Sashe 107
Nama Ya Dahu Romo Danye Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
nace. Hakane kam. Allah ya basu lafiya baki ɗaya. "Ni sunana Sumayya, muna zaune a Girei kefa?" Sunana Jabu. Mu a ƙauyen Jere Banyo muke" Tare muka koma ɗakin jinya da Sumayya, muna tafe tana jana da hira har muka iso inda Dada take kwance. Da Boɗɗo suka gaisa. Nina na ƙarasa naima mahaifiyarta Yaya jiki, tana zaune tana shan kunu. Komawa nayi kusa da Baɗɗo. Dada bata motsa ba Baɗɗo tunda na tafi?" Shiru Baɗɗo bata ma san inayi ba hankalinta baya asibitinnan da halama yayi nisa. Na lura bayan ciwon Dada akwai matsalar dake nuƙurƙusan Baɗɗo shine ma dalilin ramarta. Kafaɗarta na dafa sai tayi sauri ta kalleni. Komai yayi tsanani maganin yana ga Allah. Baɗɗo je kiyi Sallah ki dawo ki sanar dani damuwarki, zan taimaka miki ko da da adda'a ne." Bata ce komai ba ta fita. Ni kuma na ƙurama Dada idanu sai numfashi taie ja tana saukewa, ga wani irin sanyi da akeyi, damma ɗakin da jama'a sosai gadajen marasa lafiya zasu iya kaiwa guda talatin. "Jabu ga abinci kuci naga kamar ba'a kawo muku abincin ba tukunna ko?" Na jiyo muryar sumayya a bayana da kwanon samirah a hannunta. Nasa hannu na amsa. Mun gode Sumayya. E ba'a kawo mana abincin ba tukunna dai, nafa gode. Murmushi tayi mun tace. 'ai mun zama ɗaya Jabu, ki saki jiki duk abinda kike buƙata ki tambayeni kawai." To Shikenan Sumayya." Kwanon abincin na ajjiye a gefen katifar da Dada take kwance. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI.