta da kayan kallon falon a kashe suke.
ÆŠakin Faisal ya soma buÉ—ewa yana kwance yana danna wayarshi.
Murmushi suka sakarma junansu dashi da saurayin É—an nashi mai tsananin kama dashi.
"Ummanku wai tananan kuwa, ni fa ko É—uriyarta banji ba?"
"Abba tananan. Nima tun safe ban sata a idanuna ba, amman su Biba suna tare da'ita."
Shiru yayi kawai ya rufe ma yaron ƙofa. Yana tafe yana mamaki har zuwa ɗakin Biba da Abida. Babu kowa a cikin ɗakin kan gadonsu da ƙasa duk kayane harda plate da suka ci abinci a ƙasa.
"Wannan yara sai nayi maganinku"
Daga ɗakin Suhailat yake jiyo karaɗin Biba, yasan dai Abida tana ɓarayin uwarta dan da wuya ka ganta a ɗakin Suhailat. Yana shiga Suhailat dake kwance tana karanta littafin turanci ta wani haɗe rai da kuma dariya suke yi.
Da Biba da Anisa ƙanwar Suhailat suka gaisheshi suna shirin fita Usman yace.
"Anisa ni banga su Gaddafi ba tunda na shigo, suna yawon dare ne?"
Yayi tambayarne dan son jin ta bakin yaran.
Anisa tace.
"Su Gaddafi Abba suna Sudan sun koma gida"
Kai ya gyaɗa mata kawai hakan yasa suka fita. Sai da suka rufe ƙofar Usman ya dawo da dubanshi gun Suhailat wacce bil hakƙi ta mayar da kanta kan karatun da take yi. Bangon littafin ya dinga kallo yana nanata sunan littafin. Har tsawon minti biyar Suhailat bata saurareshi ba, take ranshi kawai ya ɓaci a zuchiye ya miƙe ya fice tare da doka mata ƙofar ɗakin nata daram kunsan masu suna Usman akwaisu da saurin fishi. A falon ƙasa yaci karo da Asma'u tana sakkowa. Ko kallo bata isheshiba taga yayi sashenshi. Bakinta ta taɓe kawai.
A cikin wannan daren Suhailat haka ta kusan raba dare a jikin windo tana kallon tsakar gida ko Usman zai zo ya fice dan yara sun sanar mata shi kaÉ—ai yazo.
Ta ɓangaren Asma'u kuwa a kwance take kanta na kallon fankar sama dake bata iska, minti_minti tana sauke ajjiyar zuchiya dan ita tafi Suhailat shaƙa, kuma zatin Iyabo yayi mata tsaye a wuya.
Usman kuma bayan ya gama danne_dannen waya, ya kira Iyabo wayarta a kashe sai yabi lafiyar gado nannauyan bacci ya É—ebeshi dama ya kwaso gajiyar aiki ainun kiran sallar asuba ne ya farkar dashi. Wanka yayo ya zura jallabiya ya fice. A dawowa daga masallaci ne yaci karo da Suhailat a falo.
"Sannu da shigowa"
Tace mishi. Ganin idanun yaranta ne yasa ya tsaya ya amsata, yaranma suka gaisheshi ya amsa musu cike da kulawa.
Wucewarshi yayi ciki ya sake faÉ—awa gado ya shiga aikin bacci. Kamar a mafarki yaji anayi mishi tafiyar tsutsa a bayanshi. Yana buÉ—e idanu yaga Suhailat a zaune a gefenshi da kayan bacci a jikinta kamar yadda ya wuceta É—azu a falo.
"Bacci ai ya isa haka ango ka fito mu karya ga kumallonka a falo"
Murmushi mai fassarori yayi mata. Ya tashi ya zauna a gefenta jikinsu na gugar juna"
"Me yasa a wannan karon kika É—auki al'amarin kishi da zafi? Ai naga ko lokacin da Asma'u ta shigo gidannan baki nuna takai macen da zaki yi kishi da'ita ba, dama ance larabawa kishin masifa gareku, shi yasa ba'a muku kishiya To me Iyabo tayi miki Suhailat da har kikai fishi dani haka, jibi abinda kika yi mun jiya kina ganin kyautuwar hakan amman?"
Murmushi tayi tace.
"Yadda kake rawar ƙafa akan ita Iyabo, ya bambanta sosai da lokacin aurenka da Asma'u. Auren Asma'u ni kaɗaice akan auren komai ni kaba kuɗin nayi. Saɓanin wannan da Anty Sumayya ka ɗaura akan komai. Aka kawota danginka suka sake nuna mana ita mowar mata ce. Ƙannena ka koresu daga ciki suka koma masaukin baƙi duk akan Iyabo ita kaɗai dame tafi sauran mata to?"
Hannunta ya riƙe yana wasa da yatsunta yace.
"In banda daru na mata shin dole ne saina É—auraki akan komaine Suhailat. Kenan ita Anty Sumayya bata da damar yin kane_kane a lamarina alhalin kinsan bani da tamkarta. Oh wannan daliline yasa kika kori su Gaddafi, kika kasa zuwa kiga iyabo?"
"Sosai in ganta inyi mata me? Ai tuni an zana mini yadda take. Bana fatan ganinta danni da zaka raba mana gida da'ita da zanfi so. Kaga mu ture batun wannan bazawarar taka muje ka karya ko?"
Miƙewa yayi ya shige banɗaki ya wanke bakinshi yana jujjuya maganganun Suhailat. Ko da ya fito bata ɗakin bai fita ba saida ya saka kayanshi. Ƙananun kaya ya saka ya feshe jikinshi da turaren boss ys fito falon ya nemi waje ya zauna Suhailat ta zuba mishi abinci. Ta haɗe rai tayi kicin_kicin yana tura soyayyen dankalin yana ƙare mata kallo yana mamakinta da kishinta yayi tsanani akan Iyabo. A cikin zuchiyarshi yace.
"Ku sha kuruminku Iyabo ba zata taɓa zama tare da ku ba tare dani zata zauna ko mun shigo ƙasar zan kaita wani gidan daban.
A fili kuma yace"
"Ki kira su Gaddafi kice su dawo. Yau zan turo a kwashe kayan Iyabo a ɓarayin, su suyi dawowarsu tunda haka kuke buƙata daga ke har Asma'un"
Da sauri ta kalleshi tace.
"Ina kuma za'a kai kayan nata to?"
Sai da ya gama tauna dankalin ya haÉ—iye kafin yace.
"Gidana dake kusa da Alhaji Baba can za'a kai mata kayan nata sai ya zama gidanta tunda bakya buƙatar a haɗaku hakkinku ne, in kuna so ne za'a iya haɗaku in ɗaya ta nuna bata so dole a raba gida"
Jin haka yasa Suhailat ta gane tayi babbar wauta ya daga zuwan wata bare za'a bata gida sukutum kuma gashi mai kyau duk da dai gidan ƙaramine amman zasu sake su sha soyayyarsu. Ai babu shiri tace.
"A_a ai bazai yiwu ba. Ka barta anan Æ´an uwanta sun riga sun gama mata jere kuma ai anan suka santa"
"To Shikenan"
Iyakar abinda yace kenan dan bashi da lokacin da mace zata dinga raina mishi wayau haka. Ita kuna a tunaninta ya bar maganar. Sai da ya gama ya fita a gidan. Fitarshi baifi da awa biyu ba sai ga motar diban kaya ta shigo harabar gidan.
Suhailat ai saita burkice ta shiga kiran layin Usman amman baya É—auka. Ta kira Mus'ab ta ari wayarshi ta kira Usman É—in ringing É—aya Usman ya É—aga wayar.
"Hello Abban yara. Masu motar kamfanine suka zo wai sun zo diban kaya. Bana baka haƙuri ba ai ba'ayi haka ba kaine fa kace baka son raba kan yaranka ko ka mance?".
"Ban mance ba. Aikin gama ya gama na kira su Gaddafi ma suna hanya zasu dawo É—akinsu. Kiba Mus'ab waya dama zanyi magana dashi"
Taso yin magiya amman ya katseta tsaki taja ta miƙama Mus'ab wayarshi ta haura sama bata ko iya gani sosai. Mus'ab ya kara wayar a kunne.
"Mus'ab ka biyosu ka nuna musu gidan, nima ina gidan ana kan wankewa. Ai naga gidan baya buƙatar ma fenti ma"
Mus'ab ya haÉ—iye dariyarshi yace.
"To Shikenan Yaya sai mun zo É—in"
Ya kashe wayarshi. Hajiya Asma'u ce ta sakko tabi masu diba kaya da idanu sun fita da kujera"
"Mus'ab lafiya kuwa ina kuma za'a kai kayan?"
"Gidan Yaya dake kusa da Alhaji Baba wannan gidan ginin turawa"
A haka ya nufi hanyar waje ya barta tana maimaita gidanshi na kusa da Alhaji Baba?
Tsakar gidan ta fito. Matan ƙannen Usman duk sun wani firfito sai ƙus_ƙus suke yi. Da uwar harara ta bisu ta doka tsaki ta shige samanta ta zauna a kan gado ta dafe kanta dake neman tsagewa gida biyu.
IYABO:.